Wa Al-Fajri | َ089-001 Inã rantsuwa da alfijiri. | وَالْفَجْرِ |
Wa Layālin `Ashrin | َ089-002 Da darũruwa gõma. | وَلَيَالٍ عَشْر ٍ |
Wa Ash-Shaf`i Wa Al-Watri | َ089-003 Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. | وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ |
Wa Al-Layli 'Idhā Yasri | َ089-004 Da dare idan yana shũɗewa. | وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ |
Hal Fī Dhālika Qasamun Lidhī Ĥijrin | َ089-005 Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? | هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَم ٌ لِذِي حِجْر ٍ |
'Alam Tara Kayfa Fa`ala Rabbuka Bi`ādin | َ089-006 Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? | أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَاد ٍ |
'Irama Dhāti Al-`Imādi | َ089-007 Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki. | إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ |
Allatī Lam Yukhlaq Mithluhā Fī Al-Bilādi | َ089-008 Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). | الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلاَدِ |
Wa Thamūda Al-Ladhīna Jābū Aş-Şakhra Bil-Wādi | َ089-009 Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? | وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ |
Wa Fir`awna Dhī Al-'Awtādi | َ089-010 Da Fir'auna mai turãku. | وَفِرْعَوْنَ ذِي الأَوْتَادِ |
Al-Ladhīna Ţaghaw Fī Al-Bilādi | َ089-011 Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? | الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلاَدِ |
Fa'aktharū Fīhā Al-Fasāda | َ089-012 Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. | فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ |
Faşabba `Alayhim Rabbuka Sawţa `Adhābin | َ089-013 Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. | فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَاب ٍ |
'Inna Rabbaka Labiālmirşādi | َ089-014 Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. | إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ |
Fa'ammā Al-'Insānu 'Idhā Mā Abtalāhu Rabbuhu Fa'akramahu Wa Na``amahu Fayaqūlu Rabbī 'Akramani | َ089-015 To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." | فَأَمَّا الإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلاَه ُُ رَبُّه ُُ فَأَكْرَمَه ُُ وَنَعَّمَه ُُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ |
Wa 'Ammā 'Idhā Mā Abtalāhu Faqadara `Alayhi Rizqahu Fayaqūlu Rabbī 'Ahānani | َ089-016 Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." | وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلاَه ُُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَه ُُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ |
Kallā ۖ Bal Lā Tukrimūna Al-Yatīma | َ089-017 A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! | كَلاَّ ۖ بَل لاَ تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ |
Wa Lā Taĥāđđūna `Alá Ţa`āmi Al-Miskīni | َ089-018 Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! | وَلاَ تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ |
Wa Ta'kulūna At-Turātha 'Aklāan Lammāan | َ089-019 Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. | وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلا ً لَمّا ً |
Wa Tuĥibbūna Al-Māla Ĥubbāan Jammāan | َ089-020 Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. | وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبّا ً جَمّا ً |
Kallā 'Idhā Dukkati Al-'Arđu Dakkāan Dakkāan | َ089-021 A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. | كَلاَّ إِذَا دُكَّتِ الأَرْضُ دَكّا ً دَكّا ً |
Wa Jā'a Rabbuka Wa Al-Malaku Şaffāan Şaffāan | َ089-022 Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. | وَجَاءَ رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفّا ً صَفّا ً |
Wa Jī'a Yawma'idhin Bijahannama ۚ Yawma'idhin Yatadhakkaru Al-'Insānu Wa 'Anná Lahu Adh-Dhikrá | َ089-023 Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi! | وَجِيءَ يَوْمَئِذ ٍ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذ ٍ يَتَذَكَّرُ الإِنْسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى |
Yaqūlu Yā Laytanī Qaddamtu Liĥayātī | َ089-024 Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!" | يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي |
Fayawma'idhin Lā Yu`adhdhibu `Adhābahu 'Aĥadun | َ089-025 To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah. | فَيَوْمَئِذ ٍ لاَ يُعَذِّبُ عَذَابَهُ~ُ أَحَد ٌ |
Wa Lā Yūthiqu Wathāqahu 'Aĥadun | َ089-026 Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa. | وَلاَ يُوثِقُ وَثَاقَهُ~ُ أَحَد ٌ |
Yā 'Ayyatuhā An-Nafsu Al-Muţma'innahu | َ089-027 Yã kai rai mai natsuwa! | يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ |
Arji`ī 'Ilá Rabbiki Rāđiyatan Marđīyahan | َ089-028 Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira). | ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَة ً مَرْضِيَّة ً |
Fādkhulī Fī `Ibādī | َ089-029 Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya). | فَادْخُلِي فِي عِبَادِي |
Wa Adkhulī Jannatī | َ089-030 Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira). | وَادْخُلِي جَنَّتِي |