63) Sūrat Al-Munāfiqūn

Printed format

63)

'Idhā Jā'aka Al-Munāfiqūna Qālū Nash/hadu 'Innaka Larasūlu Al-Lahi Wa Allāhu Ya`lamu 'Innaka Larasūluhu Wa Allāhu Yash/hadu 'Inna Al-Munāfiqīna Lakādhibūna 063-001 Idan munãfukai suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa , maƙaryata ne.
Attakhadhū 'Aymānahum Junnatan Faşaddū `An Sabīli Al-Lahi  ۚ  'Innahum Sā'a Mā Kānū Ya`malūna 063-002 Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.  ۚ 
Dhālika Bi'annahum 'Āmanū Thumma Kafarū Faţubi`a `Alá Qulūbihim Fahum Lā Yafqahūna 063-003 Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta.
Wa 'Idhā Ra'aytahum Tu`jibuka 'Ajsāmuhum  ۖ  Wa 'In Yaqūlū Tasma` Liqawlihim  ۖ  Ka'annahum Khushubun Musannadatun  ۖ  Yaĥsabūna Kulla Şayĥatin `Alayhim  ۚ  Humu Al-`Adūwu Fāĥdharhum  ۚ  Qātalahumu Al-Lahu  ۖ  'Anná Yu'ufakūna 063-004 Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa, zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su?  ۖ   ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۖ 
Wa 'Idhā Qīla Lahum Ta`ālaw Yastaghfir Lakum Rasūlu Al-Lahi Lawwaw Ru'ūsahum Wa Ra'aytahum Yaşuddūna Wa Hum Mustakbirūna 063-005 Kuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.
Sawā'un `Alayhim 'Āstaghfarta Lahum 'Am Lam Tastaghfir Lahum Lan Yaghfira Al-Lahu Lahum  ۚ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Al-Qawma Al-Fāsiqīna 063-006 Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.  ۚ 
Humu Al-Ladhīna Yaqūlūna Lā Tunfiqū `Alá Man `Inda Rasūli Al-Lahi Ĥattá Yanfađđū  ۗ  Wa Lillahi Khazā'inu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Lakinna Al-Munāfiqīna Lā Yafqahūna 063-007 Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta.  ۗ 
Yaqūlūna La'in Raja`nā 'Ilá Al-Madīnati Layukhrijanna Al-'A`azzu Minhā Al-'Adhalla  ۚ  Wa Lillahi Al-`Izzatu Wa Lirasūlihi Wa Lilmu'uminīna Wa Lakinna Al-Munāfiqīna Lā Ya`lamūna 063-008 Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tulhikum 'Amwālukum Wa Lā 'Awlādukum `An Dhikri Al-Lahi  ۚ  Wa Man Yaf`al Dhālika Fa'ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna 063-009 Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.  ۚ 
Wa 'Anfiqū Min Mā Razaqnākum Min Qabli 'An Ya'tiya 'Aĥadakumu Al-Mawtu Fayaqūla Rabbi Lawlā 'Akhkhartanī 'Ilá 'Ajalin Qarībin Fa'aşşaddaqa Wa 'Akun Mina Aş-Şāliĥīna 063-010 Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?"
Wa Lan Yu'uakhkhira Al-Lahu Nafsāan 'Idhā Jā'a 'Ajaluhā Wa  ۚ  Allāhu Khabīrun Bimā Ta`malūna 063-011 Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa.  ۚ 
Next Sūrah