67) Sūrat Al-Mulk

Printed format

67) سُورَة المُلك

Tabāraka Al-Ladhī Biyadihi Al-Mulku Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ067-001 (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome. تَبَارَكَ الَّذِي بِيَدِهِ الْمُلْكُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Al-Ladhī Khalaqa Al-Mawta Wa Al-Ĥayāata Liyabluwakum 'Ayyukum 'Aĥsanu `Amalāan  ۚ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ghafūru َ067-002 Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara. الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلا ً  ۚ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ
Al-Ladhī Khalaqa Sab`a Samāwātin Ţibāqāan  ۖ  Mā Tará Fī Khalqi Ar-Raĥmāni Min Tafāwutin  ۖ  Fārji`i Al-Başara Hal Tará Min Fuţūrin َ067-003 Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka? الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَات ٍ طِبَاقا ً  ۖ  مَا تَرَى فِي خَلْقِ الرَّحْمَنِ مِنْ تَفَاوُت ٍ  ۖ  فَارْجِعِ الْبَصَرَ هَلْ تَرَى مِنْ فُطُور ٍ
Thumma Arji`i Al-Başara Karratayni Yanqalib 'Ilayka Al-Başaru Khāsi'āan Wa Huwa Ĥasīrun َ067-004 Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã. ثُمَّ ارْجِعِ الْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنقَلِبْ إِلَيْكَ الْبَصَرُ خَاسِئا ً وَهُوَ حَسِير ٌ
Wa Laqad Zayyannā As-Samā'a Ad-Dunyā Bimaşābīĥa Wa Ja`alnāhā Rujūmāan Lilshshayāţīni  ۖ  Wa 'A`tadnā Lahum `Adhāba As-Sa`īri َ067-005 Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr. وَلَقَدْ زَيَّنَّا السَّمَاءَ الدُّنْيَا بِمَصَابِيحَ وَجَعَلْنَاهَا رُجُوما ً لِلشَّيَاطِينِ  ۖ  وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ السَّعِيرِ
Wa Lilladhīna Kafarū Birabbihim `Adhābu Jahannama  ۖ  Wa Bi'sa Al-Maşīru َ067-006 Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu. وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ  ۖ  وَبِئْسَ الْمَصِيرُ
'Idhā 'Ulqū Fīhā Sami`ū Lahā Shahīqāan Wa Hiya Tafūru َ067-007 Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa. إِذَا أُلْقُوا فِيهَا سَمِعُوا لَهَا شَهِيقا ً وَهِيَ تَفُورُ
Takādu Tamayyazu Mina Al-Ghayži  ۖ  Kullamā 'Ulqiya Fīhā Fawjun Sa'alahum Khazanatuhā 'Alam Ya'tikum Nadhīrun َ067-008 Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?" تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ الْغَيْظِ  ۖ  كُلَّمَا أُلْقِيَ فِيهَا فَوْج ٌ سَأَلَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِير ٌ
Qālū Balá Qad Jā'anā Nadhīrun Fakadhdhabnā Wa Qulnā Mā Nazzala Al-Lahu Min Shay'in 'In 'Antum 'Illā Fī Đalālin Kabīrin َ067-009 Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'" قَالُوا بَلَى قَدْ جَاءَنَا نَذِير ٌ فَكَذَّبْنَا وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ اللَّهُ مِنْ شَيْء ٍ إِنْ أَنْتُمْ إِلاَّ فِي ضَلاَل ٍ كَبِير ٍ
Wa Qālū Law Kunnā Nasma`u 'Aw Na`qilu Mā Kunnā Fī 'Aşĥābi As-Sa`īri َ067-010 Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba." وَقَالُوا لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِي أَصْحَابِ السَّعِيرِ
Fā`tarafū Bidhanbihim Fasuĥqāan Li'şĥābi As-Sa`īri َ067-011 Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr! فَاعْتَرَفُوا بِذَنْبِهِمْ فَسُحْقا ً لِأصْحَابِ السَّعِيرِ
'Inna Al-Ladhīna Yakhshawna Rabbahum Bil-Ghaybi Lahum Maghfiratun Wa 'Ajrun Kabīrun َ067-012 Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma. إِنَّ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ بِالْغَيْبِ لَهُمْ مَغْفِرَة ٌ وَأَجْر ٌ كَبِير ٌ
Wa 'Asirrū Qawlakum 'Aw Ajharū Bihi  ۖ  'Innahu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri َ067-013 Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. وَأَسِرُّوا قَوْلَكُمْ أَوْ اجْهَرُوا بِهِ~ِ  ۖ  إِنَّه ُُ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
'Alā Ya`lamu Man Khalaqa Wa Huwa Al-Laţīfu Al-Khabīru َ067-014 Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa? أَلاَ يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ اللَّطِيفُ الْخَبِيرُ
Huwa Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Dhalūlāanmshū Fī Manākibihā Wa Kulū Min Rizqihi  ۖ  Wa 'Ilayhi An-Nushūru َ067-015 Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake. هُوَ الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ ذَلُولا ً فَامْشُوا فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُوا مِنْ رِزْقِه ِِ  ۖ  وَإِلَيْهِ النُّشُورُ
'A'amintum Man As-Samā'i 'An Yakhsifa Bikumu Al-'Arđa Fa'idhā Hiya Tamūru َ067-016 Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? أَأَمِنتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يَخْسِفَ بِكُمُ الأَرْضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ
'Am 'Amintum Man As-Samā'i 'An Yursila `Alaykum Ĥāşibāan  ۖ  Fasata`lamūna Kayfa Nadhīri َ067-017 Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda ( ãƙibar) gargaɗiNa take. أَمْ أَمِنتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبا ً  ۖ  فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ
Wa Laqad Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim Fakayfa Kāna Nakīri َ067-018 Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗiNa ta kasance? وَلَقَدْ كَذَّبَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
'Awalam Yaraw 'Ilá Aţ-Ţayri Fawqahum Şāffātin Wa Yaqbiđna  ۚ  Mā Yumsikuhunna 'Illā Ar-Raĥmānu  ۚ  'Innahu Bikulli Shay'in Başīrun َ067-019 Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme. أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَافَّات ٍ وَيَقْبِضْنَ  ۚ  مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلاَّ الرَّحْمَنُ  ۚ  إِنَّه ُُ بِكُلِّ شَيْء ٍ بَصِير ٌ
'Amman Hādhā Al-Ladhī Huwa Jundun Lakum Yanşurukum Min Dūni Ar-Raĥmāni  ۚ  'Ini Al-Kāfirūna 'Illā Fī Ghurūrin َ067-020 Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu. أَمَّنْ هَذَا الَّذِي هُوَ جُند ٌ لَكُمْ يَنصُرُكُمْ مِنْ دُونِ الرَّحْمَنِ  ۚ  إِنِ الْكَافِرُونَ إِلاَّ فِي غُرُور ٍ
'Amman Hādhā Al-Ladhī Yarzuqukum 'In 'Amsaka Rizqahu  ۚ  Bal Lajjū Fī `Utūwin Wa Nufūrin َ067-021 Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikinSa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali. أَمَّنْ هَذَا الَّذِي يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَه ُُ  ۚ  بَلْ لَجُّوا فِي عُتُوّ ٍ وَنُفُور ٍ
'Afaman Yamshī Mukibbāan `Alá Wajhihi 'Ahdá 'Amman Yamshī Sawīyāan `Alá Şirāţin Mustaqīmin َ067-022 Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya? أَفَمَنْ يَمْشِي مُكِبّاً عَلَى وَجْهِهِ~ِ أَهْدَى أَمَّنْ يَمْشِي سَوِيّاً عَلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم ٍ
Qul Huwa Al-Ladhī 'Ansha'akum Wa Ja`ala Lakumu As-Sam`a Wa Al-'Abşāra Wa Al-'Af'idata  ۖ  Qalīlāan Mā Tashkurūna َ067-023 Ka ce: "( Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!" قُلْ هُوَ الَّذِي أَنشَأَكُمْ وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالأَبْصَارَ وَالأَفْئِدَةَ  ۖ  قَلِيلا ً مَا تَشْكُرُونَ
Qul Huwa Al-Ladhī Dhara'akum Al-'Arđi Wa 'Ilayhi Tuĥsharūna َ067-024 Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku." قُلْ هُوَ الَّذِي ذَرَأَكُمْ فِي الأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ
Wa Yaqūlūna Matá Hādhā Al-Wa`du 'In Kuntum Şādiqīna َ067-025 Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?" وَيَقُولُونَ مَتَى هَذَا الْوَعْدُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ
Qul 'Innamā Al-`Ilmu `Inda Al-Lahi Wa 'Innamā 'Anā Nadhīrun Mubīnun َ067-026 Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)." قُلْ إِنَّمَا الْعِلْمُ عِنْدَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِير ٌ مُبِين ٌ
Falammā Ra'awhu Zulfatan Sī'at Wujūhu Al-Ladhīna Kafarū Wa Qīla Hādhā Al-Ladhī Kuntum Bihi Tadda`ūna َ067-027 To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa. فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَة ً سِيئَتْ وُجُوهُ الَّذِينَ كَفَرُوا وَقِيلَ هَذَا الَّذِي كُنتُمْ بِه ِِ تَدَّعُونَ
Qul 'Ara'aytum 'In 'Ahlakaniya Al-Lahu Wa Man Ma`ī 'Aw Raĥimanā Faman Yujīru Al-Kāfirīna Min `Adhābin 'Alīmin َ067-028 Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?" قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِيَ اللَّهُ وَمَنْ مَعِي أَوْ رَحِمَنَا فَمَنْ يُجِيرُ الْكَافِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيم ٍ
Qul Huwa Ar-Raĥmānu 'Āmannā Bihi Wa `Alayhi Tawakkalnā  ۖ  Fasata`lamūna Man Huwa Fī Đalālin Mubīnin َ067-029 Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya." قُلْ هُوَ الرَّحْمَنُ آمَنَّا بِه ِِ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا  ۖ  فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
Qul 'Ara'aytum 'In 'Aşbaĥa Mā'uukum Ghawrāan Faman Ya'tīkum Bimā'in Ma`īnin َ067-030 Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?" قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَاؤُكُمْ غَوْرا ً فَمَنْ يَأْتِيكُمْ بِمَاء ٍ مَعِين ٍ
Next Sūrah