Wa An-Nāzi`āti Gharqāan | َ079-001 Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. | وَالنَّازِعَاتِ غَرْقا ً |
Wa An-Nāshiţāti Nashţāan | َ079-002 Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. | وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطا ً |
Wa As-Sābiĥāti Sabĥāan | َ079-003 Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. | وَالسَّابِحَاتِ سَبْحا ً |
Fālssābiqāti Sabqāan | َ079-004 Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre. | فَالسَّابِقَاتِ سَبْقا ً |
Fālmudabbirāti 'Amrāan | َ079-005 Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. | فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرا ً |
Yawma Tarjufu Ar-Rājifahu | َ079-006 Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. | يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ |
Tatba`uhā Ar-Rādifahu | َ079-007 Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. | تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ |
Qulūbun Yawma'idhin Wājifahun | َ079-008 Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. | قُلُوب ٌ يَوْمَئِذ ٍ وَاجِفَة ٌ |
'Abşāruhā Khāshi`ahun | َ079-009 Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. | أَبْصَارُهَا خَاشِعَة ٌ |
Yaqūlūna 'A'innā Lamardūdūna Fī Al-Ĥāfirahi | َ079-010 Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? | يَقُولُونَ أَئِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ |
'A'idhā Kunnā `Ižāmāan Nakhirahan | َ079-011 "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" | أَئِذَا كُنَّا عِظَاما ً نَخِرَة ً |
Qālū Tilka 'Idhāan Karratun Khāsirahun | َ079-012 Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" | قَالُوا تِلْكَ إِذا ً كَرَّةٌ خَاسِرَة ٌ |
Fa'innamā Hiya Zajratun Wāĥidahun | َ079-013 To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. | فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَة ٌ وَاحِدَة ٌ |
Fa'idhā Hum Bis-Sāhirahi | َ079-014 Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. | فَإِذَا هُمْ بِالسَّاهِرَةِ |
Hal 'Tāka Ĥadīthu Mūsá | َ079-015 Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? | هَلْ أتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى |
'Idh Nādāhu Rabbuhu Bil-Wādi Al-Muqaddasi Ţūáan | َ079-016 A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? | إِذْ نَادَاه ُُ رَبُّه ُُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوى ً |
Adh/hab 'Ilá Fir`awna 'Innahu Ţaghá | َ079-017 Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. | اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّه ُُ طَغَى |
Faqul Hal Laka 'Ilá 'An Tazakká | َ079-018 "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. | فَقُلْ هَلْ لَكَ إِلَى أَنْ تَزَكَّى |
Wa 'Ahdiyaka 'Ilá Rabbika Fatakhshá | َ079-019 "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" | وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى |
Fa'arāhu Al-'Āyata Al-Kubrá | َ079-020 Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. | فَأَرَاهُ الآيَةَ الْكُبْرَى |
Fakadhdhaba Wa `Aşá | َ079-021 Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), | فَكَذَّبَ وَعَصَى |
Thumma 'Adbara Yas`á | َ079-022 Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. | ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى |
Faĥashara Fanādá | َ079-023 Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. | فَحَشَرَ فَنَادَى |
Faqāla 'Anā Rabbukumu Al-'A`lá | َ079-024 Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." | فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الأَعْلَى |
Fa'akhadhahu Al-Lahu Nakāla Al-'Ākhirati Wa Al-'Ūlá | َ079-025 Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. | فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الآخِرَةِ وَالأُولَى |
'Inna Fī Dhālika La`ibratan Liman Yakhshá | َ079-026 Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. | إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَة ً لِمَنْ يَخْشَى |
'A'antum 'Ashaddu Khalqāan 'Ami As-Samā'u ۚ Banāhā | َ079-027 Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. | أَأَنْتُمْ أَشَدُّ خَلْقاً أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَا |
Rafa`a Samkahā Fasawwāhā | َ079-028 Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. | رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا |
Wa 'Aghţasha Laylahā Wa 'Akhraja Đuĥāhā | َ079-029 Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. | وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا |
Wa Al-'Arđa Ba`da Dhālika Daĥāhā | َ079-030 Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. | وَالأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا |
'Akhraja Minhā Mā'ahā Wa Mar`āhā | َ079-031 Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. | أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا |
Wa Al-Jibāla 'Arsāhā | َ079-032 Da duwatsu, Yã kafe ta. | وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا |
Matā`āan Lakum Wa Li'an`āmikum | َ079-033 Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. | مَتَاعا ً لَكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ |
Fa'idhā Jā'ati Aţ-Ţāmmatu Al-Kubrá | َ079-034 To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. | فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى |
Yawma Yatadhakkaru Al-'Insānu Mā Sa`á | َ079-035 Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. | يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الإِنسَانُ مَا سَعَى |
Wa Burrizati Al-Jaĥīmu Liman Yará | َ079-036 Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. | وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَنْ يَرَى |
Fa'ammā Man Ţaghá | َ079-037 To, amma wanda ya yi girman kai. | فَأَمَّا مَنْ طَغَى |
Wa 'Āthara Al-Ĥayāata Ad-Dunyā | َ079-038 Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). | وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا |
Fa'inna Al-Jaĥīma Hiya Al-Ma'wá | َ079-039 To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. | فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى |
Wa 'Ammā Man Khāfa Maqāma Rabbihi Wa Nahá An-Nafsa `Ani Al-Hawá | َ079-040 Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. | وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّه ِِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى |
Fa'inna Al-Jannata Hiya Al-Ma'wá | َ079-041 To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. | فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى |
Yas'alūnaka `Ani As-Sā`ati 'Ayyāna Mursāhā | َ079-042 Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? | يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا |
Fīma 'Anta Min Dhikrāhā | َ079-043 Me ya haɗã ka da ambatonta? | فِيمَ أَنْتَ مِنْ ذِكْرَاهَا |
'Ilá Rabbika Muntahāhā | َ079-044 Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. | إِلَى رَبِّكَ مُنتَهَاهَا |
'Innamā 'Anta Mundhiru Man Yakhshāhā | َ079-045 Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. | إِنَّمَا أَنْتَ مُنذِرُ مَنْ يَخْشَاهَا |
Ka'annahum Yawma Yarawnahā Lam Yalbathū 'Illā `Ashīyatan 'Aw Đuĥāhā | َ079-046 Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. | كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلاَّ عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا |