Waylun Likulli Humazatin Lumazahin | َ104-001 Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa). | وَيْل ٌ لِكُلِّ هُمَزَة ٍ لُمَزَة ٍ |
Al-Ladhī Jama`a Mālāan Wa `Addadahu | َ104-002 Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa. | الَّذِي جَمَعَ مَالا ً وَعَدَّدَهُ |
Yaĥsabu 'Anna Mālahu 'Akhladahu | َ104-003 Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi. | يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُ~ُ أَخْلَدَهُ |
Kallā ۖ Layunbadhanna Fī Al-Ĥuţamahi | َ104-004 A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama. | كَلاَّ ۖ لَيُنْبَذَنَّ فِي الْحُطَمَةِ |
Wa Mā 'Adrāka Mā Al-Ĥuţamahu | َ104-005 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama? | وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحُطَمَةُ |
Nāru Al-Lahi Al-Mūqadahu | َ104-006 Wutar Allah ce wadda ake hurawa. | نَارُ اللَّهِ الْمُوقَدَةُ |
Allatī Taţţali`u `Alá Al-'Af'idahi | َ104-007 Wadda take lẽƙãwa a kan zukata. | الَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى الأَفْئِدَةِ |
'Innahā `Alayhim Mu'uşadahun | َ104-008 Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu. | إِنَّهَا عَلَيْهِمْ مُؤصَدَة ٌ |
Fī `Amadin Mumaddadahin | َ104-009 A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu. | فِي عَمَد ٍ مُمَدَّدَة ٍ |