96) Sūrat Al-`Alaq

Printed format

96)

Aqra' Biāsmi Rabbika Al-Ladhī Khalaqa 096-001 Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
Khalaqa Al-'Insāna Min `Alaqin 096-002 Ya hahitta mutum daga gudan jini.
Aqra' Wa Rabbuka Al-'Akramu 096-003 Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
Al-Ladhī `Allama Bil-Qalami 096-004 Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
`Allama Al-'Insāna Mā Lam Ya`lam 096-005 Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
Kallā 'Inna Al-'Insāna Layaţghá 096-006 A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
'An Ra'āhu Astaghná 096-007 Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
'Inna 'Ilá Rabbika Ar-Ruj 096-008 Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
'Ara'ayta Al-Ladhī Yanhá 096-009 Shin, kã ga wanda ke hana.
`Abdāan 'Idhā Şallá 096-010 Bãwã idan yã yi salla?
'Ara'ayta 'In Kāna `Alá Al-Hudá 096-011 Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
'Aw 'Amara Bit-Taq 096-012 Ko ya yi umurni da taƙawa?
'Ara'ayta 'In Kadhdhaba Wa Tawallá 096-013 Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
'Alam Ya`lam Bi'anna Al-Laha Yará 096-014 Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
Kallā La'in Lam Yantahi Lanasfa`ā Bin-Nāşiyahi 096-015 A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
Nāşiyatindhibatin Khāţi'ahin 096-016 Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
Falyad`u Nādiyah 096-017 Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
Sanad`u Az-Zabāniyaha 096-018 Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
Kallā Lā Tuţi`hu Wa Asjudqtarib 096-019 A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
Next Sūrah