59) Sūrat Al-Ĥashr

Printed format

59) سُورَة الحَشر

Sabbaĥa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ059-001 Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Huwa Al-Ladhī 'Akhraja Al-Ladhīna Kafarū Min 'Ahli Al-Kitābi Min Diyārihim Li'wwali Al-Ĥashri  ۚ  Mā Žanantum 'An Yakhrujū  ۖ  Wa Žannū 'Annahum Māni`atuhum Ĥuşūnuhum Mina Al-Lahi Fa'atāhumu Al-Lahu Min Ĥaythu Lam Yaĥtasibū  ۖ  Wa Qadhafa Fī Qulūbihimu Ar-Ru`ba  ۚ  Yukhribūna Buyūtahum Bi'aydīhim Wa 'Aydī Al-Mu'uminīna Fā`tabirū Yā 'Ū Al-'Abşāri َ059-002 Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi, daga gidãjẽnsu da kõra ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri. هُوَ الَّذِي أَخْرَجَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مِنْ دِيَارِهِمْ لِأوَّلِ الْحَشْرِ  ۚ  مَا ظَنَنْتُمْ أَنْ يَخْرُجُوا  ۖ  وَظَنُّوا أَنَّهُمْ مَانِعَتُهُمْ حُصُونُهُمْ مِنَ اللَّهِ فَأَتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ حَيْثُ لَمْ يَحْتَسِبُوا  ۖ  وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ الرُّعْبَ  ۚ  يُخْرِبُونَ بُيُوتَهُمْ بِأَيْدِيهِمْ وَأَيْدِي الْمُؤْمِنِينَ فَاعْتَبِرُوا يَا أُولِي الأَبْصَارِ
Wa Lawlā 'An Kataba Al-Lahu `Alayhimu Al-Jalā'a La`adhdhabahum Ad-Dunyā  ۖ  Wa Lahum Al-'Ākhirati `Adhābu An-Nāri َ059-003 Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã. وَلَوْلاَ أَنْ كَتَبَ اللَّهُ عَلَيْهِمُ الْجَلاَءَ لَعَذَّبَهُمْ فِي الدُّنْيَا  ۖ  وَلَهُمْ فِي الآخِرَةِ عَذَابُ النَّارِ
Dhālika Bi'annahum Shāqqū Al-Laha Wa Rasūlahu  ۖ  Wa Man Yushāqqi Al-Laha Fa'inna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi َ059-004 Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne. ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ شَاقُّوا اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ  ۖ  وَمَنْ يُشَاقِّ اللَّهَ فَإِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Mā Qaţa`tum Min Līnatin 'Aw Taraktumūhā Qā'imatan `Alá 'Uşūlihā Fabi'idhni Al-Lahi Wa Liyukhziya Al-Fāsiqīna َ059-005 Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai, مَا قَطَعْتُمْ مِنْ لِينَةٍ أَوْ تَرَكْتُمُوهَا قَائِمَةً عَلَى أُصُولِهَا فَبِإِذْنِ اللَّهِ وَلِيُخْزِيَ الْفَاسِقِينَ
Wa Mā 'Afā'a Al-Lahu `Alá Rasūlihi Minhum Famā 'Awjaftum `Alayhi Min Khaylin Wa Lā Rikābin Wa Lakinna Al-Laha Yusalliţu Rusulahu `Alá Man Yashā'u Wa  ۚ  Allāhu `Alá Kulli Shay'in Qadīrun َ059-006 Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga ManzonSa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da ManzanninSa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme. وَمَا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَى رَسُولِه ِِ مِنْهُمْ فَمَا أَوْجَفْتُمْ عَلَيْهِ مِنْ خَيْل ٍ وَلاَ رِكَاب ٍ وَلَكِنَّ اللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَه ُُ عَلَى مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ
Mā 'Afā'a Al-Lahu `Alá Rasūlihi Min 'Ahli Al-Qurá Falillāhi Wa Lilrrasūli Wa Lidhī Al-Qurbá Wa Al-Yatāmá Wa Al-Masākīni Wa Abni As-Sabīli Kay Lā Yakūna Dūlatan Bayna Al-'Aghniyā'i Minkum  ۚ  Wa Mā 'Ātākumu Ar-Rasūlu Fakhudhūhu Wa Mā Nahākum `Anhu Fāntahū  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha  ۖ  'Inna Al-Laha Shadīdu Al-`Iqābi َ059-007 Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya ( matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne. مَا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَى رَسُولِه ِِ مِنْ أَهْلِ الْقُرَى فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ وَابْنِ السَّبِيلِ كَيْ لاَ يَكُونَ دُولَة ً بَيْنَ الأَغْنِيَاءِ مِنْكُمْ  ۚ  وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوه ُُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا  ۚ  وَاتَّقُوا اللَّهَ  ۖ  إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ
Lilfuqarā'i Al-Muhājirīna Al-Ladhīna 'Ukhrijū Min Dīārihim Wa 'Amwālihim Yabtaghūna Fađlāan Mina Al-Lahi Wa Riđwānāan Wa Yanşurūna Al-Laha Wa Rasūlahu  ۚ  'Ūlā'ika Humu Aş-Şādiqūna َ059-008 (Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya. لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيارِهِمْ وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلا ً مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانا ً وَيَنْصُرُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ~ُ  ۚ  أُوْلَائِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ
Wa Al-Ladhīna Tabawwa'ū Ad-Dāra Wa Al-'Īmāna Min Qablihim Yuĥibbūna Man Hājara 'Ilayhim Wa Lā Yajidūna Fī Şudūrihim Ĥājatan Mimmā 'Ūtū Wa Yu'uthirūna `Alá 'Anfusihim Wa Law Kāna Bihim  ۚ  Khaşāşatun Wa Man Yūqa Shuĥĥa Nafsihi Fa'ūlā'ika Humu Al-Mufliĥūna َ059-009 Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu, sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالإِيمَانَ مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلاَ يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ حَاجَة ً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَة ٌ  ۚ  وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِه ِِ فَأُوْلَائِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ
Wa Al-Ladhīna Jā'ū Min Ba`dihim Yaqūlūna Rabbanā Aghfir Lanā Wa Li'akhwāninā Al-Ladhīna Sabaqūnā Bil-'Īmāni Wa Lā Taj`al Fī Qulūbinā Ghillāan Lilladhīna 'Āmanū Rabbanā 'Innaka Ra'ūfun Raĥīmun َ059-010 Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai. وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِأَخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالإِيمَانِ وَلاَ تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلّا ً لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوف ٌ رَحِيم ٌ
'Alam Tará 'Ilá Al-Ladhīna Nāfaqū Yaqūlūna Li'khwānihimu Al-Ladhīna Kafarū Min 'Ahli Al-Kitābi La'in 'Ukhrijtum Lanakhrujanna Ma`akum Wa Lā Nuţī`u Fīkum 'Aĥadāan 'Abadāan Wa 'In Qūtiltum Lananşurannakum Wa Allāhu Yash/hadu 'Innahum Lakādhibūna َ059-011 Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne. أَلَمْ تَرى إِلَى الَّذِينَ نَافَقُوا يَقُولُونَ لِأخْوَانِهِمُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَئِنْ أُخْرِجْتُمْ لَنَخْرُجَنَّ مَعَكُمْ وَلاَ نُطِيعُ فِيكُمْ أَحَداً أَبَدا ً وَإِنْ قُوتِلْتُمْ لَنَنْصُرَنَّكُمْ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ
La'in 'Ukhrijū Lā Yakhrujūna Ma`ahum Wa La'in Qūtilū Lā Yanşurūnahum Wa La'in Naşarūhum Layuwallunna Al-'Adbāra Thumma Lā Yunşarūna َ059-012 Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba. لَئِنْ أُخْرِجُوا لاَ يَخْرُجُونَ مَعَهُمْ وَلَئِنْ قُوتِلُوا لاَ يَنْصُرُونَهُمْ وَلَئِنْ نَصَرُوهُمْ لَيُوَلُّنَّ الأَدْبَارَ ثُمَّ لاَ يُنْصَرُونَ
La'antum 'Ashaddu Rahbatan Fī Şudūrihim Mina Al-Lahi  ۚ  Dhālika Bi'annahum Qawmun Lā Yafqahūna َ059-013 Lalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa. لَأَنْتُمْ أَشَدُّ رَهْبَة ً فِي صُدُورِهِمْ مِنَ اللَّهِ  ۚ  ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْم ٌ لاَ يَفْقَهُونَ
Lā Yuqātilūnakum Jamī`āan 'Illā Fī Quráan Muĥaşşanatin 'Aw Min Warā'i Judurin  ۚ  Ba'suhum Baynahum Shadīdun  ۚ  Taĥsabuhum Jamī`āan Wa Qulūbuhum Shattá  ۚ  Dhālika Bi'annahum Qawmun Lā Ya`qilūna َ059-014 Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta. لاَ يُقَاتِلُونَكُمْ جَمِيعا ً إِلاَّ فِي قُرى ً مُحَصَّنَةٍ أَوْ مِنْ وَرَاءِ جُدُر ٍ  ۚ  بَأْسُهُمْ بَيْنَهُمْ شَدِيد ٌ  ۚ  تَحْسَبُهُمْ جَمِيعا ً وَقُلُوبُهُمْ شَتَّى  ۚ  ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْم ٌ لاَ يَعْقِلُونَ
Kamathali Al-Ladhīna Min Qablihim Qarībāan  ۖ  Dhāqū Wabāla 'Amrihim Wa Lahum `Adhābun 'Alīmun َ059-015 Kamar misãlin waɗanda ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai raRaɗi. كَمَثَلِ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ قَرِيبا ً  ۖ  ذَاقُوا وَبَالَ أَمْرِهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيم ٌ
Kamathali Ash-Shayţāni 'Idh Qāla Lil'insāni Akfur Falammā Kafara Qāla 'Innī Barī'un Minka 'Innī 'Akhāfu Al-Laha Rabba Al-`Ālamīna َ059-016 Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, "Ka kãfirta," To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta!" كَمَثَلِ الشَّيْطَانِ إِذْ قَالَ لِلإِنسَانِ اكْفُرْ فَلَمَّا كَفَرَ قَالَ إِنِّي بَرِيء ٌ مِنْكَ إِنِّي أَخَافُ اللَّهَ رَبَّ الْعَالَمِينَ
Fakāna `Āqibatahumā 'Annahumā Fī An-Nāri Khālidayni Fīhā  ۚ  Wa Dhalika Jazā'u Až-Žālimīna َ059-017 Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci." فَكَانَ عَاقِبَتَهُمَا أَنَّهُمَا فِي النَّارِ خَالِدَيْنِ فِيهَا  ۚ  وَذَلِكَ جَزَاءُ الظَّالِمِينَ
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa Ltanžur Nafsun Mā Qaddamat Lighadin  ۖ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Khabīrun Bimā Ta`malūna َ059-018 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa. يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَلْتَنْظُرْ نَفْس ٌ مَا قَدَّمَتْ لِغَد ٍ وَاتَّقُوا  ۖ  اللَّهَ إِنَّ  ۚ  اللَّهَ خَبِير ٌ بِمَا تَعْمَلُونَ
Wa Lā Takūnū Kālladhīna Nasū Al-Laha Fa'ansāhum 'Anfusahum  ۚ  'Ūlā'ika Humu Al-Fāsiqūna َ059-019 Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai. وَلاَ تَكُونُوا كَالَّذِينَ نَسُوا اللَّهَ فَأَنْسَاهُمْ أَنْفُسَهُمْ  ۚ  أُوْلَائِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ
Lā Yastawī 'Aşĥābu An-Nāri Wa 'Aşĥābu Al-Jannati  ۚ  'Aşĥābu Al-Jannati Humu Al-Fā'izūna َ059-020 'Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo. لاَ يَسْتَوِي أَصْحَابُ النَّارِ وَأَصْحَابُ الْجَنَّةِ  ۚ  أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمُ الْفَائِزُونَ
Law 'Anzalnā Hādhā Al-Qur'āna `Alá Jabalin Lara'aytahu Khāshi`āan Mutaşaddi`āan Min Khashyati Al-Lahi  ۚ  Wa Tilka Al-'Amthālu Nađribuhā Lilnnāsi La`allahum Yatafakkarūna َ059-021 Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni. لَوْ أَنْزَلْنَا هَذَا الْقُرْآنَ عَلَى جَبَل ٍ لَرَأَيْتَه ُُ خَاشِعا ً مُتَصَدِّعا ً مِنْ خَشْيَةِ اللَّهِ  ۚ  وَتِلْكَ الأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
Huwa Al-Lahu Al-Ladhī Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  `Ālimu Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati  ۖ  Huwa Ar-Raĥmānu Ar-Raĥīmu َ059-022 (Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai. هُوَ اللَّهُ الَّذِي لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۖ  عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ  ۖ  هُوَ الرَّحْمَنُ الرَّحِيمُ
Huwa Al-Lahu Al-Ladhī Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Al-Maliku Al-Quddūsu As-Salāmu Al-Mu'uminu Al-Muhayminu Al-`Azīzu Al-Jabbāru Al-Mutakabbiru  ۚ  Subĥāna Al-Lahi `Ammā Yushrikūna َ059-023 Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai t஛astãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi. هُوَ اللَّهُ الَّذِي لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ الْمَلِكُ الْقُدُّوسُ السَّلاَمُ الْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ الْعَزِيزُ الْجَبَّارُ الْمُتَكَبِّرُ  ۚ  سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Huwa Al-Lahu Al-Khāliqu Al-Bāri'u Al-Muşawwiru  ۖ  Lahu Al-'Asmā'u Al-Ĥusná  ۚ  Yusabbiĥu Lahu Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu َ059-024 Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa.Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi,Mai hikima. هُوَ اللَّهُ الْخَالِقُ الْبَارِئُ الْمُصَوِّرُ  ۖ  لَهُ الأَسْمَاءُ الْحُسْنَى  ۚ  يُسَبِّحُ لَه ُُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۖ  وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Next Sūrah