80) Sūrat `Abasa

Printed format

80)

`Abasa Wa Tawallá 080-001 Yã game huska kuma ya jũya bãya.
'An Jā'ahu Al-'A`má 080-002 Sabõda makãho yã je masa.
Wa Mā Yudrīka La`allahu Yazzakká 080-003 To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
'Aw Yadhdhakkaru Fatanfa`ahu Adh-Dhikrá 080-004 Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
'Ammā Mani Astaghná 080-005 Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
Fa'anta Lahu Taşaddá 080-006 Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
Wa Mā `Alayka 'Allā Yazzakká 080-007 To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
Wa 'Ammā Man Jā'aka Yas`á 080-008 Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
Wa Huwa Yakhshá 080-009 Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
Fa'anta `Anhu Talahhá 080-010 Kai kuma kã shagala ga barinsa!
Kallā 'Innahā Tadhkirahun 080-011 A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
Faman Shā'a Dhakarahu 080-012 Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
Fī Şuĥufin Mukarramahin 080-013 (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
Marfū`atin Muţahharahin 080-014 Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
Bi'aydī Safarahin 080-015 A cikin hannãyen mala'iku marubũta.
Kirāmin Bararahin 080-016 Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
Qutila Al-'Insānu Mā 'Akfarahu 080-017 An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
Min 'Ayyi Shay'in Khalaqahu 080-018 Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
Min Nuţfatin Khalaqahu Faqaddarahu 080-019 Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
Thumma As-Sabīla Yassarahu 080-020 Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
Thumma 'Amātahu Fa'aqbarahu 080-021 Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
Thumma 'Idhā Shā'a 'Ansharahu 080-022 Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
Kallā Lammā Yaqđi Mā 'Amarahu 080-023 Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
Falyanžuri Al-'Insānu 'Ilá Ţa`āmihi 080-024 To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
'Annā Şabab Al-Mā'a Şabbāan 080-025 Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
Thumma Shaqaq Al-'Arđa Shaqqāan 080-026 Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
Fa'anbatnā Fīhā Ĥabbāan 080-027 Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya ,a cikinta.
Wa `Inabāan Wa Qađbāan 080-028 Da inabi da ciyãwa.
Wa Zaytūnāan Wa Nakhan 080-029 Da zaitũni da itãcen dabĩno.
Wa Ĥadā'iqa Ghulbāan 080-030 Da lambuna, mãsu yawan itãce.
Wa Fākihatan Wa 'Abbāan 080-031 Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
Matā`āan Lakum Wa Li'an`āmikum 080-032 Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
Fa'idhā Jā'ati Aş-Şākhkhahu 080-033 To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
Yawma Yafirru Al-Mar'u Min 'Akhīhi 080-034 Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
Wa 'Ummihi Wa 'Abīhi 080-035 Da uwarsa da ubansa.
Wa Şāĥibatihi Wa Banīhi 080-036 Da mãtarsa da ɗiyansa.
Likulli Amri'in Minhum Yawma'idhin Sha'nun Yughnīhi 080-037 Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
Wujūhun Yawma'idhin Musfirahun 080-038 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
Đāĥikatun Mustabshirahun 080-039 Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
Wa Wujūhun Yawma'idhin `Alayhā Ghabarahun 080-040 Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
Tarhaquhā Qatarahun 080-041 Baƙi zai rufe su.
'Ūlā'ika Humu Al-Kafaratu Al-Fajarahu 080-042 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).
Next Sūrah