Yusabbiĥu Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Lahu Al-Mulku Wa Lahu Al-Ĥamdu Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun | َ064-001 Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne. | يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ |
Huwa Al-Ladhī Khalaqakum Faminkum Kāfirun Wa Minkum Mu'uminun Wa ۚ Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun | َ064-002 Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. | هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ فَمِنْكُمْ كَافِر ٌ وَمِنْكُمْ مُؤْمِن ٌ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير ٌ |
Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi Wa Şawwarakum Fa'aĥsana Şuwarakum ۖ Wa 'Ilayhi Al-Maşīru | َ064-003 Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take. | خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ وَصَوَّرَكُمْ فَأَحْسَنَ صُوَرَكُمْ ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ |
Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Ya`lamu Mā Tusirrūna Wa Mā Tu`linūna Wa ۚ Allāhu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri | َ064-004 Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. | يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ ۚ وَاللَّهُ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ |
'Alam Ya'tikum Naba'u Al-Ladhīna Kafarū Min Qablu Fadhāqū Wabāla 'Amrihim Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun | َ064-005 Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi? | أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَبَأُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ قَبْلُ فَذَاقُوا وَبَالَ أَمْرِهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ |
Dhālika Bi'annahu Kānat Ta'tīhim Rusuluhum Bil-Bayyināti Faqālū 'Abasharun Yahdūnanā Fakafarū Wa Tawallaw ۚ Wa Astaghná Al-Lahu Wa ۚ Allāhu Ghanīyun Ĥamīdun | َ064-006 Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde. | ذَلِكَ بِأَنَّه ُُ كَانَتْ تَأْتِيهِمْ رُسُلُهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ فَقَالُوا أَبَشَر ٌ يَهْدُونَنَا فَكَفَرُوا وَتَوَلَّوْا ۚ وَاسْتَغْنَى اللَّهُ ۚ وَاللَّهُ غَنِيٌّ حَمِيد ٌ |
Za`ama Al-Ladhīna Kafarū 'An Lan Yub`athū ۚ Qul Balá Wa Rabbī Latub`athunna Thumma Latunabba'uunna Bimā `Amiltum ۚ Wa Dhalika `Alá Al-Lahi Yasīrun | َ064-007 Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne." | زَعَمَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَنْ لَنْ يُبْعَثُوا ۚ قُلْ بَلَى وَرَبِّي لَتُبْعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلْتُمْ ۚ وَذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِير ٌ |
Fa'āminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa An-Nūri Al-Ladhī 'Anzalnā Wa ۚ Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun | َ064-008 Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne. | فَآمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ وَالنُّورِ الَّذِي أَنزَلْنَا ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِير ٌ |
Yawma Yajma`ukum Liyawmi Al-Jam`i ۖ Dhālika Yawmu At-Taghābuni ۗ Wa Man Yu'umin Bil-Lahi Wa Ya`mal Şāliĥāan Yukaffir `Anhu Sayyi'ātihi Wa Yudkhilhu Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā 'Abadāan ۚ Dhālika Al-Fawzu Al-`Ažīmu | َ064-009 A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma. | يَوْمَ يَجْمَعُكُمْ لِيَوْمِ الْجَمْعِ ۖ ذَلِكَ يَوْمُ التَّغَابُنِ ۗ وَمَنْ يُؤْمِنْ بِاللَّهِ وَيَعْمَلْ صَالِحا ً يُكَفِّرْ عَنْهُ سَيِّئَاتِه ِِ وَيُدْخِلْهُ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدا ً ۚ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ |
Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri Khālidīna ۖ Fīhā Wa Bi'sa Al-Maşīru | َ064-010 Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita. | وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ النَّارِ خَالِدِينَ فِيهَا ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ |
Mā 'Aşāba Min Muşībatin 'Illā Bi'idhni Al-Lahi ۗ Wa Man Yu'umin Bil-Lahi Yahdi Qalbahu Wa ۚ Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun | َ064-011 Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah,Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne. | مَا أَصَابَ مِنْ مُصِيبَة ٍ إِلاَّ بِإِذْنِ اللَّهِ ۗ وَمَنْ يُؤْمِنْ بِاللَّهِ يَهْدِ قَلْبَه ُُ ۚ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيم ٌ |
Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa 'Aţī`ū Ar-Rasūla ۚ Fa'in Tawallaytum Fa'innamā `Alá Rasūlinā Al-Balāghu Al-Mubīnu | َ064-012 Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu. | وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ ۚ فَإِنْ تَوَلَّيْتُمْ فَإِنَّمَا عَلَى رَسُولِنَا الْبَلاَغُ الْمُبِينُ |
Al-Lahu Lā 'Ilāha 'Illā Huwa ۚ Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna | َ064-013 Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara. | اللَّهُ لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Inna Min 'Azwājikum Wa 'Awlādikum `Adūwāan Lakum Fāĥdharūhum ۚ Wa 'In Ta`fū Wa Taşfaĥū Wa Taghfirū Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun | َ064-014 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ مِنْ أَزْوَاجِكُمْ وَأَوْلاَدِكُمْ عَدُوّا ً لَكُمْ فَاحْذَرُوهُمْ وَإِنْ ۚ تَعْفُوا وَتَصْفَحُوا وَتَغْفِرُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ |
'Innamā 'Amwālukum Wa 'Awlādukum Fitnatun Wa ۚ Allāhu `Indahu 'Ajrun `Ažīmun | َ064-015 Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma. | إِنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلاَدُكُمْ فِتْنَة ٌ ۚ وَاللَّهُ عِنْدَهُ~ُ أَجْرٌ عَظِيم ٌ |
Fāttaqū Al-Laha Mā Astaţa`tum Wa Asma`ū Wa 'Aţī`ū Wa 'Anfiqū Khayrāan Li'nfusikum ۗ Wa Man Yūqa Shuĥĥa Nafsihi Fa'ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna | َ064-016 Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. | فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ وَاسْمَعُوا وَأَطِيعُوا وَأَنفِقُوا خَيْرا ً لِأنْفُسِكُمْ ۗ وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِه ِِ فَأُوْلَائِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ |
'In Tuqriđū Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan Yuđā`ifhu Lakum Wa Yaghfir Lakum Wa ۚ Allāhu Shakūrun Ĥalīmun | َ064-017 Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri. | إِنْ تُقْرِضُوا اللَّهَ قَرْضاً حَسَنا ً يُضَاعِفْهُ لَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۚ وَاللَّهُ شَكُورٌ حَلِيم ٌ |
`Ālimu Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu | َ064-018 Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima. | عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ |