94) Sūrat Ash-Sharĥ

Printed format

94)

'Alam Nashraĥ Laka Şadraka 094-001 Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
Wa Wađa`nā `Anka Wizraka 094-002 Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
Al-Ladhī 'Anqađa Žahraka 094-003 Wanda ya nauyayi bãyanka?
Wa Rafa`nā Laka Dhikraka 094-004 Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
Fa'inna Ma`a Al-`Usri Yusrāan 094-005 To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
'Inna Ma`a Al-`Usri Yusrāan 094-006 Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
Fa'idhā Faraghta Fānşab 094-007 Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
Wa 'Ilá Rabbika Fārghab 094-008 Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
Next Sūrah