98) Sūrat Al-Bayyinah

Printed format

98)

Lam Yakuni Al-Ladhīna Kafarū Min 'Ahli Al-Kitābi Wa Al-Mushrikīna Munfakkīna Ĥattá Ta'tiyahumu Al-Bayyinahu 098-001 Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu.
Rasūlun Mina Al-Lahi Yatlū Şuĥufāan Muţahharahan 098-002 Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki.
Fīhā Kutubun Qayyimahun 098-003 A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja.
Wa Mā Tafarraqa Al-Ladhīna 'Ū Al-Kitāba 'Illā Min Ba`di Mā Jā'at/humu Al-Bayyinahu 098-004 Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu.
Wa Mā 'Umirū 'Illā Liya`budū Al-Laha Mukhlişīna Lahu Ad-Dīna Ĥunafā'a Wa Yuqīmū Aş-Şalāata Wa Yu'utū Az-Zakāata  ۚ  Wa Dhalika Dīnu Al-Qayyimahi 098-005 Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Kafarū Min 'Ahli Al-Kitābi Wa Al-Mushrikīna Fī Nāri Jahannama Khālidīna Fīhā  ۚ  'Ūlā'ika Hum Sharru Al-Barīyahi 098-006 Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti 'Ūlā'ika Hum Khayru Al-Barīyahi 098-007 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta.
Jazā'uuhum `Inda Rabbihim Jannātu `Adnin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā 'Abadāan  ۖ  Rađiya Al-Lahu `Anhum Wa Rađū `Anhu  ۚ  Dhālika Liman Khashiya Rabbahu 098-008 Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa.  ۖ   ۚ 
Next Sūrah