56) Sūrat Al-Wāqi`ah

Printed format

56)

'Idhā Waqa`ati Al-Wāqi`ahu 056-001 Idan mai aukuwa ta auku.
Laysa Liwaq`atihā Kādhibahun 056-002 Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
Khāfiđatun Rāfi`ahun 056-003 (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
'Idhā Rujjati Al-'Arđu Rajjāan 056-004 Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
Wa Bussati Al-Jibālu Bassāan 056-005 Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
Fakānat Habā'an Munbaththāan 056-006 Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
Wa Kuntum 'Azwājāan Thalāthahan 056-007 Kuma kun kasance nau'i uku.
Fa'aşĥābu Al-Maymanati Mā 'Aşĥābu Al-Maymanahi 056-008 Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
Wa 'Aşĥābu Al-Mash'amati Mā 'Aşĥābu Al-Mash'amahi 056-009 Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
Wa As-Sābiqūna As-Sābiqūna 056-010 Da waɗanda suka tsẽre.Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
'Ūlā'ika Al-Muqarrabūna 056-011 Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
Fī Jannāti An-Na`īmi 056-012 A ckin Aljannar ni'ima.
Thullatun Mina Al-'Awwalīna 056-013 Jama'a ne daga mutãnen farko.
Wa Qalīlun Mina Al-'Ākhirīna 056-014 Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
`Alá Sururin Mawđūnahin 056-015 (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
Muttaki'īna `Alayhā Mutaqābilīna 056-016 Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
Yaţūfu `Alayhim Wildānun Mukhalladūna 056-017 Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
Bi'akwābin Wa 'Abārīqa Wa Ka'sin Min Ma`īnin 056-018 Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
Lā Yuşadda`ūna `Anhā Wa Lā Yunzifūna 056-019 Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
Wa Fākihatin Mimmā Yatakhayyarūna 056-020 Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
Wa Laĥmi Ţayrin Mimmā Yashtahūna 056-021 Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
Wa Ĥūrun `Īnun 056-022 Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
Ka'amthāli Al-Lu'ulu'ui Al-Maknūni 056-023 Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
Jazā'an Bimā Kānū Ya`malūna 056-024 A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Lā Yasma`ūna Fīhā Laghwan Wa Lā Ta'thīmāan 056-025 Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
'Illā Qīlāan Salāmāan Salāmāan 056-026 Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
Wa 'Aşĥābu Al-Yamīni Mā 'Aşĥābu Al-Yamīni 056-027 Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
Fī Sidrin Makhđūdin 056-028 (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
Wa Ţalĥin Manđūdin 056-029 Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
Wa Žillin Mamdūdin 056-030 Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
Wa Mā'in Maskūbin 056-031 Da wani ruwa mai gudãna.
Wa Fākihatin Kathīrahin 056-032 Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
Lā Maqţū`atin Wa Lā Mamnū`ahin 056-033 Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
Wa Furushin Marfū`ahin 056-034 Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
'Innā 'Ansha'nāhunna 'Inshā'an 056-035 Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
Faja`alnāhunna 'Abkārāan 056-036 Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
`Urubāan 'Atrābāan 056-037 Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
Li'aşĥābi Al-Yamīni 056-038 Ga mazõwa dãma.
Thullatun Mina Al-'Awwalīna 056-039 Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
Wa Thullatun Mina Al-'Ākhirīna 056-040 Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
Wa 'Aşĥābu Ash-Shimāli Mā 'Aşĥābu Ash-Shimāli 056-041 Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
Fī Samūmin Wa Ĥamīmin 056-042 Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
Wa Žillin Min Yaĥmūmin 056-043 Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
Lā Bāridin Wa Lā Karīmin 056-044 Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
'Innahum Kānū Qabla Dhālika Mutrafīna 056-045 Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
Wa Kānū Yuşirrūna `Alá Al-Ĥinthi Al-`Ažīmi 056-046 Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
Wa Kānū Yaqūlūna 'A'idhā Mitnā Wa Kunnā Turābāan Wa `Ižāmāan 'A'innā Lamabthūna 056-047 Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
'Awa 'Ābā'uunā Al-'Awwalūna 056-048 "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
Qul 'Inna Al-'Awwalīna Wa Al-'Ākhirīna 056-049 Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
Lamajmū`ūna 'Ilá Mīqāti Yawmin Ma`lūmin 056-050 "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
Thumma 'Innakum 'Ayyuhā Ađ-Đāllūna Al-Mukadhdhibūna 056-051 "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
La'ākilūna Min Shajarin Min Zaqqūmin 056-052 "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
Famāli'ūna Minhā Al-Buţūna 056-053 "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
Fashāribūna `Alayhi Mina Al-Ĥamīmi 056-054 "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
Fashāribūna Shurba Al-Hīmi 056-055 "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
dhā Nuzuluhum Yawma Ad-Dīni 056-056 Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
Naĥnu Khalaqnākum Falawlā Tuşaddiqūna 056-057 Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
'Afara'aytum Mā Tumnūna 056-058 Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
'A'antum Takhluqūnahu 'Am Naĥnu Al-Khāliqūna 056-059 Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? ~
Naĥnu Qaddarnā Baynakumu Al-Mawta Wa Mā Naĥnu Bimasbūqīna 056-060 Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
`Alá 'An Nubaddila 'Amthālakum Wa Nunshi'akum Fī Mā Lā Ta`lamūna 056-061 A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
Wa Laqad `Alimtumu An-Nash'ata Al-'Ūlá Falawlā Tadhkkarūna 056-062 Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
'Afara'aytum Mā Taĥruthūna 056-063 Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
'A'antum Tazra`ūnahu 'Am Naĥnu Az-Zāri`ūna 056-064 Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa? ~
Law Nashā'u Laja`alnāhu Ĥuţāmāan Fažalaltum Tafakkahūna 056-065 Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa,sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
'Innā Lamughramūna 056-066 (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
Bal Naĥnu Maĥrūmūna 056-067 "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
'Afara'aytumu Al-Mā'a Al-Ladhī Tashrabūna 056-068 Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
'A'antum 'Anzaltumūhu Mina Al-Muzni 'Am Naĥnu Al-Munzilūna 056-069 Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
Law Nashā'u Ja`alnāhu 'Ujājāan Falawlā Tashkurūna 056-070 Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa? ~
'Afara'aytumu An-Nāra Allatī Tūrūna 056-071 Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
'A'antum 'Ansha'tum Shajaratahā 'Am Naĥnu Al-Munshi'ūna 056-072 Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
Naĥnu Ja`alnāhā Tadhkiratan Wa Matā`āan Lilmuqwīna 056-073 Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
Fasabbiĥ Biāsmi Rabbika Al-`Ažīmi 056-074 Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
Falā 'Uqsimu Bimawāqi`i An-Nujūmi 056-075 To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
Wa 'Innahu Laqasamun Law Ta`lamūna `Ažīmun 056-076 Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
'Innahu Laqur'ānun Karīmun 056-077 Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
Fī Kitābin Maknūnin 056-078 A cikin wani littafi tsararre.
Lā Yamassuhu 'Illā Al-Muţahharūna 056-079 Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. ~
Tanzīlun Min Rabbi Al-`Ālamīna 056-080 Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
'Afabihadhā Al-Ĥadīthi 'Antum Mud/hinūna 056-081 Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
Wa Taj`alūna Rizqakum 'Annakum Tukadhdhibūna 056-082 Kuma kunã sanya arzikinku ( game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
Falawlā 'Idhā Balaghati Al-Ĥulqūma 056-083 To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
Wa 'Antum Ĥīna'idhin Tanžurūna 056-084 Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
Wa Naĥnu 'Aqrabu 'Ilayhi Minkum Wa Lakin Lā Tubşirūna 056-085 Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
Falawlā 'In Kuntum Ghayra Madīnīna 056-086 To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
Tarji`ūnahā 'In Kuntum Şādiqīna 056-087 Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya .
Fa'ammā 'In Kāna Mina Al-Muqarrabīna 056-088 To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
Farawĥun Wa Rayĥānun Wa Jannatu Na`īmin 056-089 Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
Wa 'Ammā 'In Kāna Min 'Aşĥābi Al-Yamīni 056-090 Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
Fasalāmun Laka Min 'Aşĥābi Al-Yamīni 056-091 Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
Wa 'Ammā 'In Kāna Mina Al-Mukadhdhibīna Ađ-Đāllīna 056-092 Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
Fanuzulun Min Ĥamīmin 056-093 Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
Wa Taşliyatu Jaĥīmin 056-094 Da ƙõnuwa da Jahĩm,
'Inna Hādhā Lahuwa Ĥaqqu Al-Yaqīni 056-095 Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
Fasabbiĥ Biāsmi Rabbika Al-`Ažīmi 056-096 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
Next Sūrah