73) Sūrat Al-Muzzammil

Printed format

73)

Yā 'Ayyuhā Al-Muzzammilu 073-001 Yã wanda ya lulluɓe!
Qumi Al-Layla 'Illā Qalīlāan 073-002 Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
Nişfahu 'Aw Anquş Minhu Qalīlāan 073-003 Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi. ~
'Aw Zid `Alayhi Wa Rattili Al-Qur'āna Tartīlāan 073-004 Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.
'Innā Sanulqī `Alayka Qawlāan Thaqīlāan 073-005 Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
'Inna Nāshi'ata Al-Layli Hiya 'Ashaddu Waţ'āan Wa 'Aqwamu Qīlāan 073-006 Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.
'Inna Laka Fī Aalnnahāri Sabĥāan Ţawīlāan 073-007 Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
Wa Adhkur Asma Rabbika Wa Tabattal 'Ilayhi Tabtīlāan 073-008 Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.
Rabbu Al-Mashriqi Wa Al-Maghribi Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Fa Attakhidh/hu Wa Kīlāan 073-009 Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili. ~
Wa Aşbir `Alá Mā Yaqūlūna Wa Ahjurhum Hajrāan Jamīlāan 073-010 Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.
Wa Dharnī Wa Al-Mukadhdhibīna 'Ū An-Na`mati Wa Mahhilhum Qalīlāan 073-011 Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
'Inna Ladaynā 'Ankālāan Wa Jaĥīmāan 073-012 Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
Wa Ţa`āmāan Dhā Ghuşşatin Wa `Adhābāan 'Alīmāan 073-013 Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
Yawma Tarjufu Al-'Arđu Wa Al-Jibālu Wa Kānati Al-Jibālu Kathībāan Mahīlāan 073-014 Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.
'Innā 'Arsalnā 'Ilaykum Rasūlāan Shāhidāan `Alaykum Kamā 'Arsalnā 'Ilá Fir`awna Rasūlāan 073-015 Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo zuwaga Fir'auna,
Fa`aşá Fir`awnu Ar-Rasūla Fa'akhadhnāhu 'Akhdhāan Wabīlāan 073-016 Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani. ~
Fakayfa Tattaqūna 'In Kafartum Yawmāan Yaj`alu Al-Wildāna Shībāan 073-017 To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.
As-Samā'u Munfaţirun Bihi  ۚ  Kāna Wa`duhu Maf`ūlāan 073-018 Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.  ۚ 
'Inna Hadhihi Tadhkiratun  ۖ  Faman Shā'a Attakhadha 'Ilá Rabbihi Sabīlāan 073-019 Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.  ۖ 
'Inna Rabbaka Ya`lamu 'Annaka Taqūmu 'Adná Min Thuluthayi Al-Layli Wa Nişfahu Wa Thuluthahu Wa Ţā'ifatun Mina Al-Ladhīna Ma`aka Wa  ۚ  Allāhu Yuqaddiru Al-Layla Wa An-Nahāra  ۚ  `Alima 'An Lan Tuĥşūhu Fatāba `Alaykum  ۖ  Fāqra'ū Mā Tayassara Mina Al-Qur'āni  ۚ  `Alima 'An Sayakūnu Minkum Marđá  ۙ  Wa 'Ākharūna Yađribūna Fī Al-'Arđi Yabtaghūna Min Fađli Al-Lahi  ۙ  Wa 'Ākharūna Yuqātilūna Fī Sabīli Al-Lahi  ۖ  Fāqra'ū Mā Tayassara Minhu  ۚ  Wa 'Aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ā Az-Zakāata Wa 'Aqriđū Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan  ۚ  Wa Mā Tuqaddimū Li'nfusikum Min Khayrin Tajidūhu `Inda Al-Lahi Huwa Khayrāan Wa 'A`žama 'Ajrāan  ۚ  Wa Astaghfirū Al-Laha  ۖ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 073-020 Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ   ۖ   ۚ   ۙ   ۙ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ 
Next Sūrah