55) Sūrat Ar-Raĥmān

Printed format

55)

Ar-Raĥmānu 055-001 (Allah) Mai rahama.
`Allama Al-Qur'āna 055-002 Yã sanar da Alƙur'ani.
Khalaqa Al-'Insāna 055-003 Yã halitta mutum.
`Allamahu Al-Bayāna 055-004 Yã sanar da shi bayãni (magana).
Ash-Shamsu Wa Al-Qamaru Biĥusbānin 055-005 Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
Wa An-Najmu Wa Ash-Shajaru Yasjudāni 055-006 Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
Wa As-Samā'a Rafa`ahā Wa Wađa`a Al-Mīzāna 055-007 Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
'Allā Taţghaw Fī Al-Mīzāni 055-008 Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
Wa 'Aqīmū Al-Wazna Bil-Qisţi Wa Lā Tukhsirū Al-Mīzāna 055-009 Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
Wa Al-'Arđa Wađa`ahā Lil'anāmi 055-010 Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
Fīhā Fākihatun Wa An-Nakhlu Dhātu Al-'Akmāmi 055-011 A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
Wa Al-Ĥabbu Dhū Al-`Aşfi Wa Ar-Rayĥānu 055-012 Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-013 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
Khalaqa Al-'Insāna Min Şalşālin Kālfakhkhāri 055-014 Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
Wa Khalaqa Al-Jānna Minrijin Min Nārin 055-015 Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-016 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Rabbu Al-Mashriqayni Wa Rabbu Al-Maghribayni 055-017 Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-018 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Maraja Al-Baĥrayni Yaltaqiyāni 055-019 Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
Baynahumā Barzakhun Lā Yabghiyāni 055-020 A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-021 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Yakhruju Minhumā Al-Lu'ulu'uu Wa Al-Marjānu 055-022 Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-023 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Wa Lahu Al-Jawāri Al-Munsha'ātu Fī Al-Baĥri Kāl'a`lāmi 055-024 Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-025 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Kullu Man `Alayhā Fānin 055-026 Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.
Wa Yabqá Wajhu Rabbika Dhū Al-Jalāli Wa Al-'Ikrāmi 055-027 Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-028 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Yas'aluhu Man As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۚ  Kulla Yawmin Huwa Fī Sha'nin 055-029 wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.  ۚ 
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-030 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Sanafrughu Lakum 'Ayyuhā Ath-Thaqalāni 055-031 Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-032 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Yā Ma`shara Al-Jinni Wa Al-'Insi 'Ini Astaţa`tum 'An Tanfudhū Min 'Aqţāri As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Fānfudhū  ۚ  Lā Tanfudhūna 'Illā Bisulţānin 055-033 Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.  ۚ 
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-034 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Yursalu `Alaykumā Shuwāžun Min Nārin Wa Nuĥāsun Falā Tantaşirāni 055-035 Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-036 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fa'idhā Anshaqqati As-Samā'u Fakānat Wardatan Kālddihāni 055-037 Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-038 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fayawma'idhin Lā Yus'alu `An Dhanbihi 'Insun Wa Lā Jānnun 055-039 To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani. ~
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-040 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Yu`rafu Al-Mujrimūna Bisīmāhum Fayu'ukhadhu Bin-Nawāşī Wa Al-'Aqdāmi 055-041 zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-042 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Hadhihi Jahannamu Allatī Yukadhdhibu Bihā Al-Mujrimūna 055-043 Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
Yaţūfūna Baynahā Wa Bayna Ĥamīmin 'Ānin 055-044 Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-045 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Wa Liman Khāfa Maqāma Rabbihi Jannatāni 055-046 Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-047 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Dhawātā 'Afnānin 055-048 Mãsu rassan itãce.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-049 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhimā `Aynāni Tajriyāni 055-050 A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-051 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhimā Min Kulli Fākihatin Zawjāni 055-052 A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-053 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Muttaki'īna `Alá Furushin Baţā'inuhā Min 'Istabraqin  ۚ  Wa Janá Al-Jannatayni Dānin 055-054 Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.  ۚ 
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-055 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhinna Qāşirātu Aţ-Ţarfi Lam Yaţmithhunna 'Insun Qablahum Wa Lā Jānnun 055-056 A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-057 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Ka'annahunna Al-Yāqūtu Wa Al-Marjānu 055-058 Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-059 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Hal Jazā'u Al-'Iĥsāni 'Illā Al-'Iĥsānu 055-060 Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-061 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Wa Min Dūnihimā Jannatāni 055-062 Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-063 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Mud/hāmmatāni 055-064 Mãsu duhun inuwa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-065 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhimā `Aynāni Nađđākhatāni 055-066 A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-067 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhimā Fākihatun Wa Nakhlun Wa Rummānun 055-068 A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-069 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Fīhinna Khayrātun Ĥisānun 055-070 A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-071 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Ĥūrun Maqşūrātun Al-Khiyāmi 055-072 Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-073 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Lam Yaţmithhunna 'Insun Qablahum Wa Lā Jānnun 055-074 Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-075 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Muttaki'īna `Alá Rafrafin Khrin Wa `Abqarīyin Ĥisānin 055-076 Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbikumā Tukadhdhibāni 055-077 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
Tabāraka Asmu Rabbika Dhī Al-Jalāli Wa Al-'Ikrāmi 055-078 Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.
Next Sūrah