69) Sūrat Al-Ĥāqqah

Printed format

69)

Al-Ĥāqqahu 069-001 Kiran gaskiya!
Al-Ĥāqqahu 069-002 Mẽne ne kiran gaskiya?
Wa Mā 'Adrāka Mā Al-Ĥāqqahu 069-003 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
Kadhdhabat Thamūdu Wa `Ādun Bil-Qāri`ahi 069-004 Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
Fa'ammā Thamūdu Fa'uhlikū Biţ-Ţāghiyahi 069-005 To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
Wa 'Ammā `Ādun Fa'uhlikū Birīĥin Şarşarin `Ātiyahin 069-006 Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
Sakhkharahā `Alayhim Sab`a Layālin Wa Thamāniyata 'Ayyāmin Ĥusūmāan Fatará Al-Qawma Fīhā Şar`á Ka'annahum 'A`jāzu Nakhlin Khāwiyahin 069-007 (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
Fahal Tará Lahum Min Bāqiyahin 069-008 To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
Wa Jā'a Fir`awnu Wa Man Qablahu Wa Al-Mu'utafikātu Bil-Khāţi'ahi 069-009 Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
Fa`aşaw Rasūla Rabbihim Fa'akhadhahum 'Akhdhatan Rābiyahan 069-010 Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
'Innā Lammā Ţaghá Al-Mā'u Ĥamalnākum Al-Jāriyahi 069-011 Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
Linaj`alahā Lakum Tadhkiratan Wa Ta`iyahā 'Udhunun Wā`iyahun 069-012 Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
Fa'idhā Nufikha Fī Aş-Şūri Nafkhatun Wāĥidahun 069-013 To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
Wa Ĥumilati Al-'Arđu Wa Al-Jibālu Fadukkatā Dakkatan Wāĥidahan 069-014 Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
Fayawma'idhin Waqa`ati Al-Wāqi`ahu 069-015 A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
Wa Anshaqqati As-Samā'u Fahiya Yawma'idhin Wa Ahiyahun 069-016 Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
Wa Al-Malaku `Alá  ۚ  'Arjā'ihā Wa Yaĥmilu `Arsha Rabbika Fawqahum Yawma'idhin Thamāniyahun 069-017 Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.  ۚ 
Yawma'idhin Tu`rađūna Lā Takhfá Minkum Khāfiyahun 069-018 A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
Fa'ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Biyamīnihi Fayaqūlu Hā'uum Aqra'ū Kitābī 069-019 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."
'Innī Žanantu 'Annī Mulāqin Ĥisābiyah 069-020 "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
Fahuwa Fī `Īshatin Rāđiyahin 069-021 Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
Fī Jannatin `Āliyahin 069-022 A cikin Aljanna maɗaukakiya.
Quţūfuhā Dāniyahun 069-023 Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
Kulū Wa Ashrabū Hanī'āan Bimā 'Aslaftum Al-'Ayyāmi Al-Khāliyahi 069-024 (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."
Wa 'Ammā Man 'Ūtiya Kitābahu Bishimālihi Fayaqūlu Yā Laytanī Lam 'Ūta Kitābīh 069-025 Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"
Wa Lam 'Adri Mā Ĥisābīh 069-026 "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
Yā Laytahā Kānati Al-Qāđiyaha 069-027 "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
Mā 'Aghná `Annī Mālīh  ۜ  069-028 "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
Halaka `Annī Sulţānīh 069-029 "Ĩkona ya ɓace mini!"
Khudhūhu Faghullūhu 069-030 (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
Thumma Al-Jaĥīma Şallūhu 069-031 "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
Thumma Fī Silsilatin Dhar`uhā Sab`ūna Dhirā`āan Fāslukūhu 069-032 "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."
'Innahu Kāna Lā Yu'uminu Bil-Lahi Al-`Ažīmi 069-033 "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
Wa Lā Yaĥuđđu `Alá Ţa`āmi Al-Miskīni 069-034 "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
Falaysa Lahu Al-Yawma Hāhunā Ĥamīmun 069-035 "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
Wa Lā Ţa`āmun 'Illā Min Ghislīnin 069-036 "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
Lā Ya'kuluhu 'Illā Al-Khāţi'ūna 069-037 "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." ~
Falā 'Uqsimu Bimā Tubşirūna 069-038 To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
Wa Mā Lā Tubşirūna 069-039 Da abin da bã ku iya gani.
'Innahu Laqawlu Rasūlin Karīmin 069-040 Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
Wa Mā Huwa Biqawli Shā`irin  ۚ  Qalīlāan Mā Tu'uminūna 069-041 Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.  ۚ 
Wa Lā Biqawli Kāhinin  ۚ  Qalīlāan Mā Tadhakkarūna 069-042 Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.  ۚ 
Tanzīlun Min Rabbi Al-`Ālamīna 069-043 Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
Wa Law Taqawwala `Alaynā Ba`đa Al-'Aqāwīli 069-044 Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
La'akhadhnā Minhu Bil-Yamīni 069-045 Dã Mun kãma shi da dãma.
Thumma Laqaţa`nā Minhu Al-Watīna 069-046 sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
Famā Minkum Min 'Aĥadin `Anhu Ĥājizīna 069-047 Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
Wa 'Innahu Latadhkiratun Lilmuttaqīna 069-048 Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
Wa 'Innā Lana`lamu 'Anna Minkum Mukadhdhibīna 069-049 Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
Wa 'Innahu Laĥasratun `Alá Al-Kāfirīna 069-050 Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
Wa 'Innahu Laĥaqqu Al-Yaqīni 069-051 Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
Fasabbiĥ Biāsmi Rabbika Al-`Ažīmi 069-052 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
Next Sūrah