88) Sūrat Al-Ghāshiyah

Printed format

88)

Hal 'Atāka Ĥadīthu Al-Ghāshiyahi 088-001 Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
Wujūhun Yawma'idhin Khāshi`ahun 088-002 Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
`Āmilatun Nāşibahun 088-003 Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
Taşlá Nārāan Ĥāmiyahan 088-004 Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
Tusqá Min `Aynin 'Āniyahin 088-005 Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
Laysa Lahum Ţa`āmun 'Illā Min Đarī`in 088-006 Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
Lā Yusminu Wa Lā Yughnī Min Jū`in 088-007 Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
Wujūhun Yawma'idhin Nā`imahun 088-008 Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
Lisa`yihā Rāđiyahun 088-009 Game da aikinsu, masu yarda ne.
Fī Jannatin `Āliyahin 088-010 (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
Lā Tasma`u Fīhā Lāghiyahan 088-011 Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
Fīhā `Aynunriyahun 088-012 A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
Fīhā Sururun Marfū`ahun 088-013 A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
Wa 'Akwābun Mawđū`ahun 088-014 Da kõfuna ar'aje.
Wa Namāriqu Maşfūfahun 088-015 Da filõli jẽre,
Wa Zarābīyu Mabthūthahun 088-016 Da katifu shimfiɗe.
'Afalā Yanžurūna 'Ilá Al-'Ibili Kayfa Khuliqat 088-017 Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
Wa 'Ilá As-Samā'i Kayfa Rufi`at 088-018 Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
Wa 'Ilá Al-Jibāli Kayfa Nuşibat 088-019 Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
Wa 'Ilá Al-'Arđi Kayfa Suţiĥat 088-020 Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
Fadhakkir 'Innamā 'Anta Mudhakkirun 088-021 sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
Lasta `Alayhim Bimusayţirin 088-022 Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
'Illā Man Tawallá Wa Kafara 088-023 Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
Fayu`adhdhibuhu Al-Lahu Al-`Adhāba Al-'Akbara 088-024 To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
'Inna 'Ilaynā 'Īābahum 088-025 Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
Thumma 'Inna `Alaynā Ĥisābahum 088-026 Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
Next Sūrah