49) Sūrat Al-Ĥujurāt

Printed format

49)

Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tuqaddimū Bayna Yadayi Al-Lahi Wa Rasūlihi Wa Attaqū Al-Laha 'Inna Al-Laha Samī`un `Alīmun 049-001 Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Tarfa`ū 'Aşwātakum Fawqa Şawti An-Nabīyi Wa Lā Tajharū Lahu Bil-Qawli Kajahri Ba`đikum Liba`đin 'An Taĥbaţa 'A`mālukum Wa 'Antum Lā Tash`urūna 049-002 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.
'Inna Al-Ladhīna Yaghuđđūna 'Aşwātahum `Inda Rasūli Al-Lahi 'Ūlā'ika Al-Ladhīna Amtaĥana Al-Lahu Qulūbahum Lilttaqwá  ۚ  Lahum Maghfiratun Wa 'Ajrun `Ažīmun 049-003 Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.  ۚ 
'Inna Al-Ladhīna Yunādūnaka Min Warā'i Al-Ĥujurāti 'Aktharuhum Lā Ya`qilūna 049-004 Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali.
Wa Law 'Annahum Şabarū Ĥattá Takhruja 'Ilayhim Lakāna Khayrāan Lahum Wa  ۚ  Allāhu Ghafūrun Raĥīmun 049-005 Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū 'In Jā'akum Fāsiqun Binaba'iin Fatabayyanū 'An Tuşībū Qawmāan Bijahālatin Fatuşbiĥū `Alá Mā Fa`altum Nādimīna 049-006 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
Wa A`lamū 'Anna Fīkum Rasūla Al-Lahi  ۚ  Law Yuţī`ukum Fī Kathīrin Mina Al-'Amri La`anittum Wa Lakinna Al-Laha Ĥabbaba 'Ilaykumu Al-'Īmāna Wa Zayyanahu Fī Qulūbikum Wa Karraha 'Ilaykumu Al-Kufra Wa Al-Fusūqa Wa Al-`Işyāna  ۚ  'Ūlā'ika Humu Ar-Rāshidūna 049-007 Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu.  ۚ  ~  ۚ 
Fađlāan Mina Al-Lahi Wa Ni`matan Wa  ۚ  Allāhu `Alīmun Ĥakīmun 049-008 Bisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.  ۚ 
Wa 'In Ţā'ifatāni Mina Al-Mu'uminīna Aqtatalū Fa'aşliĥū Baynahumā  ۖ  Fa'in Baghat 'Iĥdāhumā `Alá Al-'Ukhrá Faqātilū Allatī Tabghī Ĥattá Tafī'a 'Ilá 'Amri Al-Lahi  ۚ  Fa'in Fā'at Fa'aşliĥū Baynahumā Bil-`Adli Wa 'Aqsiţū  ۖ  'Inna Al-Laha Yuĥibbu Al-Muqsiţīna 049-009 Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.  ۖ   ۚ   ۖ 
'Innamā Al-Mu'uminūna 'Ikhwatun Fa'aşliĥū Bayna 'Akhawaykum  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha La`allakum Turĥamūna 049-010 Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama.  ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Lā Yaskhar Qawmun Min Qawmin `Asá 'An Yakūnū Khayrāan Minhum Wa Lā Nisā'un Min Nisā'in `Asá 'An Yakunna Khayrāan Minhunna  ۖ  Wa Lā Talmizū 'Anfusakum Wa Lā Tanābazū Bil-'Alqābi  ۖ  Bi'sa Al-Aismu Al-Fusūqu Ba`da Al-'Īmāni  ۚ  Wa Man Lam Yatub Fa'ūlā'ika Humu Až-Žālimūna 049-011 "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ.Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."  ۖ   ۖ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā Al-Ladhīna 'Āmanū Ajtanibū Kathīrāan Mina Až-Žanni 'Inna Ba`đa Až-Žanni 'Ithmun  ۖ  Wa Lā Tajassasū Wa Lā Yaghtab Ba`đukum Ba`đāan  ۚ  'Ayuĥibbu 'Aĥadukum 'An Ya'kula Laĥma 'Akhīhi Maytāan Fakarihtumūhu  ۚ  Wa Attaqū Al-Laha  ۚ  'Inna Al-Laha Tawwābun Raĥīmun 049-012 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.  ۖ   ۚ   ۚ   ۚ 
Yā 'Ayyuhā An-Nāsu 'Innā Khalaqnākum Min Dhakarin Wa 'Unthá Wa Ja`alnākum Shu`ūbāan Wa Qabā'ila Lita`ārafū  ۚ  'Inna 'Akramakum `Inda Al-Lahi 'Atqākum  ۚ  'Inna Al-Laha `Alīmun Khabīrun 049-013 Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.  ۚ   ۚ 
Qālati Al-'A`rābu 'Āmannā  ۖ  Qul Lam Tu'uminū Wa Lakin Qūlū 'Aslamnā Wa Lammā Yadkhuli Al-'Īmānu Fī Qulūbikum  ۖ  Wa 'In Tuţī`ū Al-Laha Wa Rasūlahu Lā Yalitkum Min 'A`mālikum Shay'āan  ۚ  'Inna Al-Laha Ghafūrun Raĥīmun 049-014 ¡auyãwa suka ce: "Mun yi ĩmãni." Ka ce: "Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."  ۖ   ۖ   ۚ 
'Innamā Al-Mu'uminūna Al-Ladhīna 'Āmanū Bil-Lahi Wa Rasūlihi Thumma Lam Yartābū Wa Jāhadū Bi'amwālihim Wa 'Anfusihim Fī Sabīli Al-Lahi  ۚ  'Ūlā'ika Humu Aş-Şādiqūna 049-015 Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.  ۚ 
Qul 'Atu`allimūna Al-Laha Bidīnikum Wa Allāhu Ya`lamu Mā Fī As-Samāwāti Wa Mā Fī Al-'Arđi Wa  ۚ  Allāhu Bikulli Shay'in `Alīmun 049-016 Ka ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme?"  ۚ 
Yamunnūna `Alayka 'An 'Aslamū  ۖ  Qul Lā Tamunnū `Alayya 'Islāmakum  ۖ  Bali Al-Lahu Yamunnu `Alaykum 'An Hadākum Lil'īmāni 'In Kuntum Şādiqīna 049-017 Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya."  ۖ   ۖ 
'Inna Al-Laha Ya`lamu Ghayba As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۚ  Allāhu Başīrun Bimā Ta`malūna 049-018 "Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da ¡asa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."  ۚ 
Next Sūrah