68) Sūrat Al-Qalam

Printed format

68)

n Wa Al-Qalami Wa Mā Yasţurūna 068-001 Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
Mā 'Anta Bini`mati Rabbika Bimajnūnin 068-002 Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
Wa 'Inna Laka La'ajrāan Ghayra Mamnūnin 068-003 Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
Wa 'Innaka La`alá Khuluqin `Ažīmin 068-004 Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
Fasatubşiru Wa Yubşirūna 068-005 Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
Bi'ayyyikumu Al-Maftūnu 068-006 Ga wanenku haukã take.
'Inna Rabbaka Huwa 'A`lamu Biman Đalla `An Sabīlihi Wa Huwa 'A`lamu Bil-Muhtadīna 068-007 Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
Falā Tuţi`i Al-Mukadhdhibīna 068-008 Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
Wa Ddū Law Tud/hinu Fayud/hinūna 068-009 Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
Wa Lā Tuţi` Kulla Ĥallāfin Mahīnin 068-010 Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
Hammāzin Mashshā'in Binamīmin 068-011 Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
Mannā`in Lilkhayri Mu`tadin 'Athīmin 068-012 Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
`Utullin Ba`da Dhālika Zanīmin 068-013 Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi ( bã ya son alhẽri).
'An Kāna Dhā Mālin Wa Banīna 068-014 Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
'Idhā Tutlá `Alayhi 'Āyātunā Qāla 'Asāţīru Al-'Awwalīna 068-015 Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
Sanasimuhu `Alá Al-Khurţūmi 068-016 Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
'Innā Balawnāhum Kamā Balawnā 'Aşĥāba Al-Jannati 'Idh 'Aqsamū Layaşrimunnahā Muşbiĥīna 068-017 Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
Wa Lā Yastathnūna 068-018 Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
Faţāfa `Alayhā Ţā'ifun Min Rabbika Wa Hum Nā'imūna 068-019 Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, ( ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
Fa'aşbaĥat Kālşşarīmi 068-020 Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
Fatanādaw Muşbiĥīna 068-021 Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
'Ani Aghdū `Alá Ĥarthikum 'In Kuntum Şārimīna 068-022 Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
nţalaqū Wa Hum Yatakhāfatūna 068-023 Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
'An Lā Yadkhulannahā Al-Yawma `Alaykum Miskīnun 068-024 "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
Waghadaw `Alá Ĥardin Qādirīna 068-025 Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
Falammā Ra'awhā Qālū 'Innā Lađāllūna 068-026 Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
Bal Naĥnu Maĥrūmūna 068-027 "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
Qāla 'Awsaţuhum 'Alam 'Aqul Lakum Lawlā Tusabbiĥūna 068-028 Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
Qālū Subĥāna Rabbinā 'Innā Kunnā Žālimīna 068-029 Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
Fa'aqbala Ba`đuhum `Alá Ba`đin Yatalāwamūna 068-030 Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
Qālū Yā Waylanā 'Innā Kunnā Ţāghīna 068-031 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
`Asá Rabbunā 'An Yubdilanā Khayrāan Minhā 'Innā 'Ilá Rabbinā Rāghibūna 068-032 "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
Kadhālika Al-`Adhābu  ۖ  Wa La`adhābu Al-'Ākhirati 'Akbaru  ۚ  Law Kānū Ya`lamūna 068-033 Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.  ۖ   ۚ 
'Inna Lilmuttaqīna `Inda Rabbihim Jannāti An-Na`īmi 068-034 Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
'Afanaj`alu Al-Muslimīna Kālmujrimīna 068-035 Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
Mā Lakum Kayfa Taĥkumūna 068-036 Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
'Am Lakum Kitābun Fīhi Tadrusūna 068-037 Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
'Inna Lakum Fīhi Lamā Takhayyarūna 068-038 Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
'Am Lakum 'Aymānun `Alaynā Bālighatun 'Ilá Yawmi Al-Qiyāmati  ۙ  'Inna Lakum Lamā Taĥkumūna 068-039 Kõ kunã ( riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?  ۙ 
Salhum 'Ayyuhum Bidhālika Za`īmun 068-040 Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
'Am Lahum Shurakā'u Falya'tū Bishurakā'ihim 'In Kānū Şādiqīna 068-041 Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
Yawma Yukshafu `An Sāqin Wa Yud`awna 'Ilá As-Sujūdi Falā Yastaţī`ūna 068-042 Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
Khāshi`atan 'Abşāruhum Tarhaquhum Dhillatun  ۖ  Wa Qad Kānū Yud`awna 'Ilá As-Sujūdi Wa Hum Sālimūna 068-043 Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).  ۖ 
Fadharnī Wa Man Yukadhdhibu Bihadhā Al-Ĥadīthi  ۖ  Sanastadrijuhum Min Ĥaythu Lā Ya`lamūna 068-044 Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.  ۖ 
Wa 'Umlī Lahum  ۚ  'Inna Kaydī Matīnun 068-045 Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.  ۚ 
'Am Tas'aluhum 'Ajrāan Fahum Min Maghramin Muthqalūna 068-046 Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
'Am `Indahumu Al-Ghaybu Fahum Yaktubūna 068-047 Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
Fāşbir Liĥukmi Rabbika Wa Lā Takun Kaşāĥibi Al-Ĥūti 'Idh Nādá Wa Huwa Makžūmun 068-048 Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
Lawlā 'An Tadārakahu Ni`matun Min Rabbihi Lanubidha Bil-`Arā'i Wa Huwa Madhmūmun 068-049 Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
jtabāhu Rabbuhu Faja`alahu Mina Aş-Şāliĥīna 068-050 Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
Wa 'In Yakādu Al-Ladhīna Kafarū Layuzliqūnaka Bi'abşārihim Lammā Sami`ū Adh-Dhikra Wa Yaqūlūna 'Innahu Lamajnūnun 068-051 Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
Wa Mā Huwa 'Illā Dhikrun Lil`ālamīna 068-052 Shi ( Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
Next Sūrah