65) Sūrat Aţ-Ţalāq

Printed format

65)

Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu 'Idhā Ţallaqtumu An-Nisā' Faţalliqūhunna Li`iddatihinna Wa 'Aĥşū Al-`Iddata Wa Attaqū Al-Laha Rabbakum Lā Tukhrijūhunna Min Buyūtihinna Wa Lā Yakhrujna 'Illā 'An Ya'tīna Bifāĥishatin Mubayyinatin Wa Tilka Ĥudūdu Al-Lahi Wa Man Yata`adda Ĥudūda Al-Lahi Faqad Žalama Nafsahu Lā Tadrī La`alla Al-Laha Yuĥdithu Ba`da Dhālika 'Aman 065-001 Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka.
Fa'idhā Balaghna 'Ajalahunna Fa'amsikūhunna Bima`rūfin 'Aw Fāriqūhunna Bima`rūfin Wa 'Ash/hidū Dhaway `Adlin Minkum Wa 'Aqīmū Ash-Shahādata Lillahi  ۚ  Dhālikum Yū`ažu Bihi Man Kāna Yu'uminu Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri  ۚ  Wa Man Yattaqi Al-Laha Yaj`al Lahu Makhrajāan 065-002 Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita.  ۚ   ۚ 
Wa Yarzuqhu Min Ĥaythu Lā Yaĥtasibu  ۚ  Wa Man Yatawakkal `Alá Al-Lahi Fahuwa Ĥasbuhu  ۚ  'Inna Al-Laha Bālighu 'Amrihi  ۚ  Qad Ja`ala Al-Lahu Likulli Shay'in Qadan 065-003 Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme.  ۚ  ~  ۚ   ۚ 
Wa Al-Lā'ī Ya'isna Mina Al-Maĥīđi Min Nisā'ikum 'Ini Artabtum Fa`iddatuhunna Thalāthatu 'Ash/hurin Wa Al-Lā'ī Lam  ۚ  Yaĥiđna Wa 'Ūlātu Al-'Aĥmāli 'Ajaluhunna 'An Yađa`na  ۚ  Ĥamlahunna Wa Man Yattaqi Al-Laha Yaj`al Lahu Min 'Amrihi Yusrāan 065-004 Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, ( Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa.  ۚ   ۚ 
Dhālika 'Amru Al-Lahi 'Anzalahu 'Ilaykum  ۚ  Wa Man Yattaqi Al-Laha Yukaffir `Anhu Sayyi'ātihi Wa Yu`žim Lahu 'Ajan 065-005 Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako. ~  ۚ  ~
'Askinūhunna Min Ĥaythu Sakantum Min Wujdikum Wa Lā Tuđārrūhunna Lituđayyiqū `Alayhinna  ۚ  Wa 'In Kunna 'Ūlāti Ĥamlin Fa'anfiqū `Alayhinna Ĥattá Yađa`na Ĥamlahunna  ۚ  Fa'in 'Arđa`na Lakum Fa'ātūhunna 'Ujūrahunna  ۖ  Wa 'Tamirū Baynakum Bima`rūfin  ۖ  Wa 'In Ta`āsartum Fasaturđi`u Lahu 'Ukh 065-006 Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi ( mijin).  ۚ   ۚ   ۖ   ۖ  ~
Liyunfiq Dhū Sa`atin Min Sa`atihi  ۖ  Wa Man Qudira `Alayhi Rizquhu Falyunfiq Mimmā 'Ātāhu Al-Lahu  ۚ  Lā Yukallifu Al-Lahu Nafsāan 'Illā Mā 'Ātāhā  ۚ  Sayaj`alu Al-Lahu Ba`da `Usrin Yusrāan 065-007 Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani.  ۖ   ۚ   ۚ 
Wa Ka'ayyin Min Qaryatin `Atat `An 'Amri Rabbihā Wa Rusulihi Faĥāsabnāhā Ĥisābāan Shadīdāan Wa `Adhdhabnāhā `Adhābāan Nukrāan 065-008 Kuma da yawa daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.
Fadhāqat Wabāla 'Amrihā Wa Kāna `Āqibatu 'Amrihā Khusrāan 065-009 Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra,
'A`adda Al-Lahu Lahum `Adhābāan Shadīdāan Fa  ۖ  Attaqū Al-Laha Yā 'Ū Al-'Albābi Al-Ladhīna 'Āmanū  ۚ  Qad 'Anzala Al-Lahu 'Ilaykum Dhikrāan 065-010 Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku.  ۖ   ۚ 
Rasūlāan Yatlū `Alaykum 'Āyāti Al-Lahi Mubayyinātin Liyukhrija Al-Ladhīna 'Āmanū Wa `Amilū Aş-Şāliĥāti Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūri  ۚ  Wa Man Yu'umin Bil-Lahi Wa Ya`mal Şāliĥāan Yudkhilhu Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā 'Abadāan  ۖ  Qad 'Aĥsana Al-Lahu Lahu Rizqāan 065-011 Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata masa arziki.  ۚ   ۖ 
Al-Lahu Al-Ladhī Khalaqa Sab`a Samāwātin Wa Mina Al-'Arđi Mithlahunna Yatanazzalu Al-'Amru Baynahunna Lita`lamū 'Anna Al-Laha `Alá Kulli Shay'in Qadīrun Wa 'Anna Al-Laha Qad 'Aĥāţa Bikulli Shay'in `Ilmāan 065-012 Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani.
Next Sūrah