87) Sūrat Al-'`lá

Printed format

87)

Sabbiĥi Asma Rabbika Al-'A`lá 087-001 Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
Al-Ladhī Khalaqa Fasawwá 087-002 Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
Wa Al-Ladhī Qaddara Fahadá 087-003 Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar,(da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
Wa Al-Ladhī 'Akhraja Al-Mar`á 087-004 Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
Faja`alahu Ghuthā'an 'Aĥwá 087-005 Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
Sanuqri'uka Falā Tan 087-006 Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
'Illā Mā Shā'a Al-Lahu  ۚ  'Innahu Ya`lamu Al-Jahra Wa Mā Yakh 087-007 Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.  ۚ 
Wa Nuyassiruka Lilyusrá 087-008 Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
Fadhakkir 'In Nafa`ati Adh-Dhikrá 087-009 Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
Sayadhdhakkaru Man Yakhshá 087-010 Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
Wa Yatajannabuhā Al-'Ash 087-011 Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
Al-Ladhī Yaşlá An-Nāra Al-Kub 087-012 Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
Thumma Lā Yamūtu Fīhā Wa Lā Yaĥyā 087-013 Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
Qad 'Aflaĥa Man Tazakká 087-014 Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
Wa Dhakara Asma Rabbihi Faşallá 087-015 Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
Bal Tu'uthirūna Al-Ĥayāata Ad-Dun 087-016 Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
Wa Al-'Ākhiratu Khayrun Wa 'Ab 087-017 Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
'Inna Hādhā Lafī Aş-Şuĥufi Al-'Ū 087-018 Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
Şuĥufi 'Ibrāhīma Wa Mūsá 087-019 Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
Next Sūrah