83) Sūrat Al-Muţaffifīn

Printed format

83)

Waylun Lilmuţaffifīna 083-001 Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
Al-Ladhīna 'Idhā Aktālū `Alá An-Nāsi Yastawfūna 083-002 Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
Wa 'Idhā Kālūhum 'Aw Wazanūhum Yukhsirūna 083-003 Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
'Alā Yažunnu 'Ūla'ika 'Annahum Mabthūna 083-004 Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
Liyawmin `Ažīmin 083-005 Domin yini mai girma.
Yawma Yaqūmu An-Nāsu Lirabbi Al-`Ālamīna 083-006 Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
Kallā 'Inna Kitāba Al-Fujjāri Lafī Sijjīnin 083-007 Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
Wa Mā 'Adrāka Mā Sijjīnun 083-008 Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
Kitābun Marqūmun 083-009 Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 083-010 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
Al-Ladhīna Yukadhdhibūna Biyawmi Ad-Dīni 083-011 Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
Wa Mā Yukadhdhibu Bihi 'Illā Kullu Mu`tadin 'Athīmin 083-012 Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
'Idhā Tutlá `Alayhi 'Āyātunā Qāla 'Asāţīru Al-'Awwalīna 083-013 Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
Kallā  ۖ  Bal  ۜ  Rāna `Alá Qulūbihim Mā Kānū Yaksibūna 083-014 A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.  ۖ   ۜ 
Kallā 'Innahum `An Rabbihim Yawma'idhin Lamaĥjūbūna 083-015 A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
Thumma 'Innahum Laşālū Al-Jaĥīmi 083-016 Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
Thumma Yuqālu Hādhā Al-Ladhī Kuntum Bihi Tukadhdhibūna 083-017 Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
Kallā 'Inna Kitāba Al-'Abrāri Lafī `Illīyīna 083-018 A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
Wa Mā 'Adrāka Mā `Illīyūna 083-019 Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
Kitābun Marqūmun 083-020 Wani littãfi ne rubũtacce.
Yash/haduhu Al-Muqarrabūna 083-021 Muƙarrabai suke halarta shi.
'Inna Al-'Abrāra Lafī Na`īmin 083-022 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
`Alá Al-'Arā'iki Yanžurūna 083-023 A kan karagu, suna ta kallo.
Ta`rifu Fī Wujūhihim Nađrata An-Na`īmi 083-024 Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
Yusqawna Min Raĥīqin Makhtūmin 083-025 Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
Khitāmuhu Miskun  ۚ  Wa Fī Dhālika Falyatanāfasi Al-Mutanāfisūna 083-026 ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.  ۚ 
Wa Mizājuhu Min Tasnīmin 083-027 Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
`Aynāan Yashrabu Bihā Al-Muqarrabūna 083-028 (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
'Inna Al-Ladhīna 'Ajramū Kānū Mina Al-Ladhīna 'Āmanū Yađĥakūna 083-029 Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
Wa 'Idhā Marrū Bihim Yataghāmazūna 083-030 Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
Wa 'Idhā Anqalabū 'Ilá 'Ahlihimu Anqalabū Fakihīna 083-031 Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
Wa 'Idhā Ra'awhum Qālū 'Inna Hā'uulā' Lađāllūna 083-032 Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
Wa Mā 'Ursilū `Alayhim Ĥāfižīna 083-033 Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
Fālyawma Al-Ladhīna 'Āmanū Mina Al-Kuffāri Yađĥakūna 083-034 To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni,sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
`Alá Al-'Arā'iki Yanžurūna 083-035 A kan karagu, suna ta kallo.
Hal Thūwiba Al-Kuffāru Mā Kānū Yaf`alūna 083-036 Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?
Next Sūrah