Ĥā-Mīm | َ044-001 Ḥ. M̃. | حَا-مِيم |
Wa Al-Kitābi Al-Mubīni | َ044-002 Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. | وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ |
'Innā 'Anzalnāhu Fī Laylatin Mubārakatin ۚ 'Innā Kunnā Mundhirīna | َ044-003 Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. | إِنَّا أَنزَلْنَاه ُُ فِي لَيْلَة ٍ مُبَارَكَة ٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ |
Fīhā Yufraqu Kullu 'Amrin Ĥakīmin | َ044-004 A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. | فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيم ٍ |
'Amrāan Min `Indinā ۚ 'Innā Kunnā Mursilīna | َ044-005 Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. | أَمْرا ً مِنْ عِنْدِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ |
Raĥmatan Min Rabbika ۚ 'Innahu Huwa As-Samī`u Al-`Alīmu | َ044-006 Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. | رَحْمَة ً مِنْ رَبِّكَ ۚ إِنَّه ُُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ |
Rabbi As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa Mā Baynahumā ۖ 'In Kuntum Mūqinīna | َ044-007 (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). | رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِنْ كُنْتُمْ مُوقِنِينَ |
Lā 'Ilāha 'Illā Huwa Yuĥyī Wa Yumītu ۖ Rabbukum Wa Rabbu 'Ābā'ikumu Al-'Awwalīna | َ044-008 Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. | لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الأَوَّلِينَ |
Bal Hum Fī Shakkin Yal`abūna | َ044-009 A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. | بَلْ هُمْ فِي شَكّ ٍ يَلْعَبُونَ |
Fārtaqib Yawma Ta'tī As-Samā'u Bidukhānin Mubīnin | َ044-010 Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. | فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَان ٍ مُبِين ٍ |
Yaghshá An-Nāsa ۖ Hādhā `Adhābun 'Alīmun | َ044-011 Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. | يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَذَا عَذَابٌ أَلِيم ٌ |
Rabbanā Akshif `Annā Al-`Adhāba 'Innā Mu'uminūna | َ044-012 Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. | رَبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ |
'Anná Lahumu Adh-Dhikrá Wa Qad Jā'ahum Rasūlun Mubīnun | َ044-013 Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? | أَنَّى لَهُمُ الذِّكْرَى وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُول ٌ مُبِين ٌ |
Thumma Tawallaw `Anhu Wa Qālū Mu`allamun Majnūnun | َ044-014 Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." | ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّم ٌ مَجْنُون ٌ |
'Innā Kāshifū Al-`Adhābi Qalīlāan ۚ 'Innakum `Ā'idūna | َ044-015 Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). | إِنَّا كَاشِفُوا الْعَذَابِ قَلِيلا ً ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ |
Yawma Nabţishu Al-Baţshata Al-Kubrá 'Innā Muntaqimūna | َ044-016 Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. | يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَى إِنَّا مُنتَقِمُونَ |
Wa Laqad Fatannā Qablahum Qawma Fir`awna Wa Jā'ahum Rasūlun Karīmun | َ044-017 Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. | وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُول ٌ كَرِيم ٌ |
'An 'Addū 'Ilayya `Ibāda Al-Lahi ۖ 'Innī Lakum Rasūlun 'Amīnun | َ044-018 (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." | أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِين ٌ |
Wa 'An Lā Ta`lū `Alá Al-Lahi ۖ 'Innī 'Ātīkum Bisulţānin Mubīnin | َ044-019 "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." | وَأَنْ لاَ تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُمْ بِسُلْطَان ٍ مُبِين ٍ |
Wa 'Innī `Udhtu Birabbī Wa Rabbikum 'An Tarjumūni | َ044-020 "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." | وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَنْ تَرْجُمُونِ |
Wa 'In Lam Tu'uminū Lī Fā`tazilūni | َ044-021 "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." | وَإِنْ لَمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ |
Fada`ā Rabbahu 'Anna Hā'uulā' Qawmun Mujrimūna | َ044-022 Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. | فَدَعَا رَبَّهُ~ُ أَنَّ هَاؤُلاَء قَوْم ٌ مُجْرِمُونَ |
Fa'asri Bi`ibādī Laylāan 'Innakum Muttaba`ūna | َ044-023 (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" | فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلا ً إِنَّكُمْ مُتَّبَعُونَ |
Wa Atruki Al-Baĥra Rahwan ۖ 'Innahum Jundun Mughraqūna | َ044-024 "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." | وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوا ً ۖ إِنَّهُمْ جُند ٌ مُغْرَقُونَ |
Kam Tarakū Min Jannātin Wa `Uyūnin | َ044-025 Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. | كَمْ تَرَكُوا مِنْ جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ |
Wa Zurū`in Wa Maqāmin Karīmin | َ044-026 Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. | وَزُرُوع ٍ وَمَقَام ٍ كَرِيم ٍ |
Wa Na`matin Kānū Fīhā Fākihīna | َ044-027 Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. | وَنَعْمَة ٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ |
Kadhālika ۖ Wa 'Awrathnāhā Qawmāan 'Ākharīna | َ044-028 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. | كَذَلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْما ً آخَرِينَ |
Famā Bakat `Alayhimu As-Samā'u Wa Al-'Arđu Wa Mā Kānū Munžarīna | َ044-029 Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. | فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ |
Wa Laqad Najjaynā Banī 'Isrā'īla Mina Al-`Adhābi Al-Muhīni | َ044-030 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. | وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ |
Min Fir`awna ۚ 'Innahu Kāna `Ālīāan Mina Al-Musrifīna | َ044-031 Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. | مِنْ فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّه ُُ كَانَ عَالِيا ً مِنَ الْمُسْرِفِينَ |
Wa Laqadi Akhtarnāhum `Alá `Ilmin `Alá Al-`Ālamīna | َ044-032 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. | وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَى عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ |
Wa 'Ātaynāhum Mina Al-'Āyāti Mā Fīhi Balā'un Mubīnun | َ044-033 Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna | وَآتَيْنَاهُمْ مِنَ الآيَاتِ مَا فِيه ِِ بَلاَء ٌ مُبِين ٌ |
'Inna Hā'uulā' Layaqūlūna | َ044-034 Lalle waɗannan mutãne , haƙĩka, sunã cẽwa, | إِنَّ هَاؤُلاَء لَيَقُولُونَ |
'In Hiya 'Illā Mawtatunā Al-'Ūlá Wa Mā Naĥnu Bimunsharīna | َ044-035 "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." | إِنْ هِيَ إِلاَّ مَوْتَتُنَا الأُولَى وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ |
Fa'tū Bi'ābā'inā 'In Kuntum Şādiqīna | َ044-036 "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." | فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ |
'Ahum Khayrun 'Am Qawmu Tubba`in Wa Al-Ladhīna Min Qablihim ۚ 'Ahlaknāhum ۖ 'Innahum Kānū Mujrimīna | َ044-037 shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. | أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّع ٍ وَالَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ |
Wa Mā Khalaqnā As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Wa Mā Baynahumā Lā`ibīna | َ044-038 Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. | وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لاَعِبِينَ |
Mā Khalaqnāhumā 'Illā Bil-Ĥaqqi Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna | َ044-039 Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. | مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ |
'Inna Yawma Al-Faşli Mīqātuhum 'Ajma`īna | َ044-040 Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. | إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ |
Yawma Lā Yughnī Mawláan `An Mawláan Shay'āan Wa Lā Hum Yunşarūna | َ044-041 Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. | يَوْمَ لاَ يُغْنِي مَوْلىً عَنْ مَوْلى ً شَيْئا ً وَلاَ هُمْ يُنصَرُونَ |
'Illā Man Raĥima Al-Lahu ۚ 'Innahu Huwa Al-`Azīzu Ar-Raĥīmu | َ044-042 fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. | إِلاَّ مَنْ رَحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّه ُُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ |
'Inna Shajarata Az-Zaqqūmi | َ044-043 Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), | إِنَّ شَجَرَةَ الزَّقُّومِ |
Ţa`āmu Al-'Athīmi | َ044-044 Ita ce abincin mai laifi. | طَعَامُ الأَثِيمِ |
Kālmuhli Yaghlī Fī Al-Buţūni | َ044-045 Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. | كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ |
Kaghalyi Al-Ĥamīmi | َ044-046 Kamar tafasar ruwan zãfi. | كَغَلْيِ الْحَمِيمِ |
Khudhūhu Fā`tilūhu 'Ilá Sawā'i Al-Jaĥīmi | َ044-047 (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." | خُذُوه ُُ فَاعْتِلُوهُ~ُ إِلَى سَوَاءِ الْجَحِيمِ |
Thumma Şubbū Fawqa Ra'sihi Min `Adhābi Al-Ĥamīmi | َ044-048 "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." | ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِه ِِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ |
Dhuq 'Innaka 'Anta Al-`Azīzu Al-Karīmu | َ044-049 (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" | ذُقْ إِنَّكَ أَنْتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ |
'Inna Hādhā Mā Kuntum Bihi Tamtarūna | َ044-050 "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." | إِنَّ هَذَا مَا كُنتُمْ بِه ِِ تَمْتَرُونَ |
'Inna Al-Muttaqīna Fī Maqāmin 'Amīnin | َ044-051 Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. | إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِين ٍ |
Fī Jannātin Wa `Uyūnin | َ044-052 A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. | فِي جَنَّات ٍ وَعُيُون ٍ |
Yalbasūna Min Sundusin Wa 'Istabraqin Mutaqābilīna | َ044-053 Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. | يَلْبَسُونَ مِنْ سُندُس ٍ وَإِسْتَبْرَق ٍ مُتَقَابِلِينَ |
Kadhālika Wa Zawwajnāhum Biĥūrin `Īnin | َ044-054 Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. | كَذَلِكَ وَزَوَّجْنَاهُمْ بِحُورٍ عِين ٍ |
Yad`ūna Fīhā Bikulli Fākihatin 'Āminīna | َ044-055 Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). | يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَة ٍ آمِنِينَ |
Lā Yadhūqūna Fīhā Al-Mawta 'Illā Al-Mawtata Al-'Ūlá ۖ Wa Waqāhum `Adhāba Al-Jaĥīmi | َ044-056 Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. | لاَ يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلاَّ الْمَوْتَةَ الأُولَى ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ |
Fađlāan Min Rabbika ۚ Dhālika Huwa Al-Fawzu Al-`Ažīmu | َ044-057 Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. | فَضْلا ً مِنْ رَبِّكَ ۚ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ |
Fa'innamā Yassarnāhu Bilisānika La`allahum Yatadhakkarūna | َ044-058 Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. | فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاه ُُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ |
Fārtaqib 'Innahum Murtaqibūna | َ044-059 Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. | فَارْتَقِبْ إِنَّهُمْ مُرْتَقِبُونَ |