91) Sūrat Ash-Shams

Printed format

91)

Wa Ash-Shamsi Wa Đuĥāhā 091-001 Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
Wa Al-Qamari 'Idhā Talāhā 091-002 Kuma da wata idan ya bi ta.
Wa An-Nahāri 'Idhā Jallāhā 091-003 Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
Wa Al-Layli 'Idhā Yaghshāhā 091-004 Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
Wa As-Samā'i Wa Mā Banāhā 091-005 Da sama da abin da ya gina ta.
Wa Al-'Arđi Wa Mā Ţaĥāhā 091-006 Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
Wa Nafsin Wa Mā Sawwāhā 091-007 Da rai da abin da ya daidaita shi.
Fa'alhamahā Fujūrahā Wa Taqwāhā 091-008 Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
Qad 'Aflaĥa Man Zakkāhā 091-009 Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
Wa Qad Khāba Man Dassāhā 091-010 Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
Kadhdhabat Thamūdu Biţaghwāhā 091-011 Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
'Idhi Anba`atha 'Ashqāhā 091-012 A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
Faqāla Lahum Rasūlu Al-Lahi Nāqata Al-Lahi Wa Suqyāhā 091-013 Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
Fakadhdhabūhu Fa`aqarūhā Fadamdama `Alayhim Rabbuhum Bidhanbihim Fasawwāhā 091-014 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
Wa Lā Yakhāfu `Uqbāhā 091-015 Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).
Next Sūrah