51) Sūrat Adh-Dhāriyāt

Printed format

51)

Wa Adh-Dhāriyāti Dharwan 051-001 Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
Fālĥāmilāti Wiqan 051-002 Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
Fāljāriyāti Yusrāan 051-003 Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
Fālmuqassimāti 'Aman 051-004 Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
'Innamā Tū`adūna Laşādiqun 051-005 Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
Wa 'Inna Ad-Dīna Lawāqi`un 051-006 Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
Wa As-Samā'i Dhāti Al-Ĥubuki 051-007 Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi ( na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
'Innakum Lafī Qawlin Mukhtalifin 051-008 Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
Yu'ufaku `Anhu Man 'Ufika 051-009 Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
Qutila Al-Kharrāşūna 051-010 An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.
Al-Ladhīna HumGhamratin Sāhūna 051-011 Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
Yas'alūna 'Ayyāna Yawmu Ad-Dīni 051-012 Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
Yawma Hum `Alá An-Nāri Yuftanūna 051-013 Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
Dhūqū Fitnatakumdhā Al-Ladhī Kuntum Bihi Tasta`jilūna 051-014 (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
'Inna Al-Muttaqīna Fī Jannātin Wa `Uyūnin 051-015 Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
'Ākhidhīna Mā 'Ātāhum Rabbuhum  ۚ  'Innahum Kānū Qabla Dhālika Muĥsinīna 051-016 Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).  ۚ 
Kānū Qalīlāan Mina Al-Layli Mā Yahja`ūna 051-017 Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
Wa Bil-'Asĥāri Hum Yastaghfirūna 051-018 Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
Wa Fī 'Amwālihim Ĥaqqun Lilssā'ili Wa Al-Maĥrūmi 051-019 Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
Wa Fī Al-'Arđi 'Āyātun Lilmūqinīna 051-020 Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
Wa Fī 'Anfusikum  ۚ  'Afalā Tubşirūna 051-021 Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?  ۚ 
Wa Fī As-Samā'i Rizqukum Wa Mā Tū`adūna 051-022 Kuma a cikin sama arzikinku ( yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
Fawarabbi As-Samā'i Wa Al-'Arđi 'Innahu Laĥaqqun Mithla Mā 'Annakum Tanţiqūna 051-023 To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
Hal 'Atāka Ĥadīthu Đayfi 'Ibrāhīma Al-Mukramīna 051-024 Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
'Idh Dakhalū `Alayhi Faqālū Salāmāan  ۖ  Qāla Salāmun Qawmun Munkarūna 051-025 A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"  ۖ 
Farāgha 'Ilá 'Ahlihi Fajā'a Bi`ijlin Samīnin 051-026 Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
Faqarrabahu 'Ilayhim Qāla 'Alā Ta'kulūna 051-027 Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" ~
Fa'awjasa Minhum Khīfatan  ۖ  Qālū Lā Takhaf  ۖ  Wa Bashsharūhu Bighulāmin `Alīmin 051-028 Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.  ۖ   ۖ 
Fa'aqbalati Amra'atuhu Fī Şarratin Faşakkat Wajhahā Wa Qālat `Ajūzun `Aqīmun 051-029 Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
Qālū Kadhāliki Qāla Rabbuki  ۖ  'Innahu Huwa Al-Ĥakīmu Al-`Alīmu 051-030 Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."  ۖ 
Qāla Famā Khaţbukum 'Ayyuhā Al-Mursalūna 051-031 (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
Qālū 'Innā 'Ursilnā 'Ilá Qawmin Mujrimīna 051-032 Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
Linursila `Alayhim Ĥijāratan Min Ţīnin 051-033 "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu ( bom).
Musawwamatan `Inda Rabbika Lilmusrifīna 051-034 "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
Fa'akhrajnā Man Kāna Fīhā Mina Al-Mu'uminīna 051-035 Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
Famā Wajadnā Fīhā Ghayra Baytin Mina Al-Muslimīna 051-036 Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
Wa Taraknā Fīhā 'Āyatan Lilladhīna Yakhāfūna Al-`Adhāba Al-'Alīma 051-037 Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
Wa Fī Mūsá 'Idh 'Arsalnāhu 'Ilá Fir`awna Bisulţānin Mubīnin 051-038 Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. ~
Fatawallá Biruknihi Wa Qāla Sāĥirun 'Aw Majnūnun 051-039 Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci !"
Fa'akhadhnāhu Wa Junūdahu Fanabadhnāhum Al-Yammi Wa Huwa Mulīmun 051-040 Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
Wa Fī `Ādin 'Idh 'Arsalnā `Alayhimu Ar-Rīĥa Al-`Aqīma 051-041 Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
Mā Tadharu Min Shay'in 'Atat `Alayhi 'Illā Ja`alat/hu Kālrramīmi 051-042 Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
Wa Fī Thamūda 'Idh Qīla Lahum Tamatta`ū Ĥattá Ĥīnin 051-043 Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
Fa`ataw `An 'Amri Rabbihim Fa'akhadhat/humu Aş-Şā`iqatu Wa Hum Yanžurūna 051-044 Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
Famā Astaţā`ū Min Qiyāmin Wa Mā Kānū Muntaşirīna 051-045 Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
Wa Qawma Nūĥin Min Qablu  ۖ  'Innahum Kānū Qawmāan Fāsiqīna 051-046 Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.  ۖ 
Wa As-Samā'a Banaynāhā Bi'ayydin Wa 'Innā Lamūsi`ūna 051-047 Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
Wa Al-'Arđa Farashnāhā Fani`ma Al-Māhidūna 051-048 Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
Wa Min Kulli Shay'in Khalaqnā Zawjayni La`allakum Tadhakkarūna 051-049 Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
Fafirrū 'Ilá Al-Lahi  ۖ  'Innī Lakum Minhu Nadhīrun Mubīnun 051-050 Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.  ۖ 
Wa Lā Taj`alū Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara  ۖ  'Innī Lakum Minhu Nadhīrun Mubīnun 051-051 Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.  ۖ 
Kadhālika Mā 'Atá Al-Ladhīna Min Qablihim Min Rasūlin 'Illā Qālū Sāĥirun 'Aw Majnūnun 051-052 Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
'Atawāşaw Bihi  ۚ  Bal Hum Qawmun Ţāghūna 051-053 shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.  ۚ 
Fatawalla `Anhum Famā 'Anta Bimalūmin 051-054 Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
Wa Dhakkir Fa'inna Adh-Dhikrá Tanfa`u Al-Mu'uminīna 051-055 Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
Wa Mā Khalaqtu Al-Jinna Wa Al-'Insa 'Illā Liya`budūni 051-056 Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
Mā 'Urīdu Minhum Min Rizqin Wa Mā 'Urīdu 'An Yuţ`imūni 051-057 Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
'Inna Al-Laha Huwa Ar-Razzāqu Dhū Al-Qūwati Al-Matīnu 051-058 Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
Fa'inna Lilladhīna Žalamū Dhanūbāan Mithla Dhanūbi 'Aşĥābihim Falā Yasta`jilūni 051-059 To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
Fawaylun Lilladhīna Kafarū Min Yawmihimu Al-Ladhī Yū`adūna 051-060 Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
Next Sūrah