82) Sūrat Al-'Infiţār

Printed format

82)

'Idhā As-Samā'u Anfaţarat 082-001 Idan sama ta tsãge.
Wa 'Idhā Al-Kawākibu Antatharat 082-002 Kuma idan taurãri suka wãtse.
Wa 'Idhā Al-Biĥāru Fujjirat 082-003 Kuma idan tẽkuna aka facce su.
Wa 'Idhā Al-Qubūru Bu`thirat 082-004 Kuma idan kaburbura aka tõne su.
`Alimat Nafsun Mā Qaddamat Wa 'Akhkharat 082-005 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
Yā 'Ayyuhā Al-'Insānu Mā Gharraka Birabbika Al-Karīmi 082-006 Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
Al-Ladhī Khalaqaka Fasawwāka Fa`adalaka 082-007 Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
Fī 'Ayyi ŞūratinShā'a Rakkabaka 082-008 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
Kallā Bal Tukadhdhibūna Bid-Dīni 082-009 A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
Wa 'Inna `Alaykum Laĥāfižīna 082-010 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
Kirāmāan Kātibīna 082-011 Mãsu daraja, marubũta.
Ya`lamūna Mā Taf`alūna 082-012 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
'Inna Al-'Abrāra Lafī Na`īmin 082-013 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
Wa 'Inna Al-Fujjāra Lafī Jaĥīmin 082-014 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
Yaşlawnahā Yawma Ad-Dīni 082-015 Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
Wa Mā Hum `Anhā Bighā'ibīna 082-016 Bã zã su faku daga gare ta ba.
Wa Mā 'Adrāka Mā Yawmu Ad-Dīni 082-017 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
Thumma Mā 'Adrāka Mā Yawmu Ad-Dīni 082-018 Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
Yawma Lā Tamliku Nafsun Linafsin Shay'āan Wa  ۖ  Al-'Amru Yawma'idhin Lillahi 082-019 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.  ۖ 
Next Sūrah