93) Sūrat Ađ-Đuĥá

Printed format

93)

Wa Ađ-Đuĥá 093-001 Inã rantsuwa da hantsi.
Wa Al-Layli 'Idhā Sajá 093-002 Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
Mā Wadda`aka Rabbuka Wa Mā Qalá 093-003 Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
Wa Lal'ākhiratu Khayrun Laka Mina Al-'Ū 093-004 Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
Wa Lasawfa Yu`ţīka Rabbuka Fatarđá 093-005 Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
'Alam Yajidka Yatīmāan Fa'ā 093-006 Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
Wa Wajadaka Đāllāan Fahadá 093-007 Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
Wa Wajadaka `Ā'ilāan Fa'aghná 093-008 Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
Fa'ammā Al-Yatīma Falā Taqhar 093-009 Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
Wa 'Ammā As-Sā'ila Falā Tanhar 093-010 Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
Wa 'Ammā Bini`mati Rabbika Faĥaddith 093-011 Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
Next Sūrah