100) Sūrat Al-`Ādiyāt

Printed format

100)

Wa Al-`Ādiyāti Đabĥāan 100-001 Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
Fālmūriyāti Qadĥāan 100-002 Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
Fālmughīrāti Şubĥāan 100-003 Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
Fa'atharna Bihi Naqan 100-004 Sai su motsar da ƙũra game da shi.
Fawasaţna Bihi Jaman 100-005 Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
'Inna Al-'Insāna Lirabbihi Lakanūdun 100-006 Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
Wa 'Innahu `Alá Dhālika Lashahīdun 100-007 Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
Wa 'Innahu Liĥubbi Al-Khayri Lashadīdun 100-008 Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
'Afalā Ya`lamu 'Idhā Bu`thira Mā Fī Al-Qubūri 100-009 Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
Wa Ĥuşşila Mā Fī Aş-Şudūri 100-010 Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
'Inna Rabbahum Bihim Yawma'idhin Lakhabīrun 100-011 Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?
Next Sūrah