54) Sūrat Al-Qamar

Printed format

54)

Aqtarabati As-Sā`atu Wa Anshaqqa Al-Qamaru 054-001 Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
Wa 'In Yaraw 'Āyatan Yu`riđū Wa Yaqūlū Siĥrun Mustamirrun 054-002 Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
Wa Kadhdhabū Wa Attaba`ū 'Ahwā'ahum  ۚ  Wa Kullu 'Amrin Mustaqirrun 054-003 Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.  ۚ 
Wa Laqad Jā'ahum Mina Al-'Anbā'i Mā Fīhi Muzdajarun 054-004 Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
Ĥikmatun Bālighatun  ۖ  Famā Tughni An-Nudhuru 054-005 Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.  ۖ 
Fatawalla `Anhum  ۘ  Yawma Yad`u Ad-Dā`i 'Ilá Shay'in Nukurin 054-006 Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.  ۘ 
Khushsha`āan 'Abşāruhum Yakhrujūna Mina Al-'Ajthi Ka'annahum Jarādun Muntashirun 054-007 ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
Muhţi`īna 'Ilá Ad-Dā`i  ۖ  Yaqūlu Al-Kāfirūna Hādhā Yawmun `Asirun 054-008 Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"  ۖ 
Kadhdhabat Qablahum Qawmu Nūĥin Fakadhdhabū `Abdanā Wa Qālū Majnūnun Wa Azdujira 054-009 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
Fada`ā Rabbahu 'Annī Maghlūbunntaşir 054-010 Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako." ~
Fafataĥnā 'Abwāba As-Samā'i Bimā'in Munhamirin 054-011 Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
Wa Fajjarnā Al-'Arđa `Uyūnāan Fāltaqá Al-Mā'u `Alá 'Amrin Qad Qudira 054-012 Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
Wa Ĥamalnāhu `Alá Dhāti 'Alwāĥin Wa Dusurin 054-013 Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
Tajrī Bi'a`yuninā Jazā'an Liman Kāna Kufira 054-014 Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
Wa Laqad Taraknāhā 'Āyatan Fahal Min Muddakirin 054-015 Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
Fakayfa Kāna `Adhābī Wa Nudhuri 054-016 To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
Wa Laqad Yassarnā Al-Qur'āna Lildhdhikri Fahal Min Muddakirin 054-017 Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Kadhdhabat `Ādun Fakayfa Kāna `Adhābī Wa Nudhuri 054-018 Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
'Innā 'Arsalnā `Alayhim Rīĥāan Şarşarāan Fī Yawmi Naĥsin Mustamirrin 054-019 Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
Tanzi`u An-Nāsa Ka'annahum 'A`jāzu Nakhlin Munqa`irin 054-020 Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
Fakayfa Kāna `Adhābī Wa Nudhuri 054-021 To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
Wa Laqad Yassarnā Al-Qur'āna Lildhdhikri Fahal Min Muddakirin 054-022 Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Kadhdhabat Thamūdu Bin-Nudhuri 054-023 Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
Faqālū 'Abasharāan Minnā Wāĥidāan Nattabi`uhu 'Innā 'Idhāan Lafī Đalālin Wa Su`urin 054-024 Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. ~
'A'uulqiya Adh-Dhikru `Alayhi Min Bayninā Bal Huwa Kadhdhābun 'Ashirun 054-025 "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
Saya`lamūna Ghadāan Mani Al-Kadhdhābu Al-'Ashiru 054-026 Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
'Innā Mursilū An-Nāqati Fitnatan Lahum Fārtaqibhum Wa Aşţabir 054-027 Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
Wa Nabbi'hum 'Anna Al-Mā'a Qismatun Baynahum  ۖ  Kullu Shirbin Muĥtađarun 054-028 Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.  ۖ 
Fanādaw Şāĥibahum Fata`āţá Fa`aqara 054-029 Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
Fakayfa Kāna `Adhābī Wa Nudhuri 054-030 To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
'Innā 'Arsalnā `Alayhim Şayĥatan Wāĥidatan Fakānū Kahashīmi Al-Muĥtažiri 054-031 Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
Wa Laqad Yassarnā Al-Qur'āna Lildhdhikri Fahal Min Muddakirin 054-032 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Kadhdhabat Qawmu Lūţin Bin-Nudhuri 054-033 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
'Innā 'Arsalnā `Alayhim Ĥāşibāan 'Illā 'Āla Lūţin  ۖ  Najjaynāhum Bisaĥarin 054-034 Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.  ۖ 
Ni`matan Min `Indinā  ۚ  Kadhālika Najzī Man Shakara 054-035 Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.  ۚ 
Wa Laqad 'Andharahum Baţshatanā Fatamāraw Bin-Nudhuri 054-036 Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
Wa Laqad Rāwadūhu `An Đayfihi Faţamasnā 'A`yunahum Fadhūqū `Adhābī Wa Nudhuri 054-037 Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
Wa Laqad Şabbaĥahum Bukratan `Adhābun Mustaqirrun 054-038 Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
Fadhūqū `Adhābī Wa Nudhuri 054-039 To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
Wa Laqad Yassarnā Al-Qur'āna Lildhdhikri Fahal Min Muddakirin 054-040 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur,ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Wa Laqad Jā'a 'Āla Fir`awna An-Nudhuru 054-041 Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
Kadhdhabū Bi'āyātinā Kullihā Fa'akhadhnāhum 'Akhdha `Azīzin Muqtadirin 054-042 Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
'Akuffārukum Khayrun Min 'Ūla'ikum 'Am Lakum Barā'atun Az-Zuburi 054-043 Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
'Am Yaqūlūna Naĥnu Jamī`un Muntaşirun 054-044 Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
Sayuhzamu Al-Jam`u Wa Yuwallūna Ad-Dubura 054-045 Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
Bali As-Sā`atu Maw`iduhum Wa As-Sā`atu 'Ad/há Wa 'Amarru 054-046 Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
'Inna Al-Mujrimīna Fī Đalālin Wa Su`urin 054-047 Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
Yawma Yusĥabūna Fī An-Nāri `Alá Wujūhihim Dhūqū Massa Saqara 054-048 Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
'Innā Kulla Shay'in Khalaqnāhu Biqadarin 054-049 Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
Wa Mā 'Amrunā 'Illā Wāĥidatun Kalamĥin Bil-Başari 054-050 Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
Wa Laqad 'Ahlaknā 'Ashyā`akum Fahal Min Muddakirin 054-051 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
Wa Kullu Shay'in Fa`alūhu Fī Az-Zuburi 054-052 Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
Wa Kullu Şaghīrin Wa Kabīrin Mustaţarun 054-053 Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa Naharin 054-054 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
Fī Maq`adi Şidqin `Inda Malīkin Muqtadirin 054-055 A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
Next Sūrah