92) Sūrat Al-Layl

Printed format

92)

Wa Al-Layli 'Idhā Yaghshá 092-001 Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
Wa An-Nahāri 'Idhā Tajallá 092-002 Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
Wa Mā Khalaqa Adh-Dhakara Wa Al-'Unthá 092-003 Da abin da ya halitta namiji da mace.
'Inna Sa`yakum Lashattá 092-004 Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
Fa'ammā Man 'A`ţá Wa Attaqá 092-005 To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
Wa Şaddaqa Bil-Ĥusná 092-006 Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
Fasanuyassiruhu Lilyusrá 092-007 To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
Wa 'Ammā Man Bakhila Wa Astaghná 092-008 Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
Wa Kadhdhaba Bil-Ĥusná 092-009 Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
Fasanuyassiruhu Lil`usrá 092-010 To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
Wa Mā Yughnī `Anhu Māluhu 'Idhā Taraddá 092-011 Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). ~
'Inna `Alaynā Lalhudá 092-012 Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
Wa 'Inna Lanā Lal'ākhirata Wa Al-'Ū 092-013 Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
Fa'andhartukum Nārāan Talažžá 092-014 Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
Lā Yaşlāhā 'Illā Al-'Ash 092-015 Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
Al-Ladhī Kadhdhaba Wa Tawallá 092-016 Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
Wa Sayujannabuhā Al-'Atqá 092-017 Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
Al-Ladhī Yu'utī Mālahu Yatazakká 092-018 Wanda yake bãyar da dũkiyarsa ,alhãli yana tsarkaka.
Wa Mā Li'ĥadin `Indahu Min Ni`matin Tuj 092-019 Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
'Illā Abtighā'a Wajhi Rabbihi Al-'A`lá 092-020 Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
Wa Lasawfa Yarđá 092-021 To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi) .
Next Sūrah