70) Sūrat Al-Ma`ārij

Printed format

70)

Sa'ala Sā'ilun Bi`adhābin Wāqi`in 070-001 Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
Lilkāfiryna Laysa Lahu Dāfi`un 070-002 Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
Mina Al-Lahi Dhī Al-Ma`āriji 070-003 Daga Allah Mai matãkala.
Ta`ruju Al-Malā'ikatu Wa Ar-Rūĥu 'Ilayhi Fī Yawmin Kāna Miqdāruhu Khamsīna 'Alfa Sanahin 070-004 Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
Fāşbir Şabrāan Jamīlāan 070-005 Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
'Innahum Yarawnahu Ba`īdāan 070-006 Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
Wa Narāhu Qarībāan 070-007 Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
Yawma Takūnu As-Samā'u Kālmuhli 070-008 Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
Wa Takūnu Al-Jibālu Kāl`ihni 070-009 Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
Wa Lā Yas'alu Ĥamīmun Ĥamīmāan 070-010 Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
Yubaşşarūnahum  ۚ  Yawaddu Al-Mujrimu Law Yaftadī Min `Adhābi Yawmi'idhin Bibanīhi 070-011 Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,  ۚ 
Wa Şāĥibatihi Wa 'Akhīhi 070-012 Da matarsa da ɗan'uwansa.
Wa Faşīlatihi Allatī Tu'uwyhi 070-013 Da danginsa, mãsu tattarã shi.
Wa Man Al-'Arđi Jamī`āan Thumma Yunjīhi 070-014 Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
Kallā  ۖ  'Innahā Lažá 070-015 A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,  ۖ 
Nazzā`atan Lilshshawá 070-016 Mai twãle fãtar goshi.
Tad`ū Man 'Adbara Wa Tawallá 070-017 Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
Wa Jama`a Fa'aw`á 070-018 Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
'Inna Al-'Insāna Khuliqa Halū`āan 070-019 Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
'Idhā Massahu Ash-Sharru Jazū`āan 070-020 Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
Wa 'Idhā Massahu Al-Khayru Manū`āan 070-021 Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
'Illā Al-Muşallīna 070-022 Sai mãsu yin salla,
Al-Ladhīna Hum `Alá Şalātihim Dā'imūna 070-023 Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
Wa Al-Ladhīna Fī 'Amwālihim Ĥaqqun Ma`lūmun 070-024 Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
Lilssā'ili Wa Al-Maĥrūmi 070-025 Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
Wa Al-Ladhīna Yuşaddiqūna Biyawmi Ad-Dīni 070-026 Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
Wa Al-Ladhīna Hum Min `Adhābi Rabbihim Mushfiqūna 070-027 Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
'Inna `Adhāba Rabbihim Ghayru Ma'mūnin 070-028 Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
Wa Al-Ladhīna Hum Lifurūjihim Ĥāfižūna 070-029 Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
'Illā `Alá 'Azwājihim 'Aw Mā Malakat 'Aymānuhum Fa'innahum Ghayru Malūmīna 070-030 Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
Famani Abtaghá Warā'a Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-`Ādūna 070-031 To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
Wa Al-Ladhīna Hum Li'mānātihim Wa `Ahdihim Rā`ūna 070-032 Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
Wa Al-Ladhīna Hum Bishahādātihim Qā'imūna 070-033 Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
Wa Al-Ladhīna Hum `Alá Şalātihim Yuĥāfižūna 070-034 Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
'Ūlā'ika Fī Jannātin Mukramūna 070-035 Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
Famāli Al-Ladhīna Kafarū Qibalaka Muhţi`īna 070-036 Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
`Ani Al-Yamīni Wa `Ani Ash-Shimāli `Izīna 070-037 Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
'Ayaţma`u Kullu Amri'in Minhum 'An Yudkhala Jannata Na`īmin 070-038 Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
Kallā  ۖ  'Innā Khalaqnāhum Mimmā Ya`lamūna 070-039 A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.  ۖ 
Falā 'Uqsimu Birabbi Al-Mashāriqi Wa Al-Maghāribi 'Innā Laqādirūna 070-040 Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
`Alá 'An Nubaddila Khayrāan Minhum Wa Mā Naĥnu Bimasbūqīna 070-041 Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
Fadharhum Yakhūđū Wa Yal`abū Ĥattá Yulāqū Yawmahumu Al-Ladhī Yū`adūna 070-042 Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita) .
Yawma Yakhrujūna Mina Al-'Ajthi Sirā`āan Ka'annahum 'Ilá Nuşubin Yūfiđūna 070-043 Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
Khāshi`atan 'Abşāruhum Tarhaquhum Dhillatun  ۚ  Dhālika Al-Yawmu Al-Ladhī Kānū Yū`adūna 070-044 Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)  ۚ 
Next Sūrah