Yusabbiĥu Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Al-Maliki Al-Quddūsi Al-`Azīzi Al-Ĥakīmi | َ062-001 Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki,Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima. | يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ الْمَلِكِ الْقُدُّوسِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ |
Huwa Al-Ladhī Ba`atha Fī Al-'Ummīyīna Rasūlāan Minhum Yatlū `Alayhim 'Āyātihi Wa Yuzakkīhim Wa Yu`allimuhumu Al-Kitāba Wa Al-Ĥikmata Wa 'In Kānū Min Qablu Lafī Đalālin Mubīnin | َ062-002 Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna. | هُوَ الَّذِي بَعَثَ فِي الأُمِّيِّينَ رَسُولا ً مِنْهُمْ يَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِه ِِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَإِنْ كَانُوا مِنْ قَبْلُ لَفِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ |
Wa 'Ākharīna Minhum Lammā Yalĥaqū Bihim ۚ Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu | َ062-003 Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. | وَآخَرِينَ مِنْهُمْ لَمَّا يَلْحَقُوا بِهِمْ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ |
Dhālika Fađlu Al-Lahi Yu'utīhi Man Yashā'u Wa ۚ Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi | َ062-004 Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma. | ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيه ِِ مَنْ يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ |
Mathalu Al-Ladhīna Ĥummilū At-Tawrāata Thumma Lam Yaĥmilūhā Kamathali Al-Ĥimāri Yaĥmilu 'Asfārāan ۚ Bi'sa Mathalu Al-Qawmi Al-Ladhīna Kadhdhabū Bi'āyāti Al-Lahi Wa ۚ Allāhu Lā Yahdī Al-Qawma Až-Žālimīna | َ062-005 Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai. | مَثَلُ الَّذِينَ حُمِّلُوا التَّوْرَاةَ ثُمَّ لَمْ يَحْمِلُوهَا كَمَثَلِ الْحِمَارِ يَحْمِلُ أَسْفَارا ً ۚ بِئْسَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللَّهِ ۚ وَاللَّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ |
Qul Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna Hādū 'In Za`amtum 'Annakum 'Awliyā 'U Lillahi Min Dūni An-Nāsi Fatamannaw Al-Mawta 'In Kuntum Şādiqīna | َ062-006 Ka ce: "Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa idan kun kasance mãsu gaskiya." | قُلْ يَاأَيُّهَا الَّذِينَ هَادُوا إِنْ زَعَمْتُمْ أَنَّكُمْ أَوْلِيَاءُ لِلَّهِ مِنْ دُونِ النَّاسِ فَتَمَنَّوْا الْمَوْتَ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ |
Wa Lā Yatamannawnahu 'Abadāan Bimā Qaddamat 'Aydīhim Wa ۚ Allāhu `Alīmun Biž-Žālimīna | َ062-007 Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai | وَلاَ يَتَمَنَّوْنَهُ~ُ أَبَدا ً بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ۚ وَاللَّهُ عَلِيم ٌ بِالظَّالِمِينَ |
Qul 'Inna Al-Mawta Al-Ladhī Tafirrūna Minhu Fa'innahu Mulāqīkum ۖ Thumma Turaddūna 'Ilá `Ālimi Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna | َ062-008 Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta,to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa." | قُلْ إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّه ُُ مُلاَقِيكُمْ ۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَى عَالِمِ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Nūdī Lilşşalāati Min Yawmi Al-Jumu`ati Fās`aw 'Ilá Dhikri Al-Lahi Wa Dharū Al-Bay`a ۚ Dhālikum Khayrun Lakum 'In Kuntum Ta`lamūna | َ062-009 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِي لِلصَّلاَةِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَى ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ذَلِكُمْ ۚ خَيْر ٌ لَكُمْ إِنْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ |
Fa'idhā Quđiyati Aş-Şalāatu Fāntashirū Fī Al-'Arđi Wa Abtaghū Min Fađli Al-Lahi Wa Adhkurū Al-Laha Kathīrāan La`allakum Tufliĥūna | َ062-010 Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo. | فَإِذَا قُضِيَتِ الصَّلاَةُ فَانتَشِرُوا فِي الأَرْضِ وَابْتَغُوا مِنْ فَضْلِ اللَّهِ وَاذْكُرُوا اللَّهَ كَثِيرا ً لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ |
Wa 'Idhā Ra'aw Tijāratan 'Aw Lahwan Anfađđū 'Ilayhā Wa Tarakūka Qā'imāan ۚ Qul Mā `Inda Al-Lahi Khayrun Mina Al-Lahwi Wa Mina At-Tijārati Wa ۚ Allāhu Khayru Ar-Rāziqīna | َ062-011 Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa." | وَإِذَا رَأَوْا تِجَارَةً أَوْ لَهْوا ً انفَضُّوا إِلَيْهَا وَتَرَكُوكَ قَائِما ً ۚ قُلْ مَا عِنْدَ اللَّهِ خَيْر ٌ مِنَ اللَّهْوِ وَمِنَ التِّجَارَةِ ۚ وَاللَّهُ خَيْرُ الرَّازِقِينَ |