Sabbaĥa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Huwa Al-`Azīzu Al-Ĥakīmu | َ057-001 Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. | سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ |
Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi ۖ Yuĥyī Wa Yumītu ۖ Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Qadīrun | َ057-002 Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme. | لَه ُُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ قَدِير ٌ |
Huwa Al-'Awwalu Wa Al-'Ākhiru Wa Až-Žāhiru Wa Al-Bāţinu ۖ Wa Huwa Bikulli Shay'in `Alīmun | َ057-003 Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme. | هُوَ الأَوَّلُ وَالآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيم ٌ |
Huwa Al-Ladhī Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Fī Sittati 'Ayyāmin Thumma Astawá `Alá Al-`Arshi ۚ Ya`lamu Mā Yaliju Fī Al-'Arđi Wa Mā Yakhruju Minhā Wa Mā Yanzilu Mina As-Samā'i Wa Mā Ya`ruju Fīhā ۖ Wa Huwa Ma`akum 'Ayna Mā Kuntum Wa ۚ Allāhu Bimā Ta`malūna Başīrun | َ057-004 Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. | هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّام ٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ ۚ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا ۖ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير ٌ |
Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi ۚ Wa 'Ilá Al-Lahi Turja`u Al-'Umūru | َ057-005 Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura. | لَه ُُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ ۚ وَإِلَى اللَّهِ تُرْجَعُ الأُمُورُ |
Yūliju Al-Layla Fī An-Nahāri Wa Yūliju An-Nahāra Fī Al-Layli ۚ Wa Huwa `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri | َ057-006 Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza. | يُولِجُ اللَّيْلَ فِي النَّهَارِ وَيُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ ۚ وَهُوَ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ |
'Āminū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Wa 'Anfiqū Mimmā Ja`alakum Mustakhlafīna Fīhi ۖ Fa-Al-Ladhīna 'Āmanū Minkum Wa 'Anfaqū Lahum 'Ajrun Kabīrun | َ057-007 Ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma. | آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِه ِِ وَأَنْفِقُوا مِمَّا جَعَلَكُمْ مُسْتَخْلَفِينَ فِيه ِِ ۖ فَالَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَأَنْفَقُوا لَهُمْ أَجْر ٌ كَبِير ٌ |
Wa Mā Lakum Lā Tu'uminūna Bil-Lahi Wa ۙ Ar-Rasūlu Yad`ūkum Litu'uminū Birabbikum Wa Qad 'Akhadha Mīthāqakum 'In Kuntum Mu'uminīna | َ057-008 kuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzonSa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance mãsu ĩmãni. | وَمَا لَكُمْ لاَ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ ۙ وَالرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ لِتُؤْمِنُوا بِرَبِّكُمْ وَقَدْ أَخَذَ مِيثَاقَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ |
Huwa Al-Ladhī Yunazzilu `Alá `Abdihi 'Āyātin Bayyinātin Liyukhrijakum Mina Až-Žulumāti 'Ilá An-Nūri ۚ Wa 'Inna Al-Laha Bikum Lara'ūfun Raĥīmun | َ057-009 Shĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga BãwanSa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai. | هُوَ الَّذِي يُنَزِّلُ عَلَى عَبْدِهِ آيَات ٍ بَيِّنَات ٍ لِيُخْرِجَكُمْ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ ۚ وَإِنَّ اللَّهَ بِكُمْ لَرَءُوف ٌ رَحِيم ٌ |
Wa Mā Lakum 'Allā Tunfiqū Fī Sabīli Al-Lahi Wa Lillahi Mīrāthu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi ۚ Lā Yastawī Minkum Man 'Anfaqa Min Qabli Al-Fatĥi Wa Qātala ۚ 'Ūlā'ika 'A`žamu Darajatan Mina Al-Ladhīna 'Anfaqū Min Ba`du Wa Qātalū ۚ Wa Kullāan Wa`ada Al-Lahu Al-Ĥusná Wa ۚ Allāhu Bimā Ta`malūna Khabīrun | َ057-010 Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. | وَمَا لَكُمْ أَلاَّ تُنْفِقُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ ۚ لاَ يَسْتَوِي مِنْكُمْ مَنْ أَنْفَقَ مِنْ قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ ۚ أُوْلَائِكَ أَعْظَمُ دَرَجَة ً مِنَ الَّذِينَ أَنْفَقُوا مِنْ بَعْدُ وَقَاتَلُوا ۚ وَكُلاّ ً وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَى ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِير ٌ |
Man Dhā Al-Ladhī Yuqriđu Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan Fayuđā`ifahu Lahu Wa Lahu 'Ajrun Karīmun | َ057-011 Wãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya)kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)? | مَنْ ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضاً حَسَنا ً فَيُضَاعِفَه ُُ لَه ُُ وَلَهُ~ُ أَجْر ٌ كَرِيم ٌ |
Yawma Tará Al-Mu'uminīna Wa Al-Mu'umināti Yas`á Nūruhum Bayna 'Aydīhim Wa Bi'aymānihim Bushrākumu Al-Yawma Jannātun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru Khālidīna Fīhā ۚ Dhālika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu | َ057-012 Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma. | يَوْمَ تَرَى الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ يَسْعَى نُورُهُمْ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ بُشْرَاكُمُ الْيَوْمَ جَنَّات ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ |
Yawma Yaqūlu Al-Munāfiqūna Wa Al-Munāfiqātu Lilladhīna 'Āmanū Anžurūnā Naqtabis Min Nūrikum Qīla Arji`ū Warā'akum Fāltamisū Nūrāan Fađuriba Baynahum Bisūrin Lahu Bābun Bāţinuhu Fīhi Ar-Raĥmatu Wa Žāhiruhu Min Qibalihi Al-`Adhābu | َ057-013 Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take. | يَوْمَ يَقُولُ الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ لِلَّذِينَ آمَنُوا انْظُرُونَا نَقْتَبِسْ مِنْ نُورِكُمْ قِيلَ ارْجِعُوا وَرَاءَكُمْ فَالْتَمِسُوا نُورا ً فَضُرِبَ بَيْنَهُمْ بِسُور ٍ لَه ُُ بَاب ٌ بَاطِنُه ُُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُه ُُ مِنْ قِبَلِهِ الْعَذَابُ |
Yunādūnahum 'Alam Nakun Ma`akum ۖ Qālū Balá Wa Lakinnakum Fatantum 'Anfusakum Wa Tarabbaştum Wa Artabtum Wa Gharratkumu Al-'Amānīyu Ĥattá Jā'a 'Amru Al-Lahi Wa Gharrakum Bil-Lahi Al-Gharūru | َ057-014 Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah." | يُنَادُونَهُمْ أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ ۖ قَالُوا بَلَى وَلَكِنَّكُمْ فَتَنْتُمْ أَنْفُسَكُمْ وَتَرَبَّصْتُمْ وَارْتَبْتُمْ وَغَرَّتْكُمُ الأَمَانِيُّ حَتَّى جَاءَ أَمْرُ اللَّهِ وَغَرَّكُمْ بِاللَّهِ الْغَرُورُ |
Fālyawma Lā Yu'ukhadhu Minkum Fidyatun Wa Lā Mina Al-Ladhīna Kafarū ۚ Ma'wākumu An-Nāru ۖ Hiya Mawlākum ۖ Wa Bi'sa Al-Maşīru | َ057-015 "To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana." | فَالْيَوْمَ لاَ يُؤْخَذُ مِنْكُمْ فِدْيَة ٌ وَلاَ مِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ مَأْوَاكُمُ النَّارُ ۖ هِيَ مَوْلاَكُمْ ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ |
'Alam Ya'ni Lilladhīna 'Āmanū 'An Takhsha`a Qulūbuhum Lidhikri Al-Lahi Wa Mā Nazala Mina Al-Ĥaqqi Wa Lā Yakūnū Kālladhīna 'Ūtū Al-Kitāba Min Qablu Faţāla `Alayhimu Al-'Amadu Faqasat Qulūbuhum ۖ Wa Kathīrun Minhum Fāsiqūna | َ057-016 Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne. | أَلَمْ يَأْنِ لِلَّذِينَ آمَنُوا أَنْ تَخْشَعَ قُلُوبُهُمْ لِذِكْرِ اللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ الْحَقِّ وَلاَ يَكُونُوا كَالَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلُ فَطَالَ عَلَيْهِمُ الأَمَدُ فَقَسَتْ قُلُوبُهُمْ ۖ وَكَثِير ٌ مِنْهُمْ فَاسِقُونَ |
A`lamū 'Anna Al-Laha Yuĥyī Al-'Arđa Ba`da Mawtihā ۚ Qad Bayyannā Lakumu Al-'Āyāti La`allakum Ta`qilūna | َ057-017 Ku sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali. | اعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يُحْيِي الأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ الآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ |
'Inna Al-Muşşaddiqīna Wa Al-Muşşaddiqāti Wa 'Aqrađū Al-Laha Qarđāan Ĥasanāan Yuđā`afu Lahum Wa Lahum 'Ajrun Karīmun | َ057-018 Lalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci. | إِنَّ الْمُصَّدِّقِينَ وَالْمُصَّدِّقَاتِ وَأَقْرَضُوا اللَّهَ قَرْضاً حَسَنا ً يُضَاعَفُ لَهُمْ وَلَهُمْ أَجْر ٌ كَرِيم ٌ |
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa Rusulihi 'Ūlā'ika Humu ۖ Aş-Şiddīqūna Wa Ash-Shuhadā'u `Inda Rabbihim Lahum 'Ajruhum ۖ Wa Nūruhum Wa Al-Ladhīna Kafarū Wa Kadhdhabū Bi'āyātinā 'Ūlā'ika 'Aşĥābu Al-Jaĥīmi | َ057-019 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su ne'yan Jahĩm. | وَالَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِهِ~ِ أُوْلَائِكَ هُمُ الصِّدِّيقُونَ ۖ وَالشُّهَدَاءُ عِنْدَ رَبِّهِمْ لَهُمْ أَجْرُهُمْ وَنُورُهُمْ ۖ وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُوْلَائِكَ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ |
A`lamū 'Annamā Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā La`ibun Wa Lahwun Wa Zīnatun Wa Tafākhurun Baynakum Wa Takāthurun Fī Al-'Amwli Wa Al-'Awlādi ۖ Kamathali Ghaythin 'A`jaba Al-Kuffāra Nabātuhu Thumma Yahīju Fatarāhu Muşfarrāan Thumma Yakūnu Ĥuţāmāan ۖ Wa Fī Al-'Ākhirati `Adhābun Shadīdun Wa Maghfiratun Mina Al-Lahi Wa Riđwānun ۚ Wa Mā Al-Ĥayāatu Ad-Dunyā 'Illā Matā`u Al-Ghurūri | َ057-020 Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai. | اعْلَمُوا أَنَّمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا لَعِب ٌ وَلَهْو ٌ وَزِينَة ٌ وَتَفَاخُر ٌ بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُر ٌ فِي الأَمْوالِ وَالأَوْلاَدِ ۖ كَمَثَلِ غَيْثٍ أَعْجَبَ الْكُفَّارَ نَبَاتُه ُُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاه ُُ مُصْفَرّا ً ثُمَّ يَكُونُ حُطَاما ً ۖ وَفِي الآخِرَةِ عَذَاب ٌ شَدِيد ٌ وَمَغْفِرَة ٌ مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَان ٌ ۚ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ مَتَاعُ الْغُرُورِ |
Sābiqū 'Ilá Maghfiratin Min Rabbikum Wa Jannatin `Arđuhā Ka`arđi As-Samā'i Wa Al-'Arđi 'U`iddat Lilladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa Rusulihi ۚ Dhālika Fađlu Al-Lahi Yu'utīhi Man Yashā'u Wa ۚ Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi | َ057-021 Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma. | سَابِقُوا إِلَى مَغْفِرَة ٍ مِنْ رَبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا كَعَرْضِ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ أُعِدَّتْ لِلَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرُسُلِه ِِ ۚ ذَلِكَ فَضْلُ اللَّهِ يُؤْتِيه ِِ مَنْ يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ |
Mā 'Aşāba Min Muşībatin Fī Al-'Arđi Wa Lā Fī 'Anfusikum 'Illā Fī Kitābin Min Qabli 'An Nabra'ahā ۚ 'Inna Dhālika `Alá Al-Lahi Yasīrun | َ057-022 Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne. | مَا أَصَابَ مِنْ مُصِيبَة ٍ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي أَنْفُسِكُمْ إِلاَّ فِي كِتَاب ٍ مِنْ قَبْلِ أَنْ نَبْرَأَهَا ۚ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِير ٌ |
Likaylā Ta'saw `Alá Mā Fātakum Wa Lā Tafraĥū Bimā 'Ātākum Wa ۗ Allāhu Lā Yuĥibbu Kulla Mukhtālin Fakhūrin | َ057-023 Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari. | لِكَيْلاَ تَأْسَوْا عَلَى مَا فَاتَكُمْ وَلاَ تَفْرَحُوا بِمَا آتَاكُمْ ۗ وَاللَّهُ لاَ يُحِبُّ كُلَّ مُخْتَال ٍ فَخُور ٍ |
Al-Ladhīna Yabkhalūna Wa Ya'murūna An-Nāsa Bil-Bukhli ۗ Wa Man Yatawalla Fa'inna Al-Laha Huwa Al-Ghanīyu Al-Ĥamīdu | َ057-024 Watau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde. | الَّذِينَ يَبْخَلُونَ وَيَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبُخْلِ ۗ وَمَنْ يَتَوَلَّ فَإِنَّ اللَّهَ هُوَ الْغَنِيُّ الْحَمِيدُ |
Laqad 'Arsalnā Rusulanā Bil-Bayyināti Wa 'Anzalnā Ma`ahumu Al-Kitāba Wa Al-Mīzāna Liyaqūma An-Nāsu Bil-Qisţi ۖ Wa 'Anzalnā Al-Ĥadīda Fīhi Ba'sun Shadīdun Wa Manāfi`u Lilnnāsi Wa Liya`lama Al-Lahu Man Yanşuruhu Wa Rusulahu Bil-Ghaybi ۚ 'Inna Al-Laha Qawīyun `Azīzun | َ057-025 Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. | لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنْزَلْنَا مَعَهُمُ الْكِتَابَ وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ ۖ وَأَنْزَلْنَا الْحَدِيدَ فِيه ِِ بَأْس ٌ شَدِيد ٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ مَنْ يَنْصُرُه ُُ وَرُسُلَه ُُ بِالْغَيْبِ ۚ إِنَّ اللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيز ٌ |
Wa Laqad 'Arsalnā Nūĥāan Wa 'Ibrāhīma Wa Ja`alnā Fī Dhurrīyatihimā An-Nubūwata Wa Al-Kitāba ۖ Faminhum Muhtadin ۖ Wa Kathīrun Minhum Fāsiqūna | َ057-026 Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne. | وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحا ً وَإِبْرَاهِيمَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِمَا النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ ۖ فَمِنْهُمْ مُهْتَد ٍ ۖ وَكَثِير ٌ مِنْهُمْ فَاسِقُونَ |
Thumma Qaffaynā `Alá 'Āthārihim Birusulinā Wa Qaffaynā Bi`īsá Abni Maryama Wa 'Ātaynāhu Al-'Injīla Wa Ja`alnā Fī Qulūbi Al-Ladhīna Attaba`ūhu Ra'fatan Wa Raĥmatan Wa Rahbānīyatan Abtada`ūhā Mā Katabnāhā `Alayhim 'Illā Abtighā'a Riđwāni Al-Lahi Famā Ra`awhā Ĥaqqa Ri`āyatihā ۖ Fa'ātaynā Al-Ladhīna 'Āmanū Minhum 'Ajrahum ۖ Wa Kathīrun Minhum Fāsiqūna | َ057-027 Sa'an nan Muka biyar a bãyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne. | ثُمَّ قَفَّيْنَا عَلَى آثَارِهِمْ بِرُسُلِنَا وَقَفَّيْنَا بِعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ وَآتَيْنَاهُ الإِنجِيلَ وَجَعَلْنَا فِي قُلُوبِ الَّذِينَ اتَّبَعُوه ُُ رَأْفَة ً وَرَحْمَة ً وَرَهْبَانِيَّة ً ابْتَدَعُوهَا مَا كَتَبْنَاهَا عَلَيْهِمْ إِلاَّ ابْتِغَاءَ رِضْوَانِ اللَّهِ فَمَا رَعَوْهَا حَقَّ رِعَايَتِهَا ۖ فَآتَيْنَا الَّذِينَ آمَنُوا مِنْهُمْ أَجْرَهُمْ ۖ وَكَثِير ٌ مِنْهُمْ فَاسِقُونَ |
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Al-Laha Wa 'Āminū Birasūlihi Yu'utikum Kiflayni Min Raĥmatihi Wa Yaj`al Lakum Nūrāan Tamshūna Bihi Wa Yaghfir Lakum Wa ۚ Allāhu Ghafūrun Raĥīmun | َ057-028 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama. | يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَآمِنُوا بِرَسُولِه ِِ يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِنْ رَحْمَتِه ِِ وَيَجْعَلْ لَكُمْ نُورا ً تَمْشُونَ بِه ِِ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ۚ غَفُور ٌ رَحِيم ٌ |
Li'allā Ya`lama 'Ahlu Al-Kitābi 'Allā Yaqdirūna `Alá Shay'in Min Fađli Al-Lahi ۙ Wa 'Anna Al-Fađla Biyadi Al-Lahi Yu'utīhi Man Yashā'u Wa ۚ Allāhu Dhū Al-Fađli Al-`Ažīmi | َ057-029 Dõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma. | لِئَلاَّ يَعْلَمَ أَهْلُ الْكِتَابِ أَلاَّ يَقْدِرُونَ عَلَى شَيْء ٍ مِنْ فَضْلِ اللَّهِ ۙ وَأَنَّ الْفَضْلَ بِيَدِ اللَّهِ يُؤْتِيه ِِ مَنْ يَشَاءُ ۚ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ |