Qad Sami`a Al-Lahu Qawla Allatī Tujādiluka Fī Zawjihā Wa Tashtakī 'Ilá Al-Lahi Wa Allāhu Yasma`u Taĥāwurakumā 'Inna Al-Laha Samī`un Başīrun | َ058-001 Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani. | قَدْ سَمِعَ اللَّهُ قَوْلَ الَّتِي تُجَادِلُكَ فِي زَوْجِهَا وَتَشْتَكِي إِلَى اللَّهِ وَاللَّهُ يَسْمَعُ تَحَاوُرَكُمَا إِنَّ اللَّهَ سَمِيع ٌ بَصِير ٌ |
Al-Ladhīna Yužāhirūna Minkum Min Nisā'ihim Mā Hunna 'Ummahātihim ۖ 'In 'Ummahātuhum 'Illā Al-Lā'ī Waladnahum ۚ Wa 'Innahum Layaqūlūna Munkarāan Mina Al-Qawli Wa Zūrāan ۚ Wa 'Inna Al-Laha La`afūwun Ghafūrun | َ058-002 Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. | الَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِنْكُمْ مِنْ نِسَائِهِمْ مَا هُنَّ أُمَّهَاتِهِمْ ۖ إِنْ أُمَّهَاتُهُمْ إِلاَّ اللاَّئِي وَلَدْنَهُمْ ۚ وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنْكَرا ً مِنَ الْقَوْلِ وَزُورا ً ۚ وَإِنَّ اللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُور ٌ |
Wa Al-Ladhīna Yužāhirūna Min Nisā'ihim Thumma Ya`ūdūna Limā Qālū Fataĥrīru Raqabatin Min Qabli 'An ۚ Yatamāssā Dhālikum Tū`ažūna ۚ Bihi Wa Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun | َ058-003 Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna.Wannan anã yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa. | وَالَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِنْ نِسَائِهِمْ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُوا فَتَحْرِيرُ رَقَبَة ٍ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَتَمَاسَّا ۚ ذَلِكُمْ تُوعَظُونَ بِه ِِ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِير ٌ |
Faman Lam Yajid Faşiyāmu Shahrayni Mutatābi`ayni Min Qabli 'An Yatamāssā ۖ Faman Lam Yastaţi` Fa'iţ`āmu Sittīna Miskīnāan ۚ Dhālika Litu'uminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi ۚ Wa Tilka Ĥudūdu Al-Lahi ۗ Wa Lilkāfirīna `Adhābun 'Alīmun | َ058-004 To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi. | فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَتَمَاسَّا ۖ فَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَإِطْعَامُ سِتِّينَ مِسْكِينا ً ۚ ذَلِكَ لِتُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ ۚ وَتِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ ۗ وَلِلْكَافِرِينَ عَذَابٌ أَلِيم ٌ |
'Inna Al-Ladhīna Yuĥāddūna Al-Laha Wa Rasūlahu Kubitū Kamā Kubita Al-Ladhīna Min Qablihim ۚ Wa Qad 'Anzalnā 'Āyātin Bayyinātin ۚ Wa Lilkāfirīna `Adhābun Muhīnun | َ058-005 Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa. | إِنَّ الَّذِينَ يُحَادُّونَ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ كُبِتُوا كَمَا كُبِتَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ ۚ وَقَدْ أَنْزَلْنَا آيَات ٍ بَيِّنَات ٍ ۚ وَلِلْكَافِرِينَ عَذَاب ٌ مُهِين ٌ |
Yawma Yab`athuhumu Al-Lahu Jamī`āan Fayunabbi'uhum Bimā `Amilū ۚ 'Aĥşāhu Al-Lahu Wa Nasūhu Wa ۚ Allāhu `Alá Kulli Shay'in Shahīdun | َ058-006 Rãnar da Allah zai tãyar da su gabã ɗaya, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata, Allah Yã lissafa shi, alhãli kuwa sũ,sun manta da shi, kuma a kan kõme Allah Halartacce ne. | يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ اللَّهُ جَمِيعا ً فَيُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا ۚ أَحْصَاهُ اللَّهُ وَنَسُوه ُُ ۚ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ شَهِيد ٌ |
'Alam Tará 'Anna Al-Laha Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi ۖ Mā Yakūnu Min Najwá Thalāthatin 'Illā Huwa Rābi`uhum Wa Lā Khamsatin 'Illā Huwa Sādisuhum Wa Lā 'Adná Min Dhālika Wa Lā 'Akthara 'Illā Huwa Ma`ahum 'Ayna Mā Kānū ۖ Thumma Yunabbi'uhum Bimā `Amilū Yawma Al-Qiyāmati ۚ 'Inna Al-Laha Bikulli Shay'in `Alīmun | َ058-007 Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme. | أَلَمْ تَرَى أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ ۖ مَا يَكُونُ مِنْ نَجْوَى ثَلاَثَة ٍ إِلاَّ هُوَ رَابِعُهُمْ وَلاَ خَمْسَة ٍ إِلاَّ هُوَ سَادِسُهُمْ وَلاَ أَدْنَى مِنْ ذَلِكَ وَلاَ أَكْثَرَ إِلاَّ هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُمْ بِمَا عَمِلُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيم ٌ |
'Alam Tará 'Ilá Al-Ladhīna Nuhū `Ani An-Najwá Thumma Ya`ūdūna Limā Nuhū `Anhu Wa Yatanājawna Bil-'Ithmi Wa Al-`Udwāni Wa Ma`şiyati Ar-Rasūli Wa 'Idhā Jā'ūka Ĥayyawka Bimā Lam Yuĥayyika Bihi Al-Lahu Wa Yaqūlūna Fī 'Anfusihim Lawlā Yu`adhdhibunā Al-Lahu Bimā Naqūlu ۚ Ĥasbuhum Jahannamu Yaşlawnahā ۖ Fabi'sa Al-Maşīru | َ058-008 Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana. | أَلَمْ تَرَى إِلَى الَّذِينَ نُهُوا عَنِ النَّجْوَى ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُوا عَنْهُ وَيَتَنَاجَوْنَ بِالإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَةِ الرَّسُولِ وَإِذَا جَاءُوكَ حَيَّوْكَ بِمَا لَمْ يُحَيِّكَ بِهِ اللَّهُ وَيَقُولُونَ فِي أَنفُسِهِمْ لَوْلاَ يُعَذِّبُنَا اللَّهُ بِمَا نَقُولُ ۚ حَسْبُهُمْ جَهَنَّمُ يَصْلَوْنَهَا ۖ فَبِئْسَ الْمَصِيرُ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Tanājaytum Falā Tatanājaw Bil-'Ithmi Wa Al-`Udwāni Wa Ma`şiyati Ar-Rasūli Wa Tanājaw Bil-Birri Wa At-Taqwá ۖ Wa Attaqū Al-Laha Al-Ladhī 'Ilayhi Tuĥsharūna | َ058-009 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا تَنَاجَيْتُمْ فَلاَ تَتَنَاجَوْا بِالإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَةِ الرَّسُولِ وَتَنَاجَوْا بِالْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَاتَّقُوا ۖ اللَّهَ الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ |
'Innamā An-Najwá Mina Ash-Shayţāni Liyaĥzuna Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Laysa Biđārrihim Shay'āan 'Illā Bi'idhni Al-Lahi ۚ Wa `Alá Al-Lahi Falyatawakkali Al-Mu'uminūna | َ058-010 Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah. | إِنَّمَا النَّجْوَى مِنَ الشَّيْطَانِ لِيَحْزُنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيْسَ بِضَارِّهِمْ شَيْئا ً إِلاَّ بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Qīla Lakum Tafassaĥū Fī Al-Majālisi Fāfsaĥū Yafsaĥi Al-Lahu Lakum ۖ Wa 'Idhā Qīla Anshuzū Fānshuzū Yarfa`i Al-Lahu Al-Ladhīna 'Āmanū Minkum Wa Al-Ladhīna 'Ūtū Al-`Ilma Darajātin Wa ۚ Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun | َ058-011 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, "Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قِيلَ لَكُمْ تَفَسَّحُوا فِي الْمَجَالِسِ فَافْسَحُوا يَفْسَحِ اللَّهُ لَكُمْ وَإِذَا ۖ قِيلَ انشُزُوا فَانشُزُوا يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَات ٍ وَاللَّهُ ۚ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِير ٌ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'Idhā Nājaytumu Ar-Rasūla Faqaddimū Bayna Yaday Najwākum Şadaqatan ۚ Dhālika Khayrun Lakum Wa 'Aţharu ۚ Fa'in Lam Tajidū Fa'inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun | َ058-012 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَاجَيْتُمُ الرَّسُولَ فَقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَة ً ذَلِكَ ۚ خَيْر ٌ لَكُمْ وَأَطْهَرُ فَإِنْ ۚ لَمْ تَجِدُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ |
'A'ashfaqtum 'An Tuqaddimū Bayna Yaday Najwākum Şadaqātin ۚ Fa'idh Lam Taf`alū Wa Tāba Al-Lahu `Alaykum Fa'aqīmū Aş-Şalāata Wa 'Ātū Az-Zakāata Wa 'Aţī`ū Al-Laha Wa Rasūlahu Wa ۚ Allāhu Khabīrun Bimā Ta`malūna | َ058-013 Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa. | أَأَشْفَقْتُمْ أَنْ تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيْ نَجْوَاكُمْ صَدَقَات ٍ ۚ فَإِذْ لَمْ تَفْعَلُوا وَتَابَ اللَّهُ عَلَيْكُمْ فَأَقِيمُوا الصَّلاَةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ ۚ وَاللَّهُ خَبِير ٌ بِمَا تَعْمَلُونَ |
'Alam Tará 'Ilá Al-Ladhīna Tawallaw Qawmāan Ghađiba Al-Lahu `Alayhim Mā Hum Minkum Wa Lā Minhum Wa Yaĥlifūna `Alá Al-Kadhibi Wa Hum Ya`lamūna | َ058-014 Ashe, baka ga waɗanda suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane? | أَلَمْ تَرَى إِلَى الَّذِينَ تَوَلَّوْا قَوْماً غَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مَا هُمْ مِنْكُمْ وَلاَ مِنْهُمْ وَيَحْلِفُونَ عَلَى الْكَذِبِ وَهُمْ يَعْلَمُونَ |
'A`adda Al-Lahu Lahum `Adhābāan Shadīdāan ۖ 'Innahum Sā'a Mā Kānū Ya`malūna | َ058-015 Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana. | أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ عَذَابا ً شَدِيدا ً ۖ إِنَّهُمْ سَاءَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ |
Attakhadhū 'Aymānahum Junnatan Faşaddū `An Sabīli Al-Lahi Falahum `Adhābun Muhīnun | َ058-016 Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa. | اتَّخَذُوا أَيْمَانَهُمْ جُنَّة ً فَصَدُّوا عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ فَلَهُمْ عَذَاب ٌ مُهِين ٌ |
Lan Tughniya `Anhum 'Amwāluhum Wa Lā 'Awlāduhum Mina Al-Lahi Shay'āan ۚ 'Ūlā'ika 'Aşĥābu An-Nāri ۖ Hum Fīhā Khālidūna | َ058-017 Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta. | لَنْ تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُمْ مِنَ اللَّهِ شَيْئاً ۚ أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ |
Yawma Yab`athuhumu Al-Lahu Jamī`āan Fayaĥlifūna Lahu Kamā Yaĥlifūna Lakum ۖ Wa Yaĥsabūna 'Annahum `Alá Shay'in ۚ 'Alā 'Innahum Humu Al-Kādhibūna | َ058-018 Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata. | يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ اللَّهُ جَمِيعا ً فَيَحْلِفُونَ لَه ُُ كَمَا يَحْلِفُونَ لَكُمْ ۖ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ عَلَى شَيْءٍ ۚ أَلاَ إِنَّهُمْ هُمُ الْكَاذِبُونَ |
Astaĥwadha `Alayhimu Ash-Shayţānu Fa'ansāhum Dhikra Al-Lahi ۚ 'Ūlā'ika Ĥizbu Ash-Shayţāni ۚ 'Alā 'Inna Ĥizba Ash-Shayţāni Humu Al-Khāsirūna | َ058-019 Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra. | اسْتَحْوَذَ عَلَيْهِمُ الشَّيْطَانُ فَأَنسَاهُمْ ذِكْرَ اللَّهِ ۚ أُوْلَائِكَ حِزْبُ الشَّيْطَانِ ۚ أَلاَ إِنَّ حِزْبَ الشَّيْطَانِ هُمُ الْخَاسِرُونَ |
'Inna Al-Ladhīna Yuĥāddūna Al-Laha Wa Rasūlahu 'Ūlā'ika Fī Al-'Adhallīna | َ058-020 Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin (mutãne) mafi ƙasƙanci. | إِنَّ الَّذِينَ يُحَادُّونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ~ُ أُوْلَائِكَ فِي الأَذَلِّينَ |
Kataba Al-Lahu La'aghlibanna 'Anā Wa Rusulī ۚ 'Inna Al-Laha Qawīyun `Azīzun | َ058-021 Allah Ya rubũta cẽwa," Lalle zan rinjãya, Nĩ da ManzanniNa." Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. | كَتَبَ اللَّهُ لَأَغْلِبَنَّ أَنَا وَرُسُلِي ۚ إِنَّ اللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيز ٌ |
Lā Tajidu Qawmāan Yu'uminūna Bil-Lahi Wa Al-Yawmi Al-'Ākhiri Yuwāddūna Man Ĥādda Al-Laha Wa Rasūlahu Wa Law Kānū 'Ābā'ahum 'Aw 'Abnā'ahum 'Aw 'Ikhwānahum 'Aw `Ashīratahum ۚ 'Ūlā'ika Kataba Fī Qulūbihimu Al-'Īmāna Wa 'Ayyadahum Birūĥin Minhu ۖ Wa Yudkhiluhum Jannātin Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā ۚ Rađiya Al-Lahu `Anhum Wa Rađū `Anhu ۚ 'Ūlā'ika Ĥizbu Al-Lahi ۚ 'Alā 'Inna Ĥizba Al-Lahi Humu Al-Mufliĥūna | َ058-022 Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo. | لاَ تَجِدُ قَوْما ً يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَه ُُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ ۚ أُوْلَائِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الإِيمَانَ وَأَيَّدَهُمْ بِرُوح ٍ مِنْهُ ۖ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّات ٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ۚ أُوْلَائِكَ حِزْبُ اللَّهِ ۚ أَلاَ إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ |