Ĥā-Mīm | َ043-001 Ḥ. M̃. | حَا-مِيم |
Wa Al-Kitābi Al-Mubīni | َ043-002 Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani. | وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ |
'Innā Ja`alnāhu Qur'ānāan `Arabīyāan La`allakum Ta`qilūna | َ043-003 Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta. | إِنَّا جَعَلْنَاه ُُ قُرْآناً عَرَبِيّا ً لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ |
Wa 'Innahu Fī 'Ummi Al-Kitābi Ladaynā La`alīyun Ĥakīmun | َ043-004 Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne. | وَإِنَّه ُُ فِي أُمِّ الْكِتَابِ لَدَيْنَا لَعَلِيٌّ حَكِيم ٌ |
'Afanađribu `Ankumu Adh-Dhikra Şafĥāan 'An Kuntum Qawmāan Musrifīna | َ043-005 Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna? | أَفَنَضْرِبُ عَنكُمُ الذِّكْرَ صَفْحاً أَنْ كُنتُمْ قَوْما ً مُسْرِفِينَ |
Wa Kam 'Arsalnā Min Nabīyin Fī Al-'Awwalīna | َ043-006 Alhãli kuwa sau nawa Muka aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko! | وَكَمْ أَرْسَلْنَا مِنْ نَبِيّ ٍ فِي الأَوَّلِينَ |
Wa Mā Ya'tīhim Min Nabīyin 'Illā Kānū Bihi Yastahzi'ūn | َ043-007 Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili. | وَمَا يَأْتِيهِمْ مِنْ نَبِيّ ٍ إِلاَّ كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون |
Fa'ahlaknā 'Ashadda Minhum Baţshāan Wa Mađá Mathalu Al-'Awwalīna | َ043-008 Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe. | فَأَهْلَكْنَا أَشَدَّ مِنْهُمْ بَطْشا ً وَمَضَى مَثَلُ الأَوَّلِينَ |
Wa La'in Sa'altahum Man Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Layaqūlunna Khalaqahunna Al-`Azīzu Al-`Alīmu | َ043-009 Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su." | وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ الْعَزِيزُ الْعَلِيمُ |
Al-Ladhī Ja`ala Lakumu Al-'Arđa Mahdāan Wa Ja`ala Lakum Fīhā Subulāan La`allakum Tahtadūna | َ043-010 Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.' | الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ مَهْدا ً وَجَعَلَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلا ً لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ |
Wa Al-Ladhī Nazzala Mina As-Samā'i Mā'an Biqadarin Fa'ansharnā Bihi Baldatan ۚ Maytāan Kadhālika Tukhrajūna | َ043-011 Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari). | وَالَّذِي نَزَّلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً بِقَدَر ٍ فَأَنشَرْنَا بِه ِِ بَلْدَة ً مَيْتا ً ۚ كَذَلِكَ تُخْرَجُونَ |
Wa Al-Ladhī Khalaqa Al-'Azwāja Kullahā Wa Ja`ala Lakum Mina Al-Fulki Wa Al-'An`ām Mā Tarkabūna | َ043-012 Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa. | وَالَّذِي خَلَقَ الأَزْوَاجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُمْ مِنَ الْفُلْكِ وَالأَنعَام مَا تَرْكَبُونَ |
Litastawū `Alá Žuhūrihi Thumma Tadhkurū Ni`mata Rabbikum 'Idhā Astawaytum `Alayhi Wa Taqūlū Subĥāna Al-Ladhī Sakhkhara Lanā Hādhā Wa Mā Kunnā Lahu Muqrinīna | َ043-013 Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. | لِتَسْتَوُوا عَلَى ظُهُورِه ِِ ثُمَّ تَذْكُرُوا نِعْمَةَ رَبِّكُمْ إِذَا اسْتَوَيْتُمْ عَلَيْهِ وَتَقُولُوا سُبْحانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَذَا وَمَا كُنَّا لَه ُُ مُقْرِنِينَ |
Wa 'Innā 'Ilá Rabbinā Lamunqalibūna | َ043-014 "Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu." | وَإِنَّا إِلَى رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ |
Wa Ja`alū Lahu Min `Ibādihi Juz'āan ۚ 'Inna Al-'Insāna Lakafūrun Mubīnun | َ043-015 Kuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin. | وَجَعَلُوا لَه ُُ مِنْ عِبَادِه ِِ جُزْءا ً ۚ إِنَّ الإِنسَانَ لَكَفُور ٌ مُبِين ٌ |
'Am Attakhadha Mimmā Yakhluqu Banātin Wa 'Aşfākum Bil-Banīna | َ043-016 Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza? | أَمْ اتَّخَذَ مِمَّا يَخْلُقُ بَنَات ٍ وَأَصْفَاكُمْ بِالْبَنِينَ |
Wa 'Idhā Bushshira 'Aĥaduhum Bimā Đaraba Lilrraĥmani Mathalāan Žalla Wajhuhu Muswaddāan Wa Huwa Kažīmun | َ043-017 Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki. | وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُمْ بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحْمَنِ مَثَلا ً ظَلَّ وَجْهُه ُُ مُسْوَدّا ً وَهُوَ كَظِيم ٌ |
'Awaman Yunashsha'u Fī Al-Ĥilyati Wa Huwa Fī Al-Khişāmi Ghayru Mubīnin | َ043-018 Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba? | أَوَمَنْ يُنَشَّأُ فِي الْحِلْيَةِ وَهُوَ فِي الْخِصَامِ غَيْرُ مُبِين ٍ |
Wa Ja`alū Al-Malā'ikata Al-Ladhīna Hum `Ibādu Ar-Raĥmāni 'Ināthāan ۚ 'Ashahidū Khalqahum ۚ Satuktabu Shahādatuhum Wa Yus'alūna | َ043-019 Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su. | وَجَعَلُوا الْمَلاَئِكَةَ الَّذِينَ هُمْ عِبَادُ الرَّحْمَنِ إِنَاثاً ۚ أَشَهِدُوا خَلْقَهُمْ ۚ سَتُكْتَبُ شَهَادَتُهُمْ وَيُسْأَلُونَ |
Wa Qālū Law Shā'a Ar-Raĥmānu Mā `Abadnāhum ۗ Mā Lahum Bidhālika Min `Ilmin ۖ 'In Hum 'Illā Yakhruşūna | َ043-020 Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi. | وَقَالُوا لَوْ شَاءَ الرَّحْمَنُ مَا عَبَدْنَاهُمْ ۗ مَا لَهُمْ بِذَلِكَ مِنْ عِلْم ٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلاَّ يَخْرُصُونَ |
'Am 'Ātaynāhum Kitābāan Min Qablihi Fahum Bihi Mustamsikūna | َ043-021 Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe? | أَمْ آتَيْنَاهُمْ كِتَابا ً مِنْ قَبْلِه ِِ فَهُمْ بِه ِِ مُسْتَمْسِكُونَ |
Bal Qālū 'Innā Wajadnā 'Ābā'anā `Alá 'Ummatin Wa 'Innā `Alá 'Āthārihim Muhtadūna | َ043-022 Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa." | بَلْ قَالُوا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَى أُمَّة ٍ وَإِنَّا عَلَى آثَارِهِمْ مُهْتَدُونَ |
Wa Kadhalika Mā 'Arsalnā Min Qablika Fī Qaryatin Min Nadhīrin 'Illā Qāla Mutrafūhā 'Innā Wajadnā 'Ābā'anā `Alá 'Ummatin Wa 'Innā `Alá 'Āthārihim Muqtadūna | َ043-023 Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu." | وَكَذَلِكَ مَا أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ فِي قَرْيَة ٍ مِنْ نَذِير ٍ إِلاَّ قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَى أُمَّة ٍ وَإِنَّا عَلَى آثَارِهِمْ مُقْتَدُونَ |
Qāla 'Awalaw Ji'tukum Bi'ahdá Mimmā Wajadtum `Alayhi 'Ābā'akum ۖ Qālū 'Innā Bimā 'Ursiltum Bihi Kāfirūna | َ043-024 (Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi." | قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكُمْ بِأَهْدَى مِمَّا وَجَدْتُمْ عَلَيْهِ آبَاءَكُمْ ۖ قَالُوا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُمْ بِه ِِ كَافِرُونَ |
Fāntaqamnā Minhum ۖ Fānžur Kayfa Kāna `Āqibatu Al-Mukadhdhibīna | َ043-025 Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take. | فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ ۖ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذِّبِينَ |
Wa 'Idh Qāla 'Ibrāhīmu Li'abīhi Wa Qawmihi 'Innanī Barā'un Mimmā Ta`budūna | َ043-026 Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa." | وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيه ِِ وَقَوْمِهِ~ِ إِنَّنِي بَرَاء ٌ مِمَّا تَعْبُدُونَ |
'Illā Al-Ladhī Faţaranī Fa'innahu Sayahdīni | َ043-027 "Fãce wannan da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni." | إِلاَّ الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّه ُُ سَيَهْدِينِ |
Wa Ja`alahā Kalimatan Bāqiyatan Fī `Aqibihi La`allahum Yarji`ūna | َ043-028 Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata. | وَجَعَلَهَا كَلِمَة ً بَاقِيَة ً فِي عَقِبِه ِِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ |
Bal Matta`tu Hā'uulā' Wa 'Ābā'ahum Ĥattá Jā'ahumu Al-Ĥaqqu Wa Rasūlun Mubīnun | َ043-029 Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu. | بَلْ مَتَّعْتُ هَاؤُلاَء وَآبَاءَهُمْ حَتَّى جَاءَهُمُ الْحَقُّ وَرَسُول ٌ مُبِين ٌ |
Wa Lammā Jā'ahumu Al-Ĥaqqu Qālū Hādhā Siĥrun Wa 'Innā Bihi Kāfirūna | َ043-030 Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne." | وَلَمَّا جَاءَهُمُ الْحَقُّ قَالُوا هَذَا سِحْر ٌ وَإِنَّا بِه ِِ كَافِرُونَ |
Wa Qālū Lawlā Nuzzila Hādhā Al-Qur'ānu `Alá Rajulin Mina Al-Qaryatayni `Ažīmin | َ043-031 Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun nan biyu ba?" | وَقَالُوا لَوْلاَ نُزِّلَ هَذَا الْقُرْآنُ عَلَى رَجُل ٍ مِنَ الْقَرْيَتَيْنِ عَظِيم ٍ |
'Ahum Yaqsimūna Raĥmata Rabbika ۚ Naĥnu Qasamnā Baynahum Ma`īshatahum Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā ۚ Wa Rafa`nā Ba`đahum Fawqa Ba`đin Darajātin Liyattakhidha Ba`đuhum Ba`đāan Sukhrīyāan ۗ Wa Raĥmatu Rabbika Khayrun Mimmā Yajma`ūna | َ043-032 Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci ), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa. | أَهُمْ يَقْسِمُونَ رَحْمَةَ رَبِّكَ ۚ نَحْنُ قَسَمْنَا بَيْنَهُمْ مَعِيشَتَهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَرَفَعْنَا بَعْضَهُمْ فَوْقَ بَعْض ٍ دَرَجَات ٍ لِيَتَّخِذَ بَعْضُهُمْ بَعْضا ً سُخْرِيّا ً ۗ وَرَحْمَةُ رَبِّكَ خَيْر ٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ |
Wa Lawlā 'An Yakūna An-Nāsu 'Ummatan Wāĥidatan Laja`alnā Liman Yakfuru Bir-Raĥmani Libuyūtihim Suqufāan Min Fađđatin Wa Ma`ārija `Alayhā Yažharūna | َ043-033 Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa. | وَلَوْلاَ أَنْ يَكُونَ النَّاسُ أُمَّة ً وَاحِدَة ً لَجَعَلْنَا لِمَنْ يَكْفُرُ بِالرَّحْمَنِ لِبُيُوتِهِمْ سُقُفا ً مِنْ فَضَّة ٍ وَمَعَارِجَ عَلَيْهَا يَظْهَرُونَ |
Wa Libuyūtihim 'Abwābāan Wa Sururāan `Alayhā Yattaki'ūna | َ043-034 Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa. | وَلِبُيُوتِهِمْ أَبْوَابا ً وَسُرُراً عَلَيْهَا يَتَّكِئُونَ |
Wa Zukhrufāan ۚ Wa 'In Kullu Dhālika Lammā Matā`u Al-Ĥayāati Ad-Dunyā Wa ۚ Al-'Ākhiratu `Inda Rabbika Lilmuttaqīna | َ043-035 Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce. | وَزُخْرُفا ً ۚ وَإِنْ كُلُّ ذَلِكَ لَمَّا مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَالآخِرَةُ عِنْدَ رَبِّكَ لِلْمُتَّقِينَ |
Wa Man Ya`shu `An Dhikri Ar-Raĥmāni Nuqayyiđ Lahu Shayţānāan Fahuwa Lahu Qarīnun | َ043-036 Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa. | وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَه ُُ شَيْطَانا ً فَهُوَ لَه ُُ قَرِين ٌ |
Wa 'Innahum Layaşuddūnahum `Ani As-Sabīli Wa Yaĥsabūna 'Annahum Muhtadūna | َ043-037 Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne. | وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ مُهْتَدُونَ |
Ĥattá 'Idhā Jā'anā Qāla Yā Layta Baynī Wa Baynaka Bu`da Al-Mashriqayni Fabi'sa Al-Qarīnu | َ043-038 Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!" | حَتَّى إِذَا جَاءَنَا قَالَ يَالَيْتَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ بُعْدَ الْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ الْقَرِينُ |
Wa Lan Yanfa`akumu Al-Yawma 'Idh Žalamtum 'Annakum Fī Al-`Adhābi Mushtarikūna | َ043-039 Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba. | وَلَنْ يَنفَعَكُمُ الْيَوْمَ إِذْ ظَلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ |
'Afa'anta Tusmi`u Aş-Şumma 'Aw Tahdī Al-`Umya Wa Man Kāna Fī Đalālin Mubīnin | َ043-040 Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna? | أَفَأَنْتَ تُسْمِعُ الصُّمَّ أَوْ تَهْدِي الْعُمْيَ وَمَنْ كَانَ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ |
Fa'immā Nadh/habanna Bika Fa'innā Minhum Muntaqimūna | َ043-041 To, kõ dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu. | فَإِمَّا نَذْهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنْهُمْ مُنْتَقِمُونَ |
'Aw Nuriyannaka Al-Ladhī Wa`adnāhum Fa'innā `Alayhim Muqtadirūna | َ043-042 Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne. | أَوْ نُرِيَنَّكَ الَّذِي وَعَدْنَاهُمْ فَإِنَّا عَلَيْهِمْ مُقْتَدِرُونَ |
Fāstamsik Bial-Ladhī 'Ūĥiya 'Ilayka ۖ 'Innaka `Alá Şirāţin Mustaqīmin | َ043-043 Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl. | فَاسْتَمْسِكْ بِالَّذِي أُوحِيَ إِلَيْكَ ۖ إِنَّكَ عَلَى صِرَاط ٍ مُسْتَقِيم ٍ |
Wa 'Innahu Ladhikrun Laka Wa Liqawmika ۖ Wa Sawfa Tus'alūna | َ043-044 Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku. | وَإِنَّه ُُ لَذِكْر ٌ لَكَ وَلِقَوْمِكَ ۖ وَسَوْفَ تُسْأَلُونَ |
Wa As'al Man 'Arsalnā Min Qablika Min Rusulinā 'Aja`alnā Min Dūni Ar-Raĥmāni 'Ālihatan Yu`badūna | َ043-045 Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?" | وَاسْأَلْ مَنْ أَرْسَلْنَا مِنْ قَبْلِكَ مِنْ رُسُلِنَا أَجَعَلْنَا مِنْ دُونِ الرَّحْمَنِ آلِهَة ً يُعْبَدُونَ |
Wa Laqad 'Arsalnā Mūsá Bi'āyātinā 'Ilá Fir`awna Wa Mala'ihi Faqāla 'Innī Rasūlu Rabbi Al-`Ālamīna | َ043-046 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu." | وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَى بِآيَاتِنَا إِلَى فِرْعَوْنَ وَمَلَئِه ِِ فَقَالَ إِنِّي رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَ |
Falammā Jā'ahum Bi'āyātinā 'Idhā Hum Minhā Yađĥakūna | َ043-047 To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya. | فَلَمَّا جَاءَهُمْ بِآيَاتِنَا إِذَا هُمْ مِنْهَا يَضْحَكُونَ |
Wa Mā Nurīhim Min 'Āyatin 'Illā Hiya 'Akbaru Min 'Ukhtihā ۖ Wa 'Akhadhnāhum Bil-`Adhābi La`allahum Yarji`ūna | َ043-048 Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa. | وَمَا نُرِيهِمْ مِنْ آيَة ٍ إِلاَّ هِيَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا ۖ وَأَخَذْنَاهُمْ بِالْعَذَابِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ |
Wa Qālū Yā 'Ayyuhā As-Sāĥiru Ad`u Lanā Rabbaka Bimā `Ahida `Indaka 'Innanā Lamuhtadūn | َ043-049 Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne." | وَقَالُوا يَاأَيُّهَا السَّاحِرُ ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِنْدَكَ إِنَّنَا لَمُهْتَدُون |
Falammā Kashafnā `Anhumu Al-`Adhāba 'Idhā Hum Yankuthūna | َ043-050 To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu. | فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الْعَذَابَ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ |
Wa Nādá Fir`awnu Fī Qawmihi Qāla Yā Qawmi 'Alaysa Lī Mulku Mişra Wa Hadhihi Al-'Anhāru Tajrī Min Taĥtī ۖ 'Afalā Tubşirūna | َ043-051 Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?" | وَنَادَى فِرْعَوْنُ فِي قَوْمِه ِِ قَالَ يَاقَوْمِ أَلَيْسَ لِي مُلْكُ مِصْرَ وَهَذِهِ الأَنْهَارُ تَجْرِي مِنْ تَحْتِي أَفَلاَ ۖ تُبْصِرُونَ |
'Am 'Anā Khayrun Min Hādhā Al-Ladhī Huwa Mahīnun Wa Lā Yakādu Yubīnu | َ043-052 "Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar? | أَمْ أَنَا خَيْر ٌ مِنْ هَذَا الَّذِي هُوَ مَهِين ٌ وَلاَ يَكَادُ يُبِينُ |
Falawlā 'Ulqiya `Alayhi 'Aswiratun Min Dhahabin 'Aw Jā'a Ma`ahu Al-Malā'ikatu Muqtarinīna | َ043-053 "To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?" | فَلَوْلاَ أُلْقِيَ عَلَيْهِ أَسْوِرَة ٌ مِنْ ذَهَبٍ أَوْ جَاءَ مَعَهُ الْمَلاَئِكَةُ مُقْتَرِنِينَ |
Fāstakhaffa Qawmahu Fa'aţā`ūhu ۚ 'Innahum Kānū Qawmāan Fāsiqīna | َ043-054 Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai. | فَاسْتَخَفَّ قَوْمَه ُُ فَأَطَاعُوهُ~ُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْما ً فَاسِقِينَ |
Falammā 'Āsafūnā Antaqamnā Minhum Fa'aghraqnāhum 'Ajma`īna | َ043-055 Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya. | فَلَمَّا آسَفُونَا انتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَ |
Faja`alnāhum Salafāan Wa Mathalāan Lil'ākhirīna | َ043-056 Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe. | فَجَعَلْنَاهُمْ سَلَفا ً وَمَثَلا ً لِلآخِرِينَ |
Wa Lammā Đuriba Abnu Maryama Mathalāan 'Idhā Qawmuka Minhu Yaşiddūna | َ043-057 Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili. | وَلَمَّا ضُرِبَ ابْنُ مَرْيَمَ مَثَلا ً إِذَا قَوْمُكَ مِنْهُ يَصِدُّونَ |
Wa Qālū 'A'ālihatunā Khayrun 'Am Huwa ۚ Mā Đarabūhu Laka 'Illā Jadalāan ۚ Bal Hum Qawmun Khaşimūna | َ043-058 Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma. | وَقَالُوا أَآلِهَتُنَا خَيْرٌ أَمْ هُوَ ۚ مَا ضَرَبُوه ُُ لَكَ إِلاَّ جَدَلا ً ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ خَصِمُونَ |
'In Huwa 'Illā `Abdun 'An`amnā `Alayhi Wa Ja`alnāhu Mathalāan Libanī 'Isrā'īla | َ043-059 Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla. | إِنْ هُوَ إِلاَّ عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ وَجَعَلْنَاه ُُ مَثَلا ً لِبَنِي إِسْرَائِيلَ |
Wa Law Nashā'u Laja`alnā Minkum Malā'ikatan Fī Al-'Arđi Yakhlufūna | َ043-060 Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa | وَلَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَا مِنْكُمْ مَلاَئِكَة ً فِي الأَرْضِ يَخْلُفُونَ |
Wa 'Innahu La`ilmun Lilssā`ati Falā Tamtarunna Bihā Wa Attabi`ūnī ۚ Hādhā Şirāţun Mustaqīmun | َ043-061 Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya. | وَإِنَّه ُُ لَعِلْم ٌ لِلسَّاعَةِ فَلاَ تَمْتَرُنَّ بِهَا وَاتَّبِعُونِي ۚ هَذَا صِرَاط ٌ مُسْتَقِيم ٌ |
Wa Lā Yaşuddannakumu Ash-Shayţānu ۖ 'Innahu Lakum `Adūwun Mubīnun | َ043-062 Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya. | وَلاَ يَصُدَّنَّكُمُ الشَّيْطَانُ ۖ إِنَّه ُُ لَكُمْ عَدُوّ ٌ مُبِين ٌ |
Wa Lammā Jā'a `Īsá Bil-Bayyināti Qāla Qad Ji'tukum Bil-Ĥikmati Wa Li'abayyina Lakum Ba`đa Al-Ladhī Takhtalifūna Fīhi Fa ۖ Attaqū Al-Laha Wa 'Aţī`ūni | َ043-063 Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a." | وَلَمَّا جَاءَ عِيسَى بِالْبَيِّنَاتِ قَالَ قَدْ جِئْتُكُمْ بِالْحِكْمَةِ وَلِأَبَيِّنَ لَكُمْ بَعْضَ الَّذِي تَخْتَلِفُونَ فِيه ِِ ۖ فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ |
'Inna Al-Laha Huwa Rabbī Wa Rabbukum Fā`budūhu ۚ Hādhā Şirāţun Mustaqīmun | َ043-064 "Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya." | إِنَّ اللَّهَ هُوَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوه ُُ ۚ هَذَا صِرَاط ٌ مُسْتَقِيم ٌ |
Fākhtalafa Al-'Aĥzābu Min Baynihim ۖ Fawaylun Lilladhīna Žalamū Min `Adhābi Yawmin 'Alīmin | َ043-065 Sai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi! | فَاخْتَلَفَ الأَحْزَابُ مِنْ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْل ٌ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْ عَذَابِ يَوْمٍ أَلِيم ٍ |
Hal Yanžurūna 'Illā As-Sā`ata 'An Ta'tiyahum Baghtatan Wa Hum Lā Yash`urūna | َ043-066 Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba. | هَلْ يَنظُرُونَ إِلاَّ السَّاعَةَ أَنْ تَأْتِيَهُمْ بَغْتَة ً وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ |
Al-'Akhillā'u Yawma'idhin Ba`đuhum Liba`đin `Adūwun 'Illā Al-Muttaqīna | َ043-067 Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne). | الأَخِلاَّءُ يَوْمَئِذ ٍ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوّ ٌ إِلاَّ الْمُتَّقِينَ |
Yā `Ibādi Lā Khawfun `Alaykumu Al-Yawma Wa Lā 'Antum Taĥzanūna | َ043-068 Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba. | يَاعِبَادِ لاَ خَوْفٌ عَلَيْكُمُ الْيَوْمَ وَلاَ أَنْتُمْ تَحْزَنُونَ |
Al-Ladhīna 'Āmanū Bi'āyātinā Wa Kānū Muslimīna | َ043-069 Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah). | الَّذِينَ آمَنُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا مُسْلِمِينَ |
Adkhulū Al-Jannata 'Antum Wa 'Azwājukum Tuĥbarūna | َ043-070 Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku. | ادْخُلُوا الْجَنَّةَ أَنْتُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ تُحْبَرُونَ |
Yuţāfu `Alayhim Bişiĥāfin Min Dhahabin Wa 'Akwābin ۖ Wa Fīhā Mā Tashtahīhi Al-'Anfusu Wa Taladhdhu Al-'A`yunu ۖ Wa 'Antum Fīhā Khālidūna | َ043-071 Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne. | يُطَافُ عَلَيْهِمْ بِصِحَاف ٍ مِنْ ذَهَب ٍ وَأَكْوَاب ٍ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ الأَنفُسُ وَتَلَذُّ الأَعْيُنُ ۖ وَأَنْتُمْ فِيهَا خَالِدُونَ |
Wa Tilka Al-Jannatu Allatī 'Ūrithtumūhā Bimā Kuntum Ta`malūna | َ043-072 Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. | وَتِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ |
Lakum Fīhā Fākihatun Kathīratun Minhā Ta'kulūna | َ043-073 Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci. | لَكُمْ فِيهَا فَاكِهَة ٌ كَثِيرَة ٌ مِنْهَا تَأْكُلُونَ |
'Inna Al-Mujrimīna Fī `Adhābi Jahannama Khālidūn | َ043-074 Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama. | إِنَّ الْمُجْرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَالِدُون |
Lā Yufattaru `Anhum Wa Hum Fīhi Mublisūna | َ043-075 Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ,a cikinta, mãsu kãsa magana ne. | لاَ يُفَتَّرُ عَنْهُمْ وَهُمْ فِيه ِِ مُبْلِسُونَ |
Wa Mā Žalamnāhum Wa Lakin Kānū Humu Až-Žālimīna | َ043-076 Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai. | وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَكِنْ كَانُوا هُمُ الظَّالِمِينَ |
Wa Nādaw Yā Māliku Liyaqđi `Alaynā Rabbuka ۖ Qāla 'Innakum Mākithūna | َ043-077 Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne." | وَنَادَوْا يَامَالِكُ لِيَقْضِ عَلَيْنَا رَبُّكَ قَالَ ۖ إِنَّكُمْ مَاكِثُونَ |
Laqad Ji'nākum Bil-Ĥaqqi Wa Lakinna 'Aktharakum Lilĥaqqi Kārihūna | َ043-078 Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne. | لَقَدْ جِئْنَاكُمْ بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَكُمْ لِلْحَقِّ كَارِهُونَ |
'Am 'Abramū 'Amrāan Fa'innā Mubrimūna | َ043-079 Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne. | أَمْ أَبْرَمُوا أَمْرا ً فَإِنَّا مُبْرِمُونَ |
'Am Yaĥsabūna 'Annā Lā Nasma`u Sirrahum Wa Najwāhum ۚ Balá Wa Rusulunā Ladayhim Yaktubūna | َ043-080 Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa. | أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لاَ نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَاهُمْ ۚ بَلَى وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَ |
Qul 'In Kāna Lilrraĥmani Waladun Fa'anā 'Awwalu Al-`Ābidīna | َ043-081 Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)." | قُلْ إِنْ كَانَ لِلرَّحْمَنِ وَلَد ٌ فَأَنَا أَوَّلُ الْعَابِدِينَ |
Subĥāna Rabbi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Rabbi Al-`Arshi `Ammā Yaşifūna | َ043-082 Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa. | سُبْحَانَ رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ رَبِّ الْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ |
Fadharhum Yakhūđū Wa Yal`abū Ĥattá Yulāqū Yawmahumu Al-Ladhī Yū`adūna | َ043-083 Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi. | فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّى يُلاَقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَ |
Wa Huwa Al-Ladhī Fī As-Samā'i 'Ilahun Wa Fī Al-'Arđi 'Ilahun ۚ Wa Huwa Al-Ĥakīmu Al-`Alīmu | َ043-084 Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani. | وَهُوَ الَّذِي فِي السَّمَاءِ إِلَه ٌ ٌ وَفِي الأَرْضِ إِلَه ٌ ٌ ۚ وَهُوَ الْحَكِيمُ الْعَلِيمُ |
Wa Tabāraka Al-Ladhī Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā Wa `Indahu `Ilmu As-Sā`ati Wa 'Ilayhi Turja`ūna | َ043-085 Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. | وَتَبَارَكَ الَّذِي لَه ُُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِنْدَه ُُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ |
Wa Lā Yamliku Al-Ladhīna Yad`ūna Min Dūnihi Ash-Shafā`ata 'Illā Man Shahida Bil-Ĥaqqi Wa Hum Ya`lamūna | َ043-086 Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka). | وَلاَ يَمْلِكُ الَّذِينَ يَدْعُونَ مِنْ دُونِهِ الشَّفَاعَةَ إِلاَّ مَنْ شَهِدَ بِالْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ |
Wa La'in Sa'altahum Man Khalaqahum Layaqūlunna Al-Lahu ۖ Fa'anná Yu'ufakūna | َ043-087 Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su? | وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ ۖ فَأَنَّى يُؤْفَكُونَ |
Wa Qīlihi Yā Rabbi 'Inna Hā'uulā' Qawmun Lā Yu'uminūna | َ043-088 Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba." | وَقِيلِه ِِ يَارَبِّ إِنَّ هَاؤُلاَء قَوْم ٌ لاَ يُؤْمِنُونَ |
Fāşfaĥ `Anhum Wa Qul Salāmun ۚ Fasawfa Ya`lamūna | َ043-089 To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani. | فَاصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلاَم ٌ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ |