78) Sūrat An-Naba'

Printed format

78)

`Amma Yatasā'alūna 078-001 A kan mẽ suke tambayar jũna?
`Ani An-Naba'i Al-`Ažīmi 078-002 A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
Al-Ladhī Hum Fīhi Mukhtalifūna 078-003 Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
Kallā Saya`lamūna 078-004 A'aha! Zã su sani.
Thumma Kallā Saya`lamūna 078-005 Kuma, a'aha! Zã su sani.
'Alam Naj`ali Al-'Arđa Mihādāan 078-006 Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
Wa Al-Jibāla 'Awtādāan 078-007 Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
Wa Khalaqnākum 'Azwājāan 078-008 Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
Wa Ja`alnā Nawmakum Subātāan 078-009 Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
Wa Ja`alnā Al-Layla Libāsāan 078-010 Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
Wa Ja`alnā An-Nahāra Ma`āshāan 078-011 Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
Wa Banaynā Fawqakum Sab`āan Shidādāan 078-012 Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
Wa Ja`alnā Sirājāan Wa Hhājāan 078-013 Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
Wa 'Anzalnā Mina Al-Mu`şirāti Mā'an Thajjājāan 078-014 Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
Linukhrija Bihi Ĥabbāan Wa Nabātāan 078-015 Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
Wa Jannātin 'Alfāfāan 078-016 Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
'Inna Yawma Al-Faşli Kāna Mīqātāan 078-017 Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
Yawma Yunfakhu Fī Aş-Şūri Fata'tūna 'Afwājāan 078-018 Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
Wa Futiĥati As-Samā'u Fakānat 'Abwābāan 078-019 Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
Wa Suyyirati Al-Jibālu Fakānat Sarābāan 078-020 Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
'Inna Jahannama Kānat Mirşādāan 078-021 Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
Lilţţāghīna Ma'āan 078-022 Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
Lābithīna Fīhā 'Aĥqābāan 078-023 Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
Lā Yadhūqūna Fīhā Bardāan Wa Lā Sharābāan 078-024 Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
'Illā Ĥamīmāan Wa Ghassāqāan 078-025 Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
Jazā'an Wifāqāan 078-026 Sakamako mai dãcẽwa.
'Innahum Kānū Lā Yarjūna Ĥisābāan 078-027 Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā Kidhdhābāan 078-028 Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
Wa Kulla Shay'in 'Aĥşaynāhu Kitābāan 078-029 Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
Fadhūqū Falan Nazīdakum 'Illā `Adhābāan 078-030 Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
'Inna Lilmuttaqīna Mafāzāan 078-031 Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
Ĥadā'iqa Wa 'A`nābāan 078-032 Lambuna da inabõbi.
Wa Kawā`iba 'Atrābāan 078-033 Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
Wa Ka'sāan Dihāqāan 078-034 Da hinjãlan giya cikakku.
Lā Yasma`ūna Fīhā Laghwan Wa Lā Kidhdhābāan 078-035 Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
Jazā'an Min Rabbika `Aţā'an Ĥisābāan 078-036 Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
Rabbi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Ar-Raĥmāni  ۖ  Lā Yamlikūna Minhu Khiţābāan 078-037 Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.  ۖ 
Yawma Yaqūmu Ar-Rūĥu Wa Al-Malā'ikatu Şaffāan  ۖ  Lā Yatakallamūna 'Illā Man 'Adhina Lahu Ar-Raĥmānu Wa Qāla Şawābāan 078-038 Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.  ۖ 
Dhālika Al-Yawmu Al-Ĥaqqu  ۖ  Faman Shā'a Attakhadha 'Ilá Rabbihi Ma'āan 078-039 Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.  ۖ 
'Innā 'Andharnākum `Adhābāan Qarībāan Yawma Yanžuru Al-Mar'u Mā Qaddamat Yadāhu Wa Yaqūlu Al-Kāfiru Yā Laytanī Kuntu Turābāan 078-040 Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"
Next Sūrah