84) Sūrat Al-'Inshiqāq

Printed format

84)

'Idhā As-Samā'u Anshaqqat 084-001 Idan sama ta kẽce,
Wa 'Adhinat Lirabbihā Wa Ĥuqqat 084-002 Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
Wa 'Idhā Al-'Arđu Muddat 084-003 Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
Wa 'Alqat Mā Fīhā Wa Takhallat 084-004 Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
Wa 'Adhinat Lirabbihā Wa Ĥuqqat 084-005 Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
Yā 'Ayyuhā Al-'Insānu 'Innaka Kādiĥun 'Ilá Rabbika Kadĥāan Famulāqīhi 084-006 Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
Fa'ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Biyamīnihi 084-007 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
Fasawfa Yuĥāsabu Ĥisābāan Yasīrāan 084-008 To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
Wa Yanqalibu 'Ilá 'Ahlihi Masrūrāan 084-009 Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
Wa 'Ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Warā'a Žahrihi 084-010 Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
Fasawfa YadThubūrāan 084-011 To, zã shi dinga kiran halaka!
Wa Yaşlá Sa`īrāan 084-012 Kuma ya shiga sa'ĩr.
'Innahu Kāna Fī 'Ahlihi Masrūrāan 084-013 Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
'Innahu Žanna 'An Lan Yaĥūra 084-014 Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
Balá 'Inna Rabbahu Kāna Bihi Başīrāan 084-015 Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
Falā 'Uqsimu Bish-Shafaqi 084-016 To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
Wa Al-Layli Wa Mā Wasaqa 084-017 Da dare, da abin da ya ƙunsa.
Wa Al-Qamari 'Idhā Attasaqa 084-018 Da watã idan (haskensa) ya cika.
Latarkabunna Ţabaqāan `An Ţabaqin 084-019 Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
Famā Lahum Lā Yu'uminūna 084-020 To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
Wa 'Idhā Quri'a `Alayhimu Al-Qur'ānu Lā Yasjudūna 084-021 Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
Bali Al-Ladhīna Kafarū Yukadhdhibūna 084-022 Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
Wa Allāhu 'A`lamu Bimā Yū`ūna 084-023 Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
Fabashshirhum Bi`adhābin 'Alīmin 084-024 Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
'Illā Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Lahum 'Ajrun Ghayru Mamnūnin 084-025 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
Next Sūrah