85) Sūrat Al-Burūj

Printed format

85)

Wa As-Samā'i Dhāti Al-Burūji 085-001 Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
Wa Al-Yawmi Al-Maw`ūdi 085-002 Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
Wa Shāhidin Wa Mash/hūdin 085-003 Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
Qutila 'Aşĥābu Al-'Ukhdūdi 085-004 An la'ani mutãnen rãmi.
An-Nāri Dhāti Al-Waqūdi 085-005 Wato wuta wadda aka hura.
'Idh Hum `Alayhā Qu`ūdun 085-006 A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
Wa Hum `Alá Mā Yaf`alūna Bil-Mu'uminīna Shuhūdun 085-007 Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
Wa Mā Naqamū Minhum 'Illā 'An Yu'uminū Bil-Lahi Al-`Azīzi Al-Ĥamīdi 085-008 Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
Al-Ladhī Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۚ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Shahīdun 085-009 Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Fatanū Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Thumma Lam Yatūbū Falahum `Adhābu Jahannama Wa Lahum `Adhābu Al-Ĥarīqi 085-010 Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
'Inna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۚ  Dhālika Al-Fawzu Al-Kabīru 085-011 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.  ۚ 
'Inna Baţsha Rabbika Lashadīdun 085-012 Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
'Innahu Huwa Yubdi'u Wa Yu`īdu 085-013 Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
Wa Huwa Al-Ghafūru Al-Wadūdu 085-014 Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
Dhū Al-`Arshi Al-Majīdu 085-015 Mai Al'arshi mai girma
Fa``ālun Limā Yurīdu 085-016 Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
Hal 'Atāka Ĥadīthu Al-Junūdi 085-017 Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
Fir`awna Wa Thamūda 085-018 Fir'auna da samũdãwa?
Bali Al-Ladhīna Kafarū Fī Takdhībin 085-019 Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
Wa Allāhu Min Warā'ihim Muĥīţun 085-020 Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
Bal Huwa Qur'ānun Majīdun 085-021 Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
Fī Lawĥin Maĥfūžin 085-022 A cikin Allo tsararre.
Next Sūrah