60) Sūrat Al-Mumtaĥanah

Printed format

60)

Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tattakhidhū `Adūwī Wa `Adūwakum 'Awliyā'a Tulqūna 'Ilayhim Bil-Mawaddati Wa Qad Kafarū Bimā Jā'akum Mina Al-Ĥaqqi Yukhrijūna Ar-Rasūla Wa 'Īyākum 'An Tu'uminū Bil-Lahi Rabbikum 'In Kuntum Kharajtum Jihādāan Fī Sabīlī Wa Abtighā'a Marđātī Tusirrūna 'Ilayhim Bil-Mawaddati Wa 'Anā 'A`lamu Bimā 'Akhfaytum Wa Mā 'A`lantum Wa Man Yaf`alhu Minkum Faqad Đalla Sawā'a As-Sabīli 060-001 Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.
'In Yathqafūkum Yakūnū Lakum 'A`dā'an Wa Yabsuţū 'Ilaykum 'Aydiyahum Wa 'Alsinatahum Bis-Sū'i Wa Waddū Law Takfurūna 060-002 Idan sun kãma ku, zã su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gũrin ku kãfirta.
Lan Tanfa`akum 'Arĥāmukum Wa Lā 'Awlādukum  ۚ  Yawma Al-Qiyāmati Yafşilu Baynakum Wa  ۚ  Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun 060-003 Zumuntarku bã zã ta amfãne ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Rãnar Kiyãma. (Allah) zai rarrabe tsakãninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.  ۚ   ۚ 
Qad Kānat Lakum 'Uswatun Ĥasanatun Fī 'Ibrāhīma Wa Al-Ladhīna Ma`ahu 'Idh Qālū Liqawmihim 'Innā Bura'ā'u Minkum Wa Mimmā Ta`budūna Min Dūni Al-Lahi Kafarnā Bikum Wa Badā Baynanā Wa Baynakumu Al-`Adāwatu Wa Al-Baghđā'u 'Abadāan Ĥattá Tu'uminū Bil-Lahi Waĥdahu 'Illā Qawla 'Ibrāhīma Li'abīhi La'astaghfiranna Laka Wa Mā 'Amliku Laka Mina Al-Lahi Min Shay'in  ۖ  Rabbanā `Alayka Tawakkalnā Wa 'Ilayka 'Anabnā Wa 'Ilayka Al-Maşīru 060-004 Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai." Fãce maganar Ibrãhĩm ga ubansa (da yace), "Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai." "Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take." ~ ~  ۖ 
Rabbanā Lā Taj`alnā Fitnatan Lilladhīna Kafarū Wa Aghfir Lanā Rabbanā  ۖ  'Innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu 060-005 "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima!  ۖ 
Laqad Kāna Lakum Fīhim 'Uswatun Ĥasanatun Liman Kāna Yarjū Al-Laha Wa Al-Yawma Al-'Ākhira  ۚ  Wa Man Yatawalla Fa'inna Al-Laha Huwa Al-Ghanīyu Al-Ĥamīdu 060-006 Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yanã fãtan (rahamar) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde.  ۚ 
`Asá Al-Lahu 'An Yaj`ala Baynakum Wa Bayna Al-Ladhīna `Ādaytum Minhum Mawaddatan Wa  ۚ  Allāhu Qadīrun Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 060-007 Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ   ۚ 
Lā Yanhākumu Al-Lahu `Ani Al-Ladhīna Lam Yuqātilūkum Ad-Dīni Wa Lam Yukhrijūkum Min Diyārikum 'An Tabarrūhum Wa Tuqsiţū 'Ilayhim  ۚ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muqsiţīna 060-008 Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci.  ۚ 
'Innamā Yanhākumu Al-Lahu `Ani Al-Ladhīna Qātalūkum Ad-Dīni Wa 'Akhrajūkum Min Diyārikum Wa Žāharū `Alá 'Ikhrājikum 'An Tawallawhum  ۚ  Wa Man Yatawallahum Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna 060-009 Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Jā'akumu Al-Mu'uminātu Muhājirātinmtaĥinūhunna  ۖ  Al-Lahu 'A`lamu Bi'īmānihinna  ۖ  Fa'in `Alimtumūhunna Mu'uminātin Falā Tarji`ūhunna 'Ilá Al-Kuffāri  ۖ  Lā Hunna Ĥillun Lahum Wa Lā Hum Yaĥillūna Lahunna  ۖ  Wa 'Ātūhum Mā 'Anfaqū  ۚ  Wa Lā Junāĥa `Alaykum 'An Tankiĥūhunna 'Idhā 'Ātaytumūhunna 'Ujūrahunna  ۚ  Wa Lā Tumsikū Bi`işami Al-Kawāfiri Wa As'alū Mā 'Anfaqtum Wa Līas'alū Mā 'Anfaqū  ۚ  Dhālikum Ĥukmu Al-Lahi  ۖ  Yaĥkumu Baynakum Wa  ۚ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 060-010 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima  ۖ   ۖ   ۖ   ۖ   ۚ   ۚ   ۚ   ۖ   ۚ 
Wa 'In Fātakum Shay'un Min 'Azwājikum 'Ilá Al-Kuffāri Fa`āqabtum Fa'ā Al-Ladhīna Dhahabat 'Azwājuhum Mithla Mā 'Anfaqū  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha Al-Ladhī 'Antum Bihi Mu'uminūna 060-011 Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa'an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nabīyu 'Idhā Jā'aka Al-Mu'uminātu Yubāyi`naka `Alá 'An Lā Yushrikna Bil-Lahi Shay'āan Wa Lā Yasriqna Wa Lā Yaznīna Wa Lā Yaqtulna 'Awlādahunna Wa Lā Ya'tīna Bibuhtānin Yaftarīnahu Bayna 'Aydīhinna Wa 'Arjulihinna Wa Lā Ya`şīnaka Fī Ma`rūfin  ۙ  Fabāyi`hunna Wa Astaghfir Lahunna Al-Laha  ۖ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 060-012 Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe, ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۙ   ۖ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tatawallaw Qawmāan Ghađiba Al-Lahu `Alayhim Qad Ya'isū Mina Al-'Ākhirati Kamā Ya'isa Al-Kuffāru Min 'Aşĥābi Al-Qubūri 060-013 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa kaburbura.
Next Sūrah