53) Sūrat An-Najm

Printed format

53)

Wa An-Najmi 'Idhā Hawá 053-001 Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
Mā Đalla Şāĥibukum Wa Mā Ghawá 053-002 Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
Wa Mā Yanţiqu `Ani Al-Hawá 053-003 Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
'In Huwa 'Illā Waĥyun Yūĥá 053-004 (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
`Allamahu Shadīdu Al-Quwá 053-005 (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
Dhū Mirratin Fāstawá 053-006 Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
Wa Huwa Bil-'Ufuqi Al-'A`lá 053-007 Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
Thumma Danā Fatadallá 053-008 Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
Fakāna Qāba Qawsayni 'Aw 'Adná 053-009 Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
Fa'awĥá 'Ilá `Abdihi Mā 'Awĥá 053-010 Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa ).
Mā Kadhaba Al-Fu'uādu Mā Ra'á 053-011 Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
'Afatumārūnahu `Alá Mā Yará 053-012 Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
Wa Laqad Ra'āhu Nazlatan 'Ukh 053-013 Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa .
`Inda Sidrati Al-Muntahá 053-014 A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
`Indahā Jannatu Al-Ma'wá 053-015 A inda taken, nan Aljannar makoma take.
'Idh Yaghshá As-Sidrata Mā Yaghshá 053-016 Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
Mā Zāgha Al-Başaru Wa Mā Ţaghá 053-017 Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
Laqad Ra'á Min 'Āyāti Rabbihi Al-Kub 053-018 Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
'Afara'aytumu Al-Lāta Wa Al-`Uzzá 053-019 Shin, kun ga Lãta da uzza?
Wa Manāata Ath-Thālithata Al-'Ukh 053-020 Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
'Alakumu Adh-Dhakaru Wa Lahu Al-'Unthá 053-021 Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
Tilka 'Idhāan Qismatun Đīzá 053-022 Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
'In Hiya 'Illā 'Asmā'un Sammaytumūhā 'Antum Wa 'Ābā'uukum Mā 'Anzala Al-Lahu Bihā Min Sulţānin  ۚ  'In Yattabi`ūna 'Illā Až-Žanna Wa Mā Tahwá Al-'Anfusu  ۖ  Wa Laqad Jā'ahum Min Rabbihimu Al-Hudá 053-023 Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).  ۚ   ۖ 
'Am Lil'insāni Mā Tamanná 053-024 Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
Falillāhi Al-'Ākhiratu Wa Al-'Ū 053-025 To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
Wa Kam Min Malakin As-Samāwāti Lā TughShafā`atuhum Shay'āan 'Illā Min Ba`di 'An Ya'dhana Al-Lahu Liman Yashā'u Wa Yarđá 053-026 Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
'Inna Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati Layusammūna Al-Malā'ikata Tasmiyata Al-'Unthá 053-027 Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.
Wa Mā Lahum Bihi Min `Ilmin  ۖ  'In Yattabi`ūna 'Illā Až-Žanna  ۖ  Wa 'Inna Až-Žanna Lā Yughnī Mina Al-Ĥaqqi Shay'āan 053-028 Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.  ۖ   ۖ 
Fa'a`riđ `An Man Tawallá `An Dhikrinā Wa Lam Yurid 'Illā Al-Ĥayāata Ad-Dun 053-029 Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
Dhālika Mablaghuhum Mina Al-`Ilmi  ۚ  'Inna Rabbaka Huwa 'A`lamu Biman Đalla `An Sabīlihi Wa Huwa 'A`lamu Bimani Ahtadá 053-030 Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.  ۚ 
Wa Lillahi Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Liyajziya Al-Ladhīna 'Asā'ū Bimā `Amilū Wa Yajziya Al-Ladhīna 'Aĥsanū Bil-Ĥusná 053-031 Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
Al-Ladhīna Yajtanibūna Kabā'ira Al-'Ithmi Wa Al-Fawāĥisha 'Illā Al-Lamama  ۚ  'Inna Rabbaka Wāsi`u Al-Maghfirati  ۚ  Huwa 'A`lamu Bikum 'Idh 'Ansha'akum Mina Al-'Arđi Wa 'Idh 'Antum 'Ajinnatun Fī Buţūni 'Ummahātikum  ۖ  Falā Tuzakkū 'Anfusakum  ۖ  Huwa 'A`lamu Bimani Attaqá 053-032 Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.  ۚ   ۚ   ۖ   ۖ 
'Afara'ayta Al-Ladhī Tawallá 053-033 Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?
Wa 'A`ţá Qalīlāan Wa 'Akdá 053-034 Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?
'A`indahu `Ilmu Al-Ghaybi Fahuwa Yará 053-035 Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
'Am Lam Yunabba' Bimā Fī Şuĥufi Mūsá 053-036 Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
Wa 'Ibrāhīma Al-Ladhī Wa Ffá 053-037 Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?
'Allā Taziru Wāziratun Wizra 'Ukh 053-038 Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
Wa 'An Laysa Lil'insāni 'Illā Mā Sa`á 053-039 Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.
Wa 'Anna Sa`yahu Sawfa Yurá 053-040 Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.
Thumma Yujzāhu Al-Jazā'a Al-'Awfá 053-041 Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
Wa 'Anna 'Ilá Rabbika Al-Muntahá 053-042 Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?
Wa 'Annahu Huwa 'Ađĥaka Wa 'Ab 053-043 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
Wa 'Annahu Huwa 'Amāta Wa 'Aĥyā 053-044 Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
Wa 'Annahu Khalaqa Az-Zawjayni Adh-Dhakara Wa Al-'Unthá 053-045 Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
Min Nuţfatin 'Idhā Tumná 053-046 Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
Wa 'Anna `Alayhi An-Nash'ata Al-'Ukh 053-047 Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
Wa 'Annahu Huwa 'Aghná Wa 'Aqná 053-048 Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
Wa 'Annahu Huwa Rabbu Ash-Shi`rá 053-049 Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira .
Wa 'Annahu 'Ahlaka `Ādāan Al-'Ū 053-050 Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko. ~
Wa Thamūda Famā 'Ab 053-051 Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
Wa Qawma Nūĥin Min Qablu  ۖ  'Innahum Kānū Hum 'Ažlama Wa 'Aţghá 053-052 Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.  ۖ 
Wa Al-Mu'utafikata 'Ahwá 053-053 Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
Faghashshāhā Mā Ghashshá 053-054 Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
Fabi'ayyi 'Ālā'i Rabbika Tatamārá 053-055 To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
dhā Nadhīrun Mina An-Nudhuri Al-'Ū 053-056 wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
'Azifati Al-'Āzifahu 053-057 Makusanciya fa, tã yi kusa.
Laysa Lahā Min Dūni Al-Lahi Kāshifahun 053-058 Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
'Afamin Hādhā Al-Ĥadīthi Ta`jabūna 053-059 Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
Wa Tađĥakūna Wa Lā Tabkūna 053-060 Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
Wa 'Antum Sāmidūna 053-061 Alhãli kunã mãsu wãsã?
Fāsjudū Lillahi Wa A`budū 053-062 To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).
Next Sūrah