81) Sūrat At-Takwīr

Printed format

81)

'Idhā Ash-Shamsu Kūwirat 081-001 Idan rãna aka shafe haskenta
Wa 'Idhā An-Nujūmu Ankadarat 081-002 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
Wa 'Idhā Al-Jibālu Suyyirat 081-003 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
Wa 'Idhā Al-`Ishāru `Uţţilat 081-004 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
Wa 'Idhā Al-Wuĥūshu Ĥushirat 081-005 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
Wa 'Idhā Al-Biĥāru Sujjirat 081-006 Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
Wa 'Idhā An-Nufūsu Zūwijat 081-007 Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
Wa 'Idhā Al-Maw'ūdatu Su'ilat 081-008 Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
Bi'ayyi Dhanbin Qutilat 081-009 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
Wa 'Idhā Aş-Şuĥufu Nushirat 081-010 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
Wa 'Idhā As-Samā'u Kushiţat 081-011 Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
Wa 'Idhā Al-Jaĥīmu Su``irat 081-012 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
Wa 'Idhā Al-Jannatu 'Uzlifat 081-013 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
`Alimat Nafsun Mā 'Aĥđarat 081-014 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
Falā 'Uqsimu Bil-Khunnasi 081-015 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
Al-Jawāri Al-Kunnasi 081-016 Mãsu gudu suna ɓũya.
Wa Al-Layli 'Idhā `As`asa 081-017 Da dare idan ya bãyar da bãya.
Wa Aş-Şubĥi 'Idhā Tanaffasa 081-018 Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
'Innahu Laqawlu Rasūlin Karīmin 081-019 Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
Dhī Qūwatin `Inda Dhī Al-`Arshi Makīnin 081-020 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
Muţā`in Thamma 'Amīnin 081-021 Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
Wa Mā Şāĥibukum Bimajnūnin 081-022 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
Wa Laqad Ra'āhu Bil-'Ufuqi Al-Mubīni 081-023 Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
Wa Mā Huwa `Alá Al-Ghaybi Biđanīnin 081-024 Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
Wa Mā Huwa Biqawli Shayţānin Rajīmin 081-025 Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
Fa'ayna Tadh/habūna 081-026 Shin, a inã zã ku tafi?
'In Huwa 'Illā Dhikrun Lil`ālamīna 081-027 Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
Liman Shā'a Minkum 'An Yastaqīma 081-028 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
Wa Mā Tashā'ūna 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu Rabbu Al-`Ālamīna 081-029 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
Next Sūrah