52) Sūrat Aţ-Ţūr

Printed format

52)

Wa Aţūri 052-001 Inã rantsuwa da ũr (Dũtsen Mũsã).
Wa Kitābin Masţūrin 052-002 Da wani littãfi rubũtacce.
Fī Raqqin Manshūrin 052-003 A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.
Wa Al-Bayti Al-Ma`mūri 052-004 Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).
Wa As-Saqfi Al-Marfū`i 052-005 Da rufin nan da aka ɗaukaka.
Wa Al-Baĥri Al-Masjūri 052-006 Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).
'Inna `Adhāba Rabbika Lawāqi`un 052-007 Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.
Mā Lahu Min Dāfi`in 052-008 Bã ta da mai tunkuɗẽwa.
Yawma Tamūru As-Samā'u Mawrāan 052-009 Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.
Wa Tasīru Al-Jibālu Sayrāan 052-010 Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.
Fawaylun Yawma'idhin Lilmukadhdhibīna 052-011 To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
Al-Ladhīna HumKhawđin Yal`abūna 052-012 Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.
Yawma Yuda``ūna 'Ilá Nāri Jahannama Da``āan 052-013 Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.
Hadhihi An-Nāru Allatī Kuntum Bihā Tukadhdhibūna 052-014 (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
'Afasiĥrun Hādhā 'Am 'Antum Lā Tubşirūna 052-015 "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"
Aşlawhā Fāşbirū 'Aw Lā Taşbirū Sawā'un `Alaykum  ۖ  'Innamā Tujzawna Mā Kuntum Ta`malūna 052-016 "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."  ۖ 
'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa Na`īmin 052-017 Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.
Fākihīna Bimā 'Ātāhum Rabbuhum Wa Waqāhum Rabbuhum `Adhāba Al-Jaĥīmi 052-018 Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.
Kulū Wa Ashrabū Hanī'āan Bimā Kuntum Ta`malūna 052-019 (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
Muttaki'īna `Alá Sururin Maşfūfatin  ۖ  Wa Zawwajnāhum Biĥūrin `Īnin 052-020 Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.  ۖ 
Wa Al-Ladhīna 'Āmanū Wa Attaba`at/hum Dhurrīyatuhum Bi'īmānin 'Alĥaqnā Bihim Dhurrīyatahum Wa Mā 'Alatnāhum Min `Amalihim Min  ۚ  Shay'in Kullu Amri'in Bimā Kasaba Rahīnun 052-021 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.  ۚ 
Wa 'Amdadnāhum Bifākihatin Wa Laĥmin Mimmā Yashtahūna 052-022 Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.
Yatanāza`ūna Fīhā Ka'sāan Lā Laghwun Fīhā Wa Lā Ta'thīmun 052-023 Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.
Wa Yaţūfu `Alayhim Ghilmānun Lahum Ka'annahum Lu'ulu'uun Maknūnun 052-024 Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.
Wa 'Aqbala Ba`đuhum `Alá Ba`đin Yatasā'alūna 052-025 Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.
Qālū 'Innā Kunnā Qablu Fī 'Ahlinā Mushfiqīna 052-026 Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya ) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."
Famanna Al-Lahu `Alaynā Wa Waqānā `Adhāba As-Samūmi 052-027 "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."
'Innā Kunnā Min Qablu Nad`ūhu  ۖ  'Innahu Huwa Al-Barru Ar-Raĥīmu 052-028 "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama." ~  ۖ 
Fadhakkir Famā 'Anta Bini`mati Rabbika Bikāhinin Wa Lā Majnūnin 052-029 To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.
'Am Yaqūlūna Shā`irun Natarabbaşu Bihi Rayba Al-Manūni 052-030 Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?
Qul Tarabbaşū Fa'innī Ma`akum Mina Al-Mutarabbişīna 052-031 Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."
'Am Ta'muruhum 'Aĥlāmuhum Bihadhā  ۚ  'Am Hum Qawmun Ţāghūna 052-032 Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?  ۚ 
'Am Yaqūlūna Taqawwalahu  ۚ  Bal Lā Yu'uminūna 052-033 Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.  ۚ 
Falya'tū Biĥadīthin Mithlihi 'In Kānū Şādiqīna 052-034 Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne. ~
'Am Khuliqū Min Ghayri Shay'in 'Am Humu Al-Khāliqūna 052-035 Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?
'Am Khalaqū As-Samāwāti Wa Al-'Arđa  ۚ  Bal Lā Yūqinūna 052-036 Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.  ۚ 
'Am `Indahum Khazā'inu Rabbika 'Am Humu Al-Musayţirūna 052-037 Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?
'Am Lahum Sullamun Yastami`ūna Fīhi  ۖ  Falya'ti Mustami`uhum Bisulţānin Mubīnin 052-038 Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.  ۖ 
'Am Lahu Al-Banātu Wa Lakumu Al-Banūna 052-039 Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?
'Am Tas'aluhum 'Ajrāan Fahum Min Maghramin Muthqalūna 052-040 Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?
'Am `Indahumu Al-Ghaybu Fahum Yaktubūna 052-041 Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?
'Am Yurīdūna Kaydāan  ۖ  Fa-Al-Ladhīna Kafarū Humu Al-Makīdūna 052-042 Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.  ۖ 
'Am Lahum 'Ilahun Ghayru Al-Lahi  ۚ  Subĥāna Al-Lahi `Ammā Yushrikūna 052-043 Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!  ۚ 
Wa 'In Yaraw Kisfāan Mina As-Samā'i Sāqiţāan Yaqūlū Saĥābun Markūmun 052-044 Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.
Fadharhum Ĥattá Yulāqū Yawmahumu Al-Ladhī Fīhi Yuş`aqūna 052-045 To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.
Yawma Lā Yughnī `Anhum Kayduhum Shay'āan Wa Lā Hum Yunşarūna 052-046 Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.
Wa 'Inna Lilladhīna Žalamū `Adhābāan Dūna Dhālika Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna 052-047 Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.
Wa Aşbir Liĥukmi Rabbika Fa'innaka Bi'a`yuninā  ۖ  Wa Sabbiĥ Biĥamdi Rabbika Ĥīna Taqūmu 052-048 Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).  ۖ 
Wa Mina Al-Layli Fasabbiĥhu Wa 'Idbāra An-Nujūmi 052-049 Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri.
Next Sūrah