77) Sūratālmursalāt

Printed format

77)

Wa Al-Mursalāti `Urfāan 077-001 Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
Fāl`āşifāti `Aşfāan 077-002 Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
Wa An-Nāshirāti Nashan 077-003 Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
Fālfāriqāti Farqāan 077-004 sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
Fālmulqiyāti Dhikrāan 077-005 Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
`Udhrāan 'Aw Nudhan 077-006 Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
'Innamā Tū`adūna Lawāqi`un 077-007 Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
Fa'idhā An-Nujūmu Ţumisat 077-008 To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
Wa 'Idhā As-Samā'u Furijat 077-009 Kuma, idan sama aka tsãge ta.
Wa 'Idhā Al-Jibālu Nusifat 077-010 Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
Wa 'Idhā Ar-Rusulu 'Uqqitat 077-011 Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
L'ayyi Yawmin 'Ujjilat 077-012 Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
Liyawmi Al-Faşli 077-013 Domin rãnar rarrabẽwa .
Wa Mā 'Adrāka Mā Yawmu Al-Faşli 077-014 Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-015 Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
'Alam Nuhliki Al-'Awwalīna 077-016 Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
Thumma Nutbi`uhumu Al-'Ākhirīna 077-017 Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
Kadhālika Naf`alu Bil-Mujrimīna 077-018 Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-019 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
'Alam Nakhluqkum Min Mā'in Mahīnin 077-020 Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
Faja`alnāhu Fī Qarārin Makīnin 077-021 Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
'Ilá Qadarin Ma`lūmin 077-022 Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
Faqadarnā Fani`ma Al-Qādirūna 077-023 Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-024 Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
'Alam Naj`ali Al-'Arđa Kifātāan 077-025 Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
'Aĥyā'an Wa 'Amwātāan 077-026 Ga rãyayyu da matattu,
Wa Ja`alnā Fīhā Rawāsiya Shāmikhātin Wa 'Asqaynākum Mā'an Furātāan 077-027 Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-028 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Anţaliqū 'Ilá Mā Kuntum Bihi Tukadhdhibūna 077-029 Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
Anţaliqū 'Ilá Žillin Dhī Thalāthi Shu`abin 077-030 Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
Lā Žalīlin Wa Lā Yughnī Mina Al-Lahabi 077-031 Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
'Innahā Tarmī Bishararin Kālqaşri 077-032 Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
Ka'annahu Jimālatun Şufrun 077-033 Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-034 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
dhā Yawmu Lā Yanţiqūna 077-035 Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
Wa Lā Yu'udhanu Lahum Faya`tadhirūna 077-036 Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-037 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
dhā Yawmu Al-Faşli  ۖ  Jama`nākum Wa Al-'Awwalīna 077-038 Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.  ۖ 
Fa'in Kāna Lakum Kaydun Fakīdūni 077-039 To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-040 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
'Inna Al-Muttaqīna Fī Žilālin Wa `Uyūnin 077-041 Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
Wa Fawākiha Mimmā Yashtahūna 077-042 Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
Kulū Wa Ashrabū Hanī'āan Bimā Kuntum Ta`malūna 077-043 (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
'Innā Kadhālika Naj Al-Muĥsinyna 077-044 Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-045 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Kulū Wa Tamatta`ū Qalīlāan 'Innakum Mujrimūna 077-046 (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-047 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Wa 'Idhā Qīla Lahumu Arka`ū Lā Yarka`ūna 077-048 Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
Waylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 077-049 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Fabi'ayyi Ĥadīthin Ba`dahu Yu'uminūna 077-050 To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
Next Sūrah