72) Sūrat Al-Jinn

Printed format

72) سُورَة الجِنّ

Qul 'Ūĥiya 'Ilayya 'Annahu Astama`a Nafarun Mina Al-Jinni Faqālū 'Innā Sami`nā Qur'ānāan `Ajabāan َ072-001 Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki." قُلْ أُوحِيَ إِلَيَّ أَنَّهُ اسْتَمَعَ نَفَر ٌ مِنَ الْجِنِّ فَقَالُوا إِنَّا سَمِعْنَا قُرْآناً عَجَبا ً
Yahdī 'Ilá Ar-Rushdi Fa'āmannā Bihi  ۖ  Wa Lan Nushrika Birabbinā 'Aĥadāan َ072-002 "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba." يَهْدِي إِلَى الرُّشْدِ فَآمَنَّا بِه ِِ  ۖ  وَلَنْ نُشْرِكَ بِرَبِّنَا أَحَدا ً
Wa 'Annahu Ta`ālá Jaddu Rabbinā Mā Attakhadha Şāĥibatan Wa Lā Waladāan َ072-003 "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba." وَأَنَّه ُُ تَعَالَى جَدُّ رَبِّنَا مَا اتَّخَذَ صَاحِبَة ً وَلاَ وَلَدا ً
Wa 'Annahu Kāna Yaqūlu Safīhunā `Alá Al-Lahi Shaţaţāan َ072-004 "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah." وَأَنَّه ُُ كَانَ يَقُولُ سَفِيهُنَا عَلَى اللَّهِ شَطَطا ً
Wa 'Annā Žanannā 'An Lan Taqūla Al-'Insu Wa Al-Jinnu `Alá Al-Lahi Kadhibāan َ072-005 "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah." وَأَنَّا ظَنَنَّا أَنْ لَنْ تَقُولَ الإِنسُ وَالْجِنُّ عَلَى اللَّهِ كَذِبا ً
Wa 'Annahu Kāna Rijālun Mina Al-'Insi Ya`ūdhūna Birijālin Mina Al-Jinni Fazādūhum Rahaqāan َ072-006 "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai." وَأَنَّه ُُ كَانَ رِجَال ٌ مِنَ الإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَال ٍ مِنَ الْجِنِّ فَزَادُوهُمْ رَهَقا ً
Wa 'Annahum Žannū Kamā Žanantum 'An Lan Yab`atha Al-Lahu 'Aĥadāan َ072-007 "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba." وَأَنَّهُمْ ظَنُّوا كَمَا ظَنَنتُمْ أَنْ لَنْ يَبْعَثَ اللَّهُ أَحَدا ً
Wa 'Annā Lamasnā As-Samā'a Fawajadnāhā Muli'at Ĥarasāan Shadīdāan Wa Shuhubāan َ072-008 "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye." وَأَنَّا لَمَسْنَا السَّمَاءَ فَوَجَدْنَاهَا مُلِئَتْ حَرَسا ً شَدِيدا ً وَشُهُبا ً
Wa 'Annā Kunnā Naq`udu Minhā Maqā`ida Lilssam`i  ۖ  Faman Yastami`i Al-'Āna Yajid Lahu Shihābāan Raşadāan َ072-009 "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa." وَأَنَّا كُنَّا نَقْعُدُ مِنْهَا مَقَاعِدَ لِلسَّمْعِ  ۖ  فَمَنْ يَسْتَمِعِ الآنَ يَجِدْ لَه ُُ شِهَابا ً رَصَدا ً
Wa 'Annā Lā Nadrī 'Asharrun 'Urīda Biman Al-'Arđi 'Am 'Arāda Bihim Rabbuhum Rashadāan َ072-010 "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?" وَأَنَّا لاَ نَدْرِي أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَنْ فِي الأَرْضِ أَمْ أَرَادَ بِهِمْ رَبُّهُمْ رَشَدا ً
Wa 'Annā Minnā Aş-Şāliĥūna Wa Minnā Dūna Dhālika  ۖ  Kunnā Ţarā'iqa Qidadāan َ072-011 "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam." وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَلِكَ  ۖ  كُنَّا طَرَائِقَ قِدَدا ً
Wa 'Annā Žanannā 'An Lan Nu`jiza Al-Laha Fī Al-'Arđi Wa Lan Nu`jizahu Harabāan َ072-012 "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba." وَأَنَّا ظَنَنَّا أَنْ لَنْ نُعجِزَ اللَّهَ فِي الأَرْضِ وَلَنْ نُعْجِزَه ُُ هَرَبا ً
Wa 'Annā Lammā Sami`nā Al-Hudá 'Āmannā Bihi  ۖ  Faman Yu'umin Birabbihi Falā Yakhāfu Bakhsāan Wa Lā Rahaqāan َ072-013 "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba." وَأَنَّا لَمَّا سَمِعْنَا الْهُدَى آمَنَّا بِه ِِ  ۖ  فَمَنْ يُؤْمِنْ بِرَبِّه ِِ فَلاَ يَخَافُ بَخْسا ً وَلاَ رَهَقا ً
Wa 'Annā Minnā Al-Muslimūna Wa Minnā Al-Qāsiţūna  ۖ  Faman 'Aslama Fa'ūlā'ika Taĥarraw Rashadāan َ072-014 "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa." وَأَنَّا مِنَّا الْمُسْلِمُونَ وَمِنَّا الْقَاسِطُونَ  ۖ  فَمَنْ أَسْلَمَ فَأُوْلَائِكَ تَحَرَّوْا رَشَدا ً
Wa 'Ammā Al-Qāsiţūna Fakānū Lijahannama Ĥaţabāan َ072-015 "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama." وَأَمَّا الْقَاسِطُونَ فَكَانُوا لِجَهَنَّمَ حَطَبا ً
Wa 'Allawi Astaqāmū `Alá Aţ-Ţarīqati L'asqaynāhum Mā'an Ghadaqāan َ072-016 "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa." وَأَلَّوِ اسْتَقَامُوا عَلَى الطَّرِيقَةِ لأَسْقَيْنَاهُمْ مَاءً غَدَقا ً
Linaftinahum Fīhi  ۚ  Wa Man Yu`riđ `An Dhikri Rabbihi Yasluk/hu `Adhābāan Şa`adāan َ072-017 "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa." لِنَفْتِنَهُمْ فِيه ِِ  ۚ  وَمَنْ يُعْرِضْ عَنْ ذِكْرِ رَبِّه ِِ يَسْلُكْهُ عَذَابا ً صَعَدا ً
Wa 'Anna Al-Masājida Lillahi Falā Tad`ū Ma`a Al-Lahi 'Aĥadāan َ072-018 "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)." وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلاَ تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدا ً
Wa 'Annahu Lammā Qāma `Abdu Al-Lahi Yad`ūhu Kādū Yakūnūna `Alayhi Libadāan َ072-019 "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa." وَأَنَّه ُُ لَمَّا قَامَ عَبْدُ اللَّهِ يَدْعُوه ُُ كَادُوا يَكُونُونَ عَلَيْهِ لِبَدا ً
Qul 'Innamā 'Ad`ū Rabbī Wa Lā 'Ushriku Bihi 'Aĥadāan َ072-020 Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba." قُلْ إِنَّمَا أَدْعُو رَبِّي وَلاَ أُشْرِكُ بِهِ~ِ أَحَدا ً
Qul 'Innī Lā 'Amliku Lakum Đarrāan Wa Lā Rashadāan َ072-021 Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri." قُلْ إِنِّي لاَ أَمْلِكُ لَكُمْ ضَرّا ً وَلاَ رَشَدا ً
Qul 'Innī Lan Yujīranī Mina Al-Lahi 'Aĥadun Wa Lan 'Ajida Min Dūnihi Multaĥadāan َ072-022 Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi." قُلْ إِنِّي لَنْ يُجِيرَنِي مِنَ اللَّهِ أَحَد ٌ وَلَنْ أَجِدَ مِنْ دُونِه ِِ مُلْتَحَدا ً
'Illā Balāghāan Mina Al-Lahi Wa Risālātihi  ۚ  Wa Man Ya`şi Al-Laha Wa Rasūlahu Fa'inna Lahu Nāra Jahannama Khālidīna Fīhā 'Abadāan َ072-023 "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada." إِلاَّ بَلاَغا ً مِنَ اللَّهِ وَرِسَالاَتِه ِِ  ۚ  وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ فَإِنَّ لَه ُُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدا ً
Ĥattá 'Idhā Ra'aw Mā Yū`adūna Fasaya`lamūna Man 'Ađ`afu Nāşirāan Wa 'Aqallu `Adadāan َ072-024 Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi. حَتَّى إِذَا رَأَوْا مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ أَضْعَفُ نَاصِرا ً وَأَقَلُّ عَدَدا ً
Qul 'In 'Adrī 'Aqarībun Mā Tū`adūna 'Am Yaj`alu Lahu Rabbī 'Amadāan َ072-025 Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!" قُلْ إِنْ أَدْرِي أَقَرِيب ٌ مَا تُوعَدُونَ أَمْ يَجْعَلُ لَه ُُ رَبِّي أَمَدا ً
`Ālimu Al-Ghaybi Falā Yužhiru `Alá Ghaybihi 'Aĥadāan َ072-026 "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa." عَالِمُ الْغَيْبِ فَلاَ يُظْهِرُ عَلَى غَيْبِهِ~ِ أَحَدا ً
'Illā Mani Artađá Min Rasūlin Fa'innahu Yasluku Min Bayni Yadayhi Wa Min Khalfihi Raşadāan َ072-027 "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi." إِلاَّ مَنِ ارْتَضَى مِنْ رَسُول ٍ فَإِنَّه ُُ يَسْلُكُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِه ِِ رَصَدا ً
Liya`lama 'An Qad 'Ablaghū Risālāti Rabbihim Wa 'Aĥāţa Bimā Ladayhim Wa 'Aĥşá Kulla Shay'in `Adadāan َ072-028 "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga." لِيَعْلَمَ أَنْ قَدْ أَبْلَغُوا رِسَالاَتِ رَبِّهِمْ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيْهِمْ وَأَحْصَى كُلَّ شَيْءٍ عَدَدا ً
Next Sūrah