50) Sūrat Qāf

Printed format

50)

Qāf Wa Al-Qur'āni Al-Majīdi 050-001 ¡̃ . Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
Bal `Ajibū 'An Jā'ahum Mundhirun Minhum Faqāla Al-Kāfirūna Hādhā Shay'un `Ajībun 050-002 Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
'A'idhā Mitnā Wa Kunnā Turābāan  ۖ  Dhālika Raj`un Ba`īdun 050-003 "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."  ۖ 
Qad `Alimnā Mā Tanquşu Al-'Arđu Minhum  ۖ  Wa `Indanā Kitābun Ĥafīžun 050-004 Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.  ۖ 
Bal Kadhdhabū Bil-Ĥaqqi Lammā Jā'ahum Fahum Fī 'Amrin Marījin 050-005 Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
'Afalam Yanžurū 'Ilá As-Samā'i Fawqahum Kayfa Banaynāhā Wa Zayyannāhā Wa Mā Lahā Min Furūjin 050-006 Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
Wa Al-'Arđa Madadnāhā Wa 'Alqaynā Fīhā Rawāsiya Wa 'Anbatnā Fīhā Min Kulli Zawjin Bahījin 050-007 Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
Tabşiratan Wa Dhikrá Likulli `Abdin Munībin 050-008 Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
Wa Nazzalnā Mina As-Samā'i Mā'an Mubārakāan Fa'anbatnā Bihi Jannātin Wa Ĥabba Al-Ĥaşīdi 050-009 Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
Wa An-Nakhla Bāsiqātin Lahā Ţal`un Nađīdun 050-010 Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
Rizqāan Lil`ibādi  ۖ  Wa 'Aĥyaynā Bihi Baldatan Maytāan  ۚ  Kadhālika Al-Khurūju 050-011 Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.  ۖ   ۚ 
Kadhdhabat Qablahum Qawmu Nūĥin Wa 'Aşĥābu Ar-Rassi Wa Thamūdu 050-012 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa.
Wa `Ādun Wa Fir`awnu Wa 'Ikhwānu Lūţin 050-013 Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
Wa 'Aşĥābu Al-'Aykati Wa Qawmu Tubba`in  ۚ  Kullun Kadhdhaba Ar-Rusula Faĥaqqa Wa`īdi 050-014 Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.  ۚ 
'Afa`ayīnā Bil-Khalqi Al-'Awwali  ۚ  Bal Hum Fī Labsin Min Khalqin Jadīdin 050-015 Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.  ۚ 
Wa Laqad Khalaq Al-'Insāna Wa Na`lamu Mā Tuwaswisu Bihi Nafsuhu  ۖ  Wa Naĥnu 'Aqrabu 'Ilayhi Min Ĥabli Al-Warīdi 050-016 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.  ۖ 
'Idh Yatalaqqá Al-Mutalaqqiyāni `Ani Al-Yamīni Wa `Ani Ash-Shimāli Qa`īdun 050-017 A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
Mā Yalfižu Min Qawlin 'Illā Ladayhi Raqībun `Atīdun 050-018 Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
Wa Jā'at Sakratu Al-Mawti Bil-Ĥaqqi  ۖ  Dhālika Mā Kunta Minhu Taĥīdu 050-019 Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.  ۖ 
Wa Nufikha Fī Aş-Şūri  ۚ  Dhālika Yawmu Al-Wa`īdi 050-020 Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.  ۚ 
Wa Jā'at Kullu Nafsin Ma`ahā Sā'iqun Wa Shahīdun 050-021 Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
Laqad Kunta Fī Ghaflatin Min Hādhā Fakashafnā `Anka Ghā'aka Fabaşaruka Al-Yawma Ĥadīdun 050-022 (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
Wa Qāla Qarīnuhu Hādhā Mā Ladayya `Atīdun 050-023 Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
'Alqiyā Fī Jahannama Kulla Kaffārin `Anīdin 050-024 (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
Mannā`in Lilkhayri Mu`tadin Murībin 050-025 "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
Al-Ladhī Ja`ala Ma`a Al-Lahi 'Ilahāan 'Ākhara Fa'alqiyāhu Fī Al-`Adhābi Ash-Shadīdi 050-026 "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
Qāla Qarīnuhu Rabbanā Mā 'Aţghaytuhu Wa Lakin Kāna Fī Đalālin Ba`īdin 050-027 Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
Qāla Lā Takhtaşimū Ladayya Wa Qad Qaddamtu 'Ilaykum Bil-Wa`īdi 050-028 Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
Mā Yubaddalu Al-Qawlu Ladayya Wa Mā 'Anā Bižallāmin Lil`abīdi 050-029 "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."
Yawma Naqūlu Lijahannama Hal Amtala'ti Wa Taqūlu Hal Min Mazīdin 050-030 Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?"
Wa 'Uzlifati Al-Jannatu Lilmuttaqīna Ghayra Ba`īdin 050-031 Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
dhā Mā Tū`adūna Likulli 'Awwābin Ĥafīžin 050-032 "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
Man Khashiya Ar-Raĥmana Bil-Ghaybi Wa Jā'a Biqalbin Munībin 050-033 "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
Adkhulūhā Bisalāmin  ۖ  Dhālika Yawmu Al-Khulūdi 050-034 (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama."  ۖ 
Lahum Mā Yashā'ūna Fīhā Wa Ladaynā Mazīdun 050-035 Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
Wa Kam 'Ahlaknā Qablahum Min Qarnin Hum 'Ashaddu Minhum Baţshāan Fanaqqabū Fī Al-Bilādi Hal Min Maĥīşin 050-036 Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? ( Babu).
'Inna Fī Dhālika Ladhikrá Liman Kāna Lahu Qalbun 'Aw 'Alqá As-Sam`a Wa Huwa Shahīdun 050-037 Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
Wa Laqad Khalaq As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā Fī Sittati 'Ayyāmin Wa Mā Massanā Min Lughūbin 050-038 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
Fāşbir `Alá Mā Yaqūlūna Wa Sabbiĥ Biĥamdi Rabbika Qabla Ţulū`i Ash-Shamsi Wa Qabla Al-Ghurūbi 050-039 Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
Wa Mina Al-Layli Fasabbiĥhu Wa 'Adbāra As-Sujūdi 050-040 Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
Wa Astami` Yawma Yunādi Al-Munādi Min Makānin Qarībin 050-041 Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
Yawma Yasma`ūna Aş-Şayĥata Bil-Ĥaqqi  ۚ  Dhālika Yawmu Al-Khurūji 050-042 Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).  ۚ 
'Innā Naĥnu Nuĥyī Wa Numītu Wa 'Ilaynā Al-Maşīru 050-043 Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
Yawma Tashaqqaqu Al-'Arđu `Anhum Sirā`āan  ۚ  Dhālika Ĥashrun `Alaynā Yasīrun 050-044 Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.  ۚ 
Naĥnu 'A`lamu Bimā Yaqūlūna  ۖ  Wa Mā 'Anta `Alayhim Bijabbārin  ۖ  Fadhakkir Bil-Qur'āni Man Yakhāfu Wa`īdi 050-045 Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.  ۖ   ۖ 
Next Sūrah