Lā 'Uqsimu Bihadhā Al-Baladi | َ090-001 Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba. | لاَ أُقْسِمُ بِهَذَا الْبَلَدِ |
Wa 'Anta Ĥillun Bihadhā Al-Baladi | َ090-002 Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. | وَأَنْتَ حِلّ ٌ بِهَذَا الْبَلَدِ |
Wa Wālidin Wa Mā Walada | َ090-003 Da mahaifi da abin da ya haifa. | وَوَالِد ٍ وَمَا وَلَدَ |
Laqad Khalaqnā Al-'Insāna Fī Kabadin | َ090-004 Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. | لَقَدْ خَلَقْنَا الإِنسَانَ فِي كَبَد ٍ |
'Ayaĥsabu 'An Lan Yaqdira `Alayhi 'Aĥadun | َ090-005 Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? | أَيَحْسَبُ أَنْ لَنْ يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَد ٌ |
Yaqūlu 'Ahlaktu Mālāan Lubadāan | َ090-006 Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa," | يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالا ً لُبَدا ً |
'Ayaĥsabu 'An Lam Yarahu 'Aĥadun | َ090-007 Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? | أَيَحْسَبُ أَنْ لَمْ يَرَهُ~ُ أَحَد ٌ |
'Alam Naj`al Lahu `Aynayni | َ090-008 Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? | أَلَمْ نَجْعَلْ لَه ُُ عَيْنَيْنِ |
Wa Lisānāan Wa Shafatayni | َ090-009 Da harshe, da leɓɓa biyu. | وَلِسَانا ً وَشَفَتَيْنِ |
Wa Hadaynāhu An-Najdayni | َ090-010 Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba? | وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ |
Falā Aqtaĥama Al-`Aqabaha | َ090-011 To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? | فَلاَ اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ |
Wa Mā 'Adrāka Mā Al-`Aqabahu | َ090-012 Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? | وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ |
Fakku Raqabahin | َ090-013 Ita ce fansar wuyan bãwa. | فَكُّ رَقَبَة ٍ |
'Aw 'Iţ`āmun Fī Yawmin Dhī Masghabahin | َ090-014 Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. | أَوْ إِطْعَام ٌ فِي يَوْم ٍ ذِي مَسْغَبَة ٍ |
Yatīmāan Dhā Maqrabahin | َ090-015 Ga marãya ma'abũcin zumunta. | يَتِيما ً ذَا مَقْرَبَة ٍ |
'Aw Miskīnāan Dhā Matrabahin | َ090-016 Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. | أَوْ مِسْكِينا ً ذَا مَتْرَبَة ٍ |
Thumma Kāna Mina Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Tawāşaw Biş-Şabri Wa Tawāşaw Bil-Marĥamahi | َ090-017 Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. | ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ |
'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Maymanahi | َ090-018 Waɗannan ne ma'abũta albarka | أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ |
Wa Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyātinā Hum 'Aşĥābu Al-Mash'amahi | َ090-019 Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci | وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ |
`Alayhim Nārun Mu'uşadahun | َ090-020 A kansu akwai wata wuta abar kullewa. | عَلَيْهِمْ نَار ٌ مُؤصَدَة ٌ |