76) Sūrat Al-'Inn

Printed format

76)

Hal 'Atá `Alá Al-'Insāni Ĥīnun Mina Ad-Dahri Lam Yakun Shay'āan Madhkūrāan 076-001 Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
'Innā Khalaq Al-'Insāna Min Nuţfatin 'Amshājin Nabtalīhi Faja`alnāhu Samī`āan Başīrāan 076-002 Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
'Innā Hadaynāhu As-Sabīla 'Immā Shākirāan Wa 'Immā Kafūrāan 076-003 Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
'Innā 'A`tadnā Lilkāfirīna Salāsilāan Wa 'Aghlālāan Wa Sa`īrāan 076-004 Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
'Inna Al-'Abrāra Yashrabūna Min Ka'sin Kāna Mizājuhā Kāfūrāan 076-005 Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
`Aynāan Yashrabu Bihā `Ibādu Al-Lahi Yufajjirūnahā Tafjīrāan 076-006 Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
Yūfūna Bin-Nadhri Wa Yakhāfūna Yawmāan Kāna Sharruhu Mustaţīrāan 076-007 Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
Wa Yuţ`imūna Aţ-Ţa`āma `Alá Ĥubbihi Miskīnāan Wa Yatīmāan Wa 'Asīrāan 076-008 Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
'Innamā Nuţ`imukum Liwajhi Al-Lahi Lā Nurīdu Minkum Jazā'an Wa Lā Shukūrāan 076-009 (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
'Innā Nakhāfu Min Rabbinā Yawmāan `Abūsāan Qamţarīrāan 076-010 "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa."
Fawaqāhumu Al-Lahu Sharra Dhālika Al-Yawmi Wa Laqqāhum Nađratan Wa Surūrāan 076-011 Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
Wa Jazāhum Bimā Şabarū Jannatan Wa Ĥarīrāan 076-012 Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
Muttaki'īna Fīhā `Alá Al-'Arā'iki  ۖ  Lā Yarawna Fīhā Shamsāan Wa Lā Zamharīrāan 076-013 Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.  ۖ 
Wa Dāniyatan `Alayhim Žilāluhā Wa Dhullilat Quţūfuhā Tadhlīlāan 076-014 Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
Wa Yuţāfu `Alayhim Bi'āniyatin Min Fiđđatin Wa 'Akwābin Kānat Qawārīra 076-015 Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
Qawārīra Min Fiđđatin Qaddarūhā Taqdīrāan 076-016 ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
Wa Yusqawna Fīhā Ka'sāan Kāna Mizājuhā Zanjabīlāan 076-017 Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
`Aynāan Fīhā Tusammá Salsabīlāan 076-018 Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
Wa Yaţūfu `Alayhim Wildānun Mukhalladūna 'Idhā Ra'aytahum Ĥasibtahum Lu'ulu'uāan Manthūrāan 076-019 Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
Wa 'Idhā Ra'ayta Thamma Ra'ayta Na`īmāan Wa Mulkāan Kabīrāan 076-020 Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
`Āliyahum Thiyābu Sundusin Khuđrun Wa 'Istabraqun  ۖ  Wa Ĥullū 'Asāwira Min Fiđđatin Wa Saqāhum Rabbuhum Sharābāan Ţahūrāan 076-021 Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki).  ۖ 
'Inna Hādhā Kāna Lakum Jazā'an Wa Kāna Sa`yukum Mashkūrāan 076-022 (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa."
'Innā Naĥnu Nazzalnā `Alayka Al-Qur'āna Tanzīlāan 076-023 Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
Fāşbir Liĥukmi Rabbika Wa Lā Tuţi` Minhum 'Āthimāan 'Aw Kafūrāan 076-024 Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
Wa Adhkur Asma Rabbika Bukratan Wa 'Aşīlāan 076-025 Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
Wa Mina Al-Layli Fāsjud Lahu Wa Sabbiĥhu Laylāan Ţawīlāan 076-026 Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
'Inna Hā'uulā' Yuĥibbūna Al-`Ājilata Wa Yadharūna Warā'ahum Yawmāan Thaqīlāan 076-027 Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
Naĥnu Khalaqnāhum Wa Shadadnā 'Asrahum  ۖ  Wa 'Idhā Shi'nā Baddalnā 'Amthālahum Tabdīlāan 076-028 Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musany su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.  ۖ 
'Inna Hadhihi Tadhkiratun  ۖ  Faman Shā'a Attakhadha 'Ilá Rabbihi Sabīlāan 076-029 Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.  ۖ 
Wa Mā Tashā'ūna 'Illā 'An Yashā'a Al-Lahu  ۚ  'Inna Al-Laha Kāna `Alīmāan Ĥakīmāan 076-030 Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.  ۚ 
Yudkhilu Man Yashā'u Fī Raĥmatihi Wa  ۚ  Až-Žālimīna 'A`adda Lahum `Adhābāan 'Alīmāan 076-031 Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.  ۚ 
Next Sūrah