39) Sūrat Az-Zumar

Printed format

39) سُورَة الزُّمَر

Tanzīlu Al-Kitābi Mina Al-Lahi Al-`Azīzi Al-Ĥakīmi َ039-001 Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima. تَنْزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ
'Innā 'Anzalnā 'Ilayka Al-Kitāba Bil-Ĥaqqi Fā`budi Al-Laha Mukhlişāan Lahu Ad-Dīna َ039-002 Lalle Mũ Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka, da gaskiya. Sabõda haka, ka bauta wa Allah kanã mai tsarkake addini a gare Shi. إِنَّا أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصا ً لَهُ الدِّينَ
'Alā Lillahi Ad-Dīnu Al-Khālişu Wa  ۚ  Al-Ladhīna Attakhadhū Min Dūnihi 'Awliyā'a Mā Na`buduhum 'Illā Liyuqarribūnā 'Ilá Al-Lahi Zulfá 'Inna Al-Laha Yaĥkumu Baynahum Fī Mā Hum Fīhi Yakhtalifūna  ۗ  'Inna Al-Laha Lā Yahdī Man Huwa Kādhibun Kaffārun َ039-003 To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci. أَلاَ لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ  ۚ  وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ~ِ أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلاَّ لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللَّهِ زُلْفَى إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِي مَا هُمْ فِيه ِِ يَخْتَلِفُونَ  ۗ  إِنَّ اللَّهَ لاَ يَهْدِي مَنْ هُوَ كَاذِب ٌ كَفَّار ٌ
Law 'Arāda Al-Lahu 'An Yattakhidha Waladāan Lāşţafá Mimmā Yakhluqu Mā Yashā'u  ۚ  Subĥānahu  ۖ  Huwa Al-Lahu Al-Wāĥidu Al-Qahhāru َ039-004 Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa. لَوْ أَرَادَ اللَّهُ أَنْ يَتَّخِذَ وَلَدا ً لاَصْطَفَى مِمَّا يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ  ۚ  سُبْحَانَه ُُ  ۖ  هُوَ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ
Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Bil-Ĥaqqi  ۖ  Yukawwiru Al-Layla `Alá An-Nahāri Wa Yukawwiru An-Nahāra `Alá Al-Layli  ۖ  Wa Sakhkhara Ash-Shamsa Wa Al-Qamara  ۖ  Kullun Yajrī Li'jalin Musammáan  ۗ  'Alā Huwa Al-`Azīzu Al-Ghaffāru َ039-005 Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara. خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ  ۖ  يُكَوِّرُ اللَّيْلَ عَلَى النَّهَارِ وَيُكَوِّرُ النَّهَارَ عَلَى اللَّيْلِ  ۖ  وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ  ۖ  كُلّ ٌ يَجْرِي لِأجَل ٍ مُسَمّىً  ۗ  أَلاَ هُوَ الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ
Khalaqakum Min Nafsin Wāĥidatin Thumma Ja`ala Minhā Zawjahā Wa 'Anzala Lakum Mina Al-'An`ām Thamāniyata 'Azwājin  ۚ  Yakhluqukum Fī Buţūni 'Ummahātikum Khalqāan Min Ba`di Khalqin Fī Žulumātin Thalāthin  ۚ  Dhalikumu Al-Lahu Rabbukum Lahu Al-Mulku  ۖ  Lā 'Ilāha 'Illā Huwa  ۖ  Fa'anná Tuşrafūna َ039-006 Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس ٍ وَاحِدَة ٍ ثُمَّ جَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَأَنْزَلَ لَكُمْ مِنَ الأَنعَام ثَمَانِيَةَ أَزْوَاج ٍ  ۚ  يَخْلُقُكُمْ فِي بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ خَلْقا ً مِنْ بَعْدِ خَلْق ٍ فِي ظُلُمَات ٍ ثَلاَث ٍ  ۚ  ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ لَهُ الْمُلْكُ  ۖ  لاَ إِلَهَ~َ إِلاَّ هُوَ  ۖ  فَأَنَّى تُصْرَفُونَ
'In Takfurū Fa'inna Al-Laha Ghanīyun `Ankum  ۖ  Wa Lā Yarđá Li`ibādihi Al-Kufra  ۖ  Wa 'In Tashkurū Yarđahu Lakum  ۗ  Wa Lā Taziru Wāziratun Wizra 'Ukhrá  ۗ  Thumma 'Ilá Rabbikum Marji`ukum Fayunabbi'ukum Bimā Kuntum Ta`malūna  ۚ  'Innahu `Alīmun Bidhāti Aş-Şudūri َ039-007 Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata. إِنْ تَكْفُرُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ عَنْكُمْ  ۖ  وَلاَ يَرْضَى لِعِبَادِهِ الْكُفْرَ  ۖ  وَإِنْ تَشْكُرُوا يَرْضَه ُُ لَكُمْ  ۗ  وَلاَ تَزِرُ وَازِرَة ٌ وِزْرَ أُخْرَى  ۗ  ثُمَّ إِلَى رَبِّكُمْ مَرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ  ۚ  إِنَّه ُُ عَلِيم ٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ
Wa 'Idhā Massa Al-'Insāna Đurrun Da`ā Rabbahu Munībāan 'Ilayhi Thumma 'Idhā Khawwalahu Ni`matan Minhu Nasiya Mā Kāna Yad`ū 'Ilayhi Min Qablu Wa Ja`ala Lillahi 'Andādāan Liyuđilla `An Sabīlihi  ۚ  Qul Tamatta` Bikufrika Qalīlāan  ۖ  'Innaka Min 'Aşĥābi An-Nāri َ039-008 Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne." وَإِذَا مَسَّ الإِنسَانَ ضُرّ ٌ دَعَا رَبَّه ُُ مُنِيبا ً إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا خَوَّلَه ُُ نِعْمَة ً مِنْهُ نَسِيَ مَا كَانَ يَدْعُو إِلَيْهِ مِنْ قَبْلُ وَجَعَلَ لِلَّهِ أَنْدَادا ً لِيُضِلَّ عَنْ سَبِيلِه ِِ  ۚ  قُلْ تَمَتَّعْ بِكُفْرِكَ قَلِيلا ً  ۖ  إِنَّكَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ
'Amman Huwa Qānitun 'Ānā'a Al-Layli Sājidāan Wa Qā'imāan Yaĥdharu Al-'Ākhirata Wa Yarjū Raĥmata Rabbihi  ۗ  Qul Hal Yastawī Al-Ladhīna Ya`lamūna Wa Al-Ladhīna Lā Ya`lamūna  ۗ  'Innamā Yatadhakkaru 'Ū Al-'Albābi َ039-009 Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni. أَمَّنْ هُوَ قَانِت ٌ آنَاءَ اللَّيْلِ سَاجِدا ً وَقَائِما ً يَحْذَرُ الآخِرَةَ وَيَرْجُو رَحْمَةَ رَبِّه ِِ  ۗ  قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لاَ يَعْلَمُونَ  ۗ  إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُوا الأَلْبَابِ
Qul Yā `Ibādi Al-Ladhīna 'Āmanū Attaqū Rabbakum  ۚ  Lilladhīna 'Aĥsanū Fī Hadhihi Ad-Dunyā Ĥasanatun  ۗ  Wa 'Arđu Al-Lahi Wāsi`atun  ۗ  'Innamā Yuwaffá Aş-Şābirūna 'Ajrahum Bighayri Ĥisābin َ039-010 Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni!Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba. قُلْ يَاعِبَادِ الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا رَبَّكُمْ لِلَّذِينَ  ۚ  أَحْسَنُوا فِي هَذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَة ٌ وَأَرْضُ  ۗ  اللَّهِ وَاسِعَة ٌ إِنَّمَا  ۗ  يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُمْ بِغَيْرِ حِسَاب ٍ
Qul 'Innī 'Umirtu 'An 'A`buda Al-Laha Mukhlişāan Lahu Ad-Dīna َ039-011 Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi. قُلْ إِنِّي أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ اللَّهَ مُخْلِصا ً لَهُ الدِّينَ
Wa 'Umirtu Li'n 'Akūna 'Awwala Al-Muslimīna َ039-012 "Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)." وَأُمِرْتُ لِأنْ أَكُونَ أَوَّلَ الْمُسْلِمِينَ
Qul 'Innī 'Akhāfu 'In `Aşaytu Rabbī `Adhāba Yawmin `Ažīmin َ039-013 Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma." قُلْ إِنِّي أَخَافُ إِنْ عَصَيْتُ رَبِّي عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيم ٍ
Quli Al-Laha 'A`budu Mukhlişāan Lahu Dīni َ039-014 Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi. قُلِ اللَّهَ أَعْبُدُ مُخْلِصا ً لَه ُُ دِينِ
Fā`budū Mā Shi'tum Min Dūnihi  ۗ  Qul 'Inna Al-Khāsirīna Al-Ladhīna Khasirū 'Anfusahum Wa 'Ahlīhim Yawma Al-Qiyāmati  ۗ  'Alā Dhālika Huwa Al-Khusrānu Al-Mubīnu َ039-015 "To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna." فَاعْبُدُوا مَا شِئْتُمْ مِنْ دُونِه ِِ  ۗ  قُلْ إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنْفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۗ  أَلاَ ذَلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ
Lahum Min Fawqihim Žulalun Mina An-Nāri Wa Min Taĥtihim Žulalun  ۚ  Dhālika Yukhawwifu Al-Lahu Bihi `Ibādahu  ۚ  Yā `Ibādi Fa Attaqūni َ039-016 Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa. لَهُمْ مِنْ فَوْقِهِمْ ظُلَل ٌ مِنَ النَّارِ وَمِنْ تَحْتِهِمْ ظُلَل ٌ  ۚ  ذَلِكَ يُخَوِّفُ اللَّهُ بِه ِِ عِبَادَه ُُ  ۚ  يَاعِبَادِ فَاتَّقُونِ
Wa Al-Ladhīna Ajtanabū Aţ-Ţāghūta 'An Ya`budūhā Wa 'Anābū 'Ilá Al-Lahi Lahumu  ۚ  Al-Bushrá Fabashshir `Ibādi َ039-017 Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa. وَالَّذِينَ اجْتَنَبُوا الطَّاغُوتَ أَنْ يَعْبُدُوهَا وَأَنَابُوا إِلَى اللَّهِ لَهُمُ الْبُشْرَى  ۚ  فَبَشِّرْ عِبَادِ
Al-Ladhīna Yastami`ūna Al-Qawla Fayattabi`ūna 'Aĥsanahu  ۚ  'Ūlā'ika Al-Ladhīna Hadāhumu Al-Lahu  ۖ  Wa 'Ūlā'ika Hum 'Ū Al-'Albābi َ039-018 Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali, الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ~ُ  ۚ  أُوْلَائِكَ الَّذِينَ هَدَاهُمُ اللَّهُ  ۖ  وَأُوْلَائِكَ هُمْ أُوْلُوا الأَلْبَابِ
'Afaman Ĥaqqa `Alayhi Kalimatu Al-`Adhābi 'Afa'anta Tunqidhu Man An-Nāri َ039-019 Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã? أَفَمَنْ حَقَّ عَلَيْهِ كَلِمَةُ الْعَذَابِ أَفَأَنْتَ تُنقِذُ مَنْ فِي النَّارِ
Lakini Al-Ladhīna Attaqaw Rabbahum Lahum Ghurafun Min Fawqihā Ghurafun Mabnīyatun Tajrī Min Taĥtihā Al-'Anhāru  ۖ  Wa`da Al-Lahi  ۖ  Lā Yukhlifu Al-Lahu Al-Mī`ād َ039-020 Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa. لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ لَهُمْ غُرَف ٌ مِنْ فَوْقِهَا غُرَف ٌ مَبْنِيَّة ٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأَنْهَارُ  ۖ  وَعْدَ اللَّهِ  ۖ  لاَ يُخْلِفُ اللَّهُ الْمِيعَاد
'Alam Tará 'Anna Al-Laha 'Anzala Mina As-Samā'i Mā'an Fasalakahu Yanābī`a Fī Al-'Arđi Thumma Yukhriju Bihi Zar`āan Mukhtalifāan 'Alwānuhu Thumma Yahīju Fatarāhu Muşfarrāan Thumma Yaj`aluhu Ĥuţāmāan  ۚ  'Inna Fī Dhālika Ladhikrá Li'wlī Al-'Albābi َ039-021 Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna). أَلَمْ تَرَى أَنَّ اللَّهَ أَنْزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاء ً فَسَلَكَه ُُ يَنَابِيعَ فِي الأَرْضِ ثُمَّ يُخْرِجُ بِه ِِ زَرْعا ً مُخْتَلِفاً أَلْوَانُه ُُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاه ُُ مُصْفَرّا ً ثُمَّ يَجْعَلُه ُُ حُطَاما ً  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَذِكْرَى لِأوْلِي الأَلْبَابِ
'Afaman Sharaĥa Al-Lahu Şadrahu Lil'islāmi Fahuwa `Alá Nūrin Min Rabbihi  ۚ  Fawaylun Lilqāsiyati Qulūbuhum Min Dhikri Al-Lahi  ۚ  'Ūlā'ika Fī Đalālin Mubīnin َ039-022 Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna. أَفَمَنْ شَرَحَ اللَّهُ صَدْرَه ُُ لِلإِسْلاَمِ فَهُوَ عَلَى نُور ٍ مِنْ رَبِّه ِِ  ۚ  فَوَيْل ٌ لِلْقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمْ مِنْ ذِكْرِ اللَّهِ  ۚ  أُوْلَائِكَ فِي ضَلاَل ٍ مُبِين ٍ
Al-Lahu Nazzala 'Aĥsana Al-Ĥadīthi Kitābāan Mutashābihāan Mathāniya Taqsha`irru Minhu Julūdu Al-Ladhīna Yakhshawna Rabbahum Thumma Talīnu Julūduhum Wa Qulūbuhum 'Ilá Dhikri Al-Lahi  ۚ  Dhālika Hudá Al-Lahi Yahdī Bihi Man Yashā'u  ۚ  Wa Man Yuđlili Al-Lahu Famā Lahu Min Hādin َ039-023 Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa. اللَّهُ نَزَّلَ أَحْسَنَ الْحَدِيثِ كِتَابا ً مُتَشَابِها ً مَثَانِيَ تَقْشَعِرُّ مِنْهُ جُلُودُ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمْ وَقُلُوبُهُمْ إِلَى ذِكْرِ اللَّهِ  ۚ  ذَلِكَ هُدَى اللَّهِ يَهْدِي بِه ِِ مَنْ يَشَاءُ  ۚ  وَمَنْ يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَه ُُ مِنْ هَاد ٍ
'Afaman Yattaqī Biwajhihi Sū'a Al-`Adhābi Yawma Al-Qiyāmati  ۚ  Wa Qīla Lilžžālimīna Dhūqū Mā Kuntum Taksibūna َ039-024 Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa." أَفَمَنْ يَتَّقِي بِوَجْهِه ِِ سُوءَ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۚ  وَقِيلَ لِلظَّالِمِينَ ذُوقُوا مَا كُنْتُمْ تَكْسِبُونَ
Kadhdhaba Al-Ladhīna Min Qablihim Fa'atāhumu Al-`Adhābu Min Ĥaythu Lā Yash`urūna َ039-025 Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba. كَذَّبَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ فَأَتَاهُمُ الْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لاَ يَشْعُرُونَ
Fa'adhāqahumu Al-Lahu Al-Khizya Fī Al-Ĥayāati Ad-Dunyā  ۖ  Wa La`adhābu Al-'Ākhirati 'Akbaru  ۚ  Law Kānū Ya`lamūna َ039-026 Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani. فَأَذَاقَهُمُ اللَّهُ الْخِزْيَ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا  ۖ  وَلَعَذَابُ الآخِرَةِ أَكْبَرُ  ۚ  لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
Wa Laqad Đarabnā Lilnnāsi Fī Hādhā Al-Qur'āni Min Kulli Mathalin La`allahum Yatadhakkarūna َ039-027 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni. وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِي هَذَا الْقُرْآنِ مِنْ كُلِّ مَثَل ٍ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
Qur'ānāan `Arabīyāan Ghayra Dhī `Iwajin La`allahum Yattaqūna َ039-028 Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa. قُرآناً عَرَبِيّاً غَيْرَ ذِي عِوَج ٍ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ
Đaraba Al-Lahu Mathalāan Rajulāan Fīhi Shurakā'u Mutashākisūna Wa Rajulāan Salamāan Lirajulin Hal Yastawiyāni Mathalāan  ۚ  Al-Ĥamdu Lillahi  ۚ  Bal 'Aktharuhum Lā Ya`lamūna َ039-029 Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba. ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلا ً رَجُلا ً فِيه ِِ شُرَكَاءُ مُتَشَاكِسُونَ وَرَجُلا ً سَلَما ً لِرَجُلٍ هَلْ يَسْتَوِيَانِ مَثَلا ً  ۚ  الْحَمْدُ لِلَّهِ  ۚ  بَلْ أَكْثَرُهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
'Innaka Mayyitun Wa 'Innahum Mayyitūna َ039-030 Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne. إِنَّكَ مَيِّت ٌ وَإِنَّهُمْ مَيِّتُونَ
Thumma 'Innakum Yawma Al-Qiyāmati `Inda Rabbikum Takhtaşimūna َ039-031 Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin husũma. ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عِنْدَ رَبِّكُمْ تَخْتَصِمُونَ
Faman 'Ažlamu Mimman Kadhaba `Alá Al-Lahi Wa Kadhdhaba Biş-Şidqi 'Idh Jā'ahu  ۚ  'Alaysa Fī Jahannama Mathwáan Lilkāfirīna َ039-032 To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai? فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ كَذَبَ عَلَى اللَّهِ وَكَذَّبَ بِالصِّدْقِ إِذْ جَاءَهُ~ُ  ۚ  أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوى ً لِلْكَافِرِينَ
Wa Al-Ladhī Jā'a Biş-Şidqi Wa Şaddaqa  ۙ  Bihi 'Ūlā'ika Humu Al-Muttaqūna َ039-033 Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa. وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ~ِ  ۙ  أُوْلَائِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ
Lahum Mā Yashā'ūna `Inda Rabbihim  ۚ  Dhālika Jazā'u Al-Muĥsinīna َ039-034 Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa. لَهُمْ مَا يَشَاءُونَ عِنْدَ رَبِّهِمْ  ۚ  ذَلِكَ جَزَاءُ الْمُحْسِنِينَ
Liyukaffira Al-Lahu `Anhum 'Aswa'a Al-Ladhī `Amilū Wa Yajziyahum 'Ajrahum Bi'aĥsani Al-Ladhī Kānū Ya`malūna َ039-035 Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa. لِيُكَفِّرَ اللَّهُ عَنْهُمْ أَسْوَأَ الَّذِي عَمِلُوا وَيَجْزِيَهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
'Alaysa Al-Lahu Bikāfin `Abdahu  ۖ  Wa Yukhawwifūnaka Bial-Ladhīna Min Dūnihi  ۚ  Wa Man Yuđlili Al-Lahu Famā Lahu Min Hādin َ039-036 Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke waninSa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa. أَلَيْسَ اللَّهُ بِكَافٍ عَبْدَه ُُ  ۖ  وَيُخَوِّفُونَكَ بِالَّذِينَ مِنْ دُونِه ِِ  ۚ  وَمَنْ يُضْلِلِ اللَّهُ فَمَا لَه ُُ مِنْ هَاد ٍ
Wa Man Yahdi Al-Lahu Famā Lahu Min Muđillin  ۗ  'Alaysa Al-Lahu Bi`azīzin Dhī Antiqāmin َ039-037 Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa? وَمَنْ يَهْدِ اللَّهُ فَمَا لَه ُُ مِنْ مُضِلٍّ  ۗ  أَلَيْسَ اللَّهُ بِعَزِيز ٍ ذِي انْتِقَام ٍ
Wa La'in Sa'altahum Man Khalaqa As-Samāwāti Wa Al-'Arđa Layaqūlunna Al-Lahu  ۚ  Qul 'Afara'aytum Mā Tad`ūna Min Dūni Al-Lahi 'In 'Arādaniya Al-Lahu Biđurrin Hal Hunna Kāshifātu Đurrihi 'Aw 'Arādanī Biraĥmatin Hal Hunna Mumsikātu Raĥmatihi  ۚ  Qul Ĥasbiya Al-Lahu  ۖ  `Alayhi Yatawakkalu Al-Mutawakkilūna َ039-038 Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara." وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ  ۚ  قُلْ أَفَرَأَيْتُمْ مَا تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ إِنْ أَرَادَنِيَ اللَّهُ بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَاشِفَاتُ ضُرِّهِ~ِ أَوْ أَرَادَنِي بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ مُمْسِكَاتُ رَحْمَتِه ِِ  ۚ  قُلْ حَسْبِيَ اللَّهُ  ۖ  عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ الْمُتَوَكِّلُونَ
Qul Yā Qawmi A`malū `Alá Makānatikum 'Innī `Āmilun  ۖ  Fasawfa Ta`lamūna َ039-039 Ka ce: "Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani." قُلْ يَاقَوْمِ اعْمَلُوا عَلَى مَكَانَتِكُمْ إِنِّي عَامِل ٌ فَسَوْفَ  ۖ  تَعْلَمُونَ
Man Ya'tīhi `Adhābun Yukhzīhi Wa Yaĥillu `Alayhi `Adhābun Muqīmun َ039-040 "Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa." مَنْ يَأْتِيه ِِ عَذَاب ٌ يُخْزِيه ِِ وَيَحِلُّ عَلَيْهِ عَذَاب ٌ مُقِيم ٌ
'Innā 'Anzalnā `Alayka Al-Kitāba Lilnnāsi Bil-Ĥaqqi  ۖ  Famani Ahtadá Falinafsihi  ۖ  Wa Man Đalla Fa'innamā Yađillu `Alayhā  ۖ  Wa Mā 'Anta `Alayhim Biwakīlin َ039-041 Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba. إِنَّا أَنْزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ لِلنَّاسِ بِالْحَقِّ  ۖ  فَمَنِ اهْتَدَى فَلِنَفْسِه ِِ  ۖ  وَمَنْ ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا  ۖ  وَمَا أَنْتَ عَلَيْهِمْ بِوَكِيل ٍ
Al-Lahu Yatawaffá Al-'Anfusa Ĥīna Mawtihā Wa A-Atī Lam Tamut Fī Manāmihā  ۖ  Fayumsiku Allatī Qađá `Alayhā Al-Mawta Wa Yursilu Al-'Ukhrá 'Ilá 'Ajalin Musammáan  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yatafakkarūna َ039-042 Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni. اللَّهُ يَتَوَفَّى الأَنْفُسَ حِينَ مَوْتِهَا وَالَّتِي لَمْ تَمُتْ فِي مَنَامِهَا  ۖ  فَيُمْسِكُ الَّتِي قَضَى عَلَيْهَا الْمَوْتَ وَيُرْسِلُ الأُخْرَى إِلَى أَجَل ٍ مُسَمّى ً  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يَتَفَكَّرُونَ
'Ami Attakhadhū Min Dūni Al-Lahi Shufa`ā'a  ۚ  Qul 'Awalaw Kānū Lā Yamlikūna Shay'āan Wa Lā Ya`qilūna َ039-043 Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: "Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?" أَمِ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِ اللَّهِ شُفَعَاءَ  ۚ  قُلْ أَوَلَوْ كَانُوا لاَ يَمْلِكُونَ شَيْئا ً وَلاَ يَعْقِلُونَ
Qul Lillahi Ash-Shafā`atu Jamī`āan  ۖ  Lahu Mulku As-Samāwāti Wa Al-'Arđi  ۖ  Thumma 'Ilayhi Turja`ūna َ039-044 Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku." قُلْ لِلَّهِ الشَّفَاعَةُ جَمِيعا ً  ۖ  لَه ُُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۖ  ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Wa 'Idhā Dhukira Al-Lahu Waĥdahu Ashma'azzat Qulūbu Al-Ladhīna Lā Yu'uminūna Bil-'Ākhirati  ۖ  Wa 'Idhā Dhukira Al-Ladhīna Min Dūnihi 'Idhā Hum Yastabshirūna َ039-045 Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki. وَإِذَا ذُكِرَ اللَّهُ وَحْدَهُ اشْمَأَزَّتْ قُلُوبُ الَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ  ۖ  وَإِذَا ذُكِرَ الَّذِينَ مِنْ دُونِهِ~ِ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ
Quli Al-Lahumma Fāţira As-Samāwāti Wa Al-'Arđi `Ālima Al-Ghaybi Wa Ash-Shahādati 'Anta Taĥkumu Bayna `Ibādika Fī Mā Kānū Fīhi Yakhtalifūna َ039-046 Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa." قُلِ اللَّهُمَّ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ أَنْتَ تَحْكُمُ بَيْنَ عِبَادِكَ فِي مَا كَانُوا فِيه ِِ يَخْتَلِفُونَ
Wa Law 'Anna Lilladhīna Žalamū Mā Fī Al-'Arđi Jamī`āan Wa Mithlahu Ma`ahu Lāftadaw Bihi Min Sū'i Al-`Adhābi Yawma Al-Qiyāmati  ۚ  Wa Badā Lahum Mina Al-Lahi Mā Lam Yakūnū Yaĥtasibūna َ039-047 Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su. وَلَوْ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا مَا فِي الأَرْضِ جَمِيعا ً وَمِثْلَه ُُ مَعَهُ لاَفْتَدَوْا بِه ِِ مِنْ سُوءِ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ  ۚ  وَبَدَا لَهُمْ مِنَ اللَّهِ مَا لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ
Wa Badā Lahum Sayyi'ātu Mā Kasabū Wa Ĥāqa Bihim Mā Kānū Bihi Yastahzi'ūn َ039-048 Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu. وَبَدَا لَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا وَحَاقَ بِهِمْ مَا كَانُوا بِه ِِ يَسْتَهْزِئُون
Fa'idhā Massa Al-'Insāna Đurrun Da`ānā Thumma 'Idhā Khawwalnāhu Ni`matan Minnā Qāla 'Innamā 'Ūtītuhu `Alá `Ilmin  ۚ  Bal Hiya Fitnatun Wa Lakinna 'Aktharahum Lā Ya`lamūna َ039-049 To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba. فَإِذَا مَسَّ الإِنسَانَ ضُرّ ٌ دَعَانَا ثُمَّ إِذَا خَوَّلْنَاه ُُ نِعْمَة ً مِنَّا قَالَ إِنَّمَا أُوتِيتُه ُُ عَلَى عِلْم ٍ  ۚ  بَلْ هِيَ فِتْنَة ٌ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ
Qad Qālahā Al-Ladhīna Min Qablihim Famā 'Aghná `Anhum Mā Kānū Yaksibūna َ039-050 Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba. قَدْ قَالَهَا الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ فَمَا أَغْنَى عَنْهُمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ
Fa'aşābahum Sayyi'ātu Mā Kasabū Wa  ۚ  Al-Ladhīna Žalamū Min Hā'uulā' Sayuşībuhum Sayyi'ātu Mā Kasabū Wa Mā Hum Bimu`jizīna َ039-051 Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba. فَأَصَابَهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا  ۚ  وَالَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْ هَاؤُلاَء سَيُصِيبُهُمْ سَيِّئَاتُ مَا كَسَبُوا وَمَا هُمْ بِمُعْجِزِينَ
'Awalam Ya`lamū 'Anna Al-Laha Yabsuţu Ar-Rizqa Liman Yashā'u Wa Yaqdiru  ۚ  'Inna Fī Dhālika La'āyātin Liqawmin Yu'uminūna َ039-052 Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni. أَوَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشَاءُ وَيَقْدِرُ  ۚ  إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَات ٍ لِقَوْم ٍ يُؤْمِنُونَ
Qul Yā `Ibādī Al-Ladhīna 'Asrafū `Alá 'Anfusihim Lā Taqnaţū Min Raĥmati Al-Lahi  ۚ  'Inna Al-Laha Yaghfiru Adh-Dhunūba Jamī`āan  ۚ  'Innahu Huwa Al-Ghafūru Ar-Raĥīmu َ039-053 Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." قُلْ يَاعِبَادِي الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَى أَنْفُسِهِمْ لاَ تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ إِنَّ  ۚ  اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعا ً إِنَّه ُُ  ۚ  هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Wa 'Anībū 'Ilá Rabbikum Wa 'Aslimū Lahu Min Qabli 'An Ya'tiyakumu Al-`Adhābu Thumma Lā Tunşarūna َ039-054 "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba." وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَه ُُ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ ثُمَّ لاَ تُنْصَرُونَ
Wa Attabi`ū 'Aĥsana Mā 'Unzila 'Ilaykum Min Rabbikum Min Qabli 'An Ya'tiyakumu Al-`Adhābu Baghtatan Wa 'Antum Lā Tash`urūna َ039-055 "Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba." وَاتَّبِعُوا أَحْسَنَ مَا أُنْزِلَ إِلَيْكُمْ مِنْ رَبِّكُمْ مِنْ قَبْلِ أَنْ يَأْتِيَكُمُ العَذَابُ بَغْتَة ً وَأَنْتُمْ لاَ تَشْعُرُونَ
'An Taqūla Nafsun Yā Ĥasratā `Alá Mā Farraţtu Fī Janbi Al-Lahi Wa 'In Kuntu Lamina As-Sākhirīna َ039-056 "Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"' أَنْ تَقُولَ نَفْس ٌ يَاحَسْرَتَا عَلَى مَا فَرَّطْتُ فِي جَنْبِ اللَّهِ وَإِنْ كُنْتُ لَمِنَ السَّاخِرِينَ
'Aw Taqūla Law 'Anna Al-Laha Hadānī Lakuntu Mina Al-Muttaqīna َ039-057 "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'" أَوْ تَقُولَ لَوْ أَنَّ اللَّهَ هَدَانِي لَكُنْتُ مِنَ الْمُتَّقِينَ
'Aw Taqūla Ĥīna Tará Al-`Adhāba Law 'Anna Lī Karratan Fa'akūna Mina Al-Muĥsinīna َ039-058 "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'" أَوْ تَقُولَ حِينَ تَرَى الْعَذَابَ لَوْ أَنَّ لِي كَرَّة ً فَأَكُونَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ
Balá Qad Jā'atka 'Āyātī Fakadhdhabta Bihā Wa Astakbarta Wa Kunta Mina Al-Kāfirīna َ039-059 "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai." بَلَى قَدْ جَاءَتْكَ آيَاتِي فَكَذَّبْتَ بِهَا وَاسْتَكْبَرْتَ وَكُنْتَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Wa Yawma Al-Qiyāmati Tará Al-Ladhīna Kadhabū `Alá Al-Lahi Wujūhuhum Muswaddatun  ۚ  'Alaysa Fī Jahannama Mathwáan Lilmutakabbirīna َ039-060 Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai? وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ تَرَى الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللَّهِ وُجُوهُهُمْ مُسْوَدَّةٌ  ۚ  أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوى ً لِلْمُتَكَبِّرِينَ
Wa Yunajjī Al-Lahu Al-Ladhīna Attaqaw Bimafāzatihim Lā Yamassuhumu As-Sū'u Wa Lā Hum Yaĥzanūna َ039-061 Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba. وَيُنَجِّي اللَّهُ الَّذِينَ اتَّقَوا بِمَفَازَتِهِمْ لاَ يَمَسُّهُمُ السُّوءُ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ
Al-Lahu Khāliqu Kulli Shay'in  ۖ  Wa Huwa `Alá Kulli Shay'in Wa Kīlun َ039-062 Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme. اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْء ٍ  ۖ  وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْء ٍ وَكِيل ٌ
Lahu Maqālīdu As-Samāwāti Wa Al-'Arđi Wa  ۗ  Al-Ladhīna Kafarū Bi'āyāti Al-Lahi 'Ūlā'ika Humu Al-Khāsirūna َ039-063 Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra. لَه ُُ مَقَالِيدُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ  ۗ  وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللَّهِ أُوْلَائِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ
Qul 'Afaghayra Al-Lahi Ta'murūnnī 'A`budu 'Ayyuhā Al-Jāhilūna َ039-064 Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!" قُلْ أَفَغَيْرَ اللَّهِ تَأْمُرُونِّي أَعْبُدُ أَيُّهَا الْجَاهِلُونَ
Wa Laqad 'Ūĥiya 'Ilayka Wa 'Ilá Al-Ladhīna Min Qablika La'in 'Ashrakta Layaĥbaţanna `Amaluka Wa Latakūnanna Mina Al-Khāsirīna َ039-065 Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra." وَلَقَدْ أُوحِيَ إِلَيْكَ وَإِلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكَ لَئِنْ أَشْرَكْتَ لَيَحْبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Bali Al-Laha Fā`bud Wa Kun Mina Ash-Shākirīna َ039-066 Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya. بَلِ اللَّهَ فَاعْبُدْ وَكُنْ مِنَ الشَّاكِرِينَ
Wa Mā Qadarū Al-Laha Ĥaqqa Qadrihi Wa Al-'Arđu Jamī`āan Qabđatuhu Yawma Al-Qiyāmati Wa As-Samāwātu Maţwīyātun Biyamīnihi  ۚ  Subĥānahu Wa Ta`ālá `Ammā Yushrikūna َ039-067 Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi. وَمَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِه ِِ وَالأَرْضُ جَمِيعا ً قَبْضَتُه ُُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَالسَّماوَاتُ مَطْوِيَّات ٌ بِيَمِينِه ِِ  ۚ  سُبْحَانَه ُُ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ
Wa Nufikha Fī Aş-Şūri Faşa`iqa Man As-Samāwāti Wa Man Al-'Arđi 'Illā Man Shā'a Al-Lahu  ۖ  Thumma Nufikha Fīhi 'Ukhrá Fa'idhā Hum Qiyāmun Yanžurūna َ039-068 Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo. وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَصَعِقَ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَمَنْ فِي الأَرْضِ إِلاَّ مَنْ شَاءَ اللَّهُ  ۖ  ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ~ِ أُخْرَى فَإِذَا هُمْ قِيَام ٌ يَنْظُرُونَ
Wa 'Ashraqati Al-'Arđu Binūri Rabbihā Wa Wuđi`a Al-Kitābu Wa Jī'a Bin-Nabīyīna Wa Ash-Shuhadā'i Wa Quđiya Baynahum Bil-Ĥaqqi Wa Hum Lā Yužlamūna َ039-069 Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba. وَأَشْرَقَتِ الأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ الْكِتَابُ وَجِيءَ بِالنَّبِيِّينَ وَالشُّهَدَاءِ وَقُضِيَ بَيْنَهُمْ بِالْحَقِّ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
Wa Wuffiyat Kullu Nafsin Mā `Amilat Wa Huwa 'A`lamu Bimā Yaf`alūna َ039-070 Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa. وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْس ٍ مَا عَمِلَتْ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَا يَفْعَلُونَ
Wa Sīqa Al-Ladhīna Kafarū 'Ilá Jahannama Zumarāan  ۖ  Ĥattá 'Idhā Jā'ūhā Futiĥat 'Abwābuhā Wa Qāla Lahum Khazanatuhā 'Alam Ya'tikum Rusulun Minkum Yatlūna `Alaykum 'Āyāti Rabbikum Wa Yundhirūnakum Liqā'a Yawmikumdhā  ۚ  Qālū Balá Wa Lakin Ĥaqqat Kalimatu Al-`Adhābi `Alá Al-Kāfirīna َ039-071 Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!" وَسِيقَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِلَى جَهَنَّمَ زُمَراً  ۖ  حَتَّى إِذَا جَاءُوهَا فُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُل ٌ مِنْكُمْ يَتْلُونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِ رَبِّكُمْ وَيُنْذِرُونَكُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَذَا  ۚ  قَالُوا بَلَى وَلَكِنْ حَقَّتْ كَلِمَةُ الْعَذَابِ عَلَى الْكَافِرِينَ
Qīla Adkhulū 'Abwāba Jahannama Khālidīna Fīhā  ۖ  Fabi'sa Math Al-Mutakabbirīna َ039-072 Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana." قِيلَ ادْخُلُوا أَبْوَابَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا  ۖ  فَبِئْسَ مَثْوَى الْمُتَكَبِّرِينَ
Wa Sīqa Al-Ladhīna Attaqaw Rabbahum 'Ilá Al-Jannati Zumarāan  ۖ  Ĥattá 'Idhā Jā'ūhā Wa Futiĥat 'Abwābuhā Wa Qāla Lahum Khazanatuhā Salāmun `Alaykum Ţibtumdkhulūhā Khālidīna َ039-073 Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama( a cikinta)." وَسِيقَ الَّذِينَ اتَّقَوْا رَبَّهُمْ إِلَى الْجَنَّةِ زُمَراً  ۖ  حَتَّى إِذَا جَاءُوهَا وَفُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا سَلاَمٌ عَلَيْكُمْ طِبْتُمْ فَادْخُلُوهَا خَالِدِينَ
Wa Qālū Al-Ĥamdu Lillahi Al-Ladhī Şadaqanā Wa`dahu Wa 'Awrathanā Al-'Arđa Natabawwa'u Mina Al-Jannati Ĥaythu Nashā'u  ۖ  Fani`ma 'Ajru Al-`Āmilīna َ039-074 Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata. وَقَالُوا الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي صَدَقَنَا وَعْدَه ُُ وَأَوْرَثَنَا الأَرْضَ نَتَبَوَّأُ مِنَ الْجَنَّةِ حَيْثُ نَشَاءُ  ۖ  فَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ
Wa Tará Al-Malā'ikata Ĥāffīna Min Ĥawli Al-`Arshi Yusabbiĥūna Biĥamdi Rabbihim  ۖ  Wa Quđiya Baynahum Bil-Ĥaqqi Wa Qīla Al-Ĥamdu Lillahi Rabbi Al-`Ālamīna َ039-075 Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu." وَتَرَى الْمَلاَئِكَةَ حَافِّينَ مِنْ حَوْلِ الْعَرْشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ  ۖ  وَقُضِيَ بَيْنَهُمْ بِالْحَقِّ وَقِيلَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ
Next Sūrah