105) Sūrat Al-Fīl

Printed format

105)

'Alam Tará Kayfa Fa`ala Rabbuka Bi'aşĥābi Al-Fīl 105-001 Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
'Alam Yaj`al Kaydahum Fī Tađlīlin 105-002 Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
Wa 'Arsala `Alayhim Ţayrāan 'Abābīla 105-003 Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
Tarmīhim Biĥijāratin Min Sijjīlin 105-004 Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
Faja`alahum Ka`aşfin Ma'kūlin 105-005 Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
Next Sūrah