'Idhā Zulzilati Al-'Arđu Zilzālahā | َ099-001 Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta. | إِذَا زُلْزِلَتِ الأَرْضُ زِلْزَالَهَا |
Wa 'Akhrajati Al-'Arđu 'Athqālahā | َ099-002 Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi. | وَأَخْرَجَتِ الأَرْضُ أَثْقَالَهَا |
Wa Qāla Al-'Insānu Mā Lahā | َ099-003 Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?" | وَقَالَ الإِنسَانُ مَا لَهَا |
Yawma'idhin Tuĥaddithu 'Akhbārahā | َ099-004 A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta. | يَوْمَئِذ ٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا |
Bi'anna Rabbaka 'Awĥá Lahā | َ099-005 cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta. | بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَى لَهَا |
Yawma'idhin Yaşduru An-Nāsu 'Ashtātāan Liyuraw 'A`mālahum | َ099-006 A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. | يَوْمَئِذ ٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتا ً لِيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ |
Faman Ya`mal Mithqāla Dharratin Khayrāan Yarahu | َ099-007 To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. | فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرا ً يَرَهُ |
Wa Man Ya`mal Mithqāla Dharratin Sharrāan Yarahu | َ099-008 Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi. | وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّة ٍ شَرّا ً يَرَهُ |