86) Sūrat Aţ-Ţāriq

Printed format

86)

Wa As-Samā'i Wa Aţ-Ţāriqi 086-001 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
Wa Mā 'Adrāka Mā Aţ-Ţāriqu 086-002 To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
An-Najmu Ath-Thāqibu 086-003 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
'In Kullu Nafsin Lammā `Alayhā Ĥāfižun 086-004 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
Falyanžuri Al-'Insānu Mimma Khuliqa 086-005 To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
Khuliqa Min Mā'in Dāfiqin 086-006 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
Yakhruju Min Bayni Aş-Şulbi Wa At-Tarā'ibi 086-007 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
'Innahu `Alá Raj`ihi Laqādirun 086-008 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
Yawma Tub As-Sarā'iru 086-009 Rãnar da ake jarrabawar asirai.
Famā Lahu Min Qūwatin Wa Lā Nāşirin 086-010 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
Wa As-Samā'i Dhāti Ar-Raj`i 086-011 Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
Wa Al-'Arđi Dhāti Aş-Şad`i 086-012 Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
'Innahu Laqawlun Faşlun 086-013 Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
Wa Mā Huwa Bil-Hazli 086-014 Kuma shĩ bã bananci bane
'Innahum Yakīdūna Kaydāan 086-015 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
Wa 'Akīdu Kaydāan 086-016 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
Famahhili Al-Kāfirīna 'Amhilhum Ruwaydāan 086-017 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
Next Sūrah